Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau, Jihar Zamfara, ta soke zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa.
Kotun ta kuma umarci APC da ta sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwani a yankin cikin kwanaki 14.
Mai shari’a Hassan Dikko ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, bayan ya saurari hujjoji da bayanan da ɓangarorin da ke shari’ar suka gabatar.
Alƙalin kotun ya umarci jam’iyyar APC da ta gudanar da sabon zaɓen bisa ƙa’idojin jam’iyyar da sauran dokokin da suka dace.
Ɗan takarar neman kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa a ƙarƙashin APC, Dokta Sani Abdullahi Shinkafi ne, ya kai ƙara zuwa kotu, inda ya ƙalubalanci sahihancin zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, Shinkafi ya yi maraba da matakin kotun, yana mai cewa hukuncin zai taimaka wajen dawo da amincewar jama’a ga ɓangaren shari’a.
Ya ce, “Ina godiya da wannan hukunci. Wannan babban mataki ne zuwa ga nasararmu. An tabbatar da martabar ɓangaren shari’a, kuma har yanzu mutane suna da amincewa da shi.”
Hukuncin kotun na nufin APC za ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa cikin kwanaki 14 da kotun ta ƙayyade.














