Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya (DHQ) ta ce sojoji sun kashe ’yan ta’adda 324 tare da kama wasu mutane 373 da ake zargi da aikata laifuka a faɗin ƙasar a watan Agustan 2026.
Daraktan Sashen Yaɗa Labaran Ayyukan Sojoji, Manjo Janar Michael Onoja ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan ayyukan sojojin a watan Agusta.
Ya ce sojojin sun kuma ceto mutane 610 da aka yi garkuwa da su, yayin da ’yan ta’adda 201 suka miƙa wuya ga sojoji.
A cewarsa, an ƙwato bindigogi 88 da harsasai 2,077 yayin ayyukan sojojin.
Onoja ya kuma ce sojojin sun lalata wuraren tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba guda 21 tare da ƙwato lita 686,800 na ɗanyen man fetur da aka sace.
Ya ce adadin ’yan ta’addan da ke miƙa wuya na nuna cewa matsin lambar da sojoji ke yi wa ƙungiyoyin masu aikata laifuka na ƙaruwa.
Adadin waɗanda suka miƙa wuya ya ƙaru daga 11 a watan Yuni zuwa 57 a Yuli, sannan ya kai 201 a watan Agusta.
Onoja ya ce sun ceto mutane 308, waɗanda mafi yawansu mata da yara ne daga dajin Kainji Lake National Park a ranar 5 ga watan Agusta.
Ya ce sojoji na ci gaba da gudanar da ayyuka a yankin da kewayen wurin domin hana ’yan ta’adda sake kai hare-hare da kuma samar da yanayin tsaro da zai bai wa mutanen da suka rasa matsugunansu damar komawa gidajensu.
Sojojin sun yi kira ga iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su da su kwantar da hankalinsu tare da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen ceto waɗanda har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane.
Onoja ya ce Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya jajirce wajen kare rayukan jama’a, ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma yaƙi da ta’addanci da sauran laifuka a faɗin ƙasar.














