ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Arewa House Ya Soke Wurin Ƙaddamar Da Littafin Sukar Gwamnatin Tinubu

by Sulaiman
2 weeks ago
Arewa house

Hukumar Gidan Binciken tarihi na Arewa (Arewa House) ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ta janye amincewar da ta bayar na gudanar da bikin ƙaddamar da wani littafi da ke sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Kaduna.

Hukumar ta danganta matakin da wasu dalilan gudanarwa, amma marubucin littafin, Abubakar Siddique Mohammed, ya yi zargin cewa, ana ƙoƙarin hana gudanar da taron ne kawai.

Mohammed, Daraktan Cibiyar Nazarin Ci Gaban Dimokuraɗiyya (CEDDERT), ya ce an sanar da shi soke amfani da wurin ta wasiƙar da ya karɓa ranar Asabar, 10 ga Oktoba.

ADVERTISEMENT

An shirya gudanar da taron ne a ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, da ƙarfe 10 na safe a Arewa House da ke Kaduna.

A cikin wasiƙar soke amincewar, hukumar ta bayyana cewa wurin ba zai kasance a shirye ba saboda bincike, gyare-gyare da sauran shirye-shiryen gudanarwa da ake yi a wurin. 

LABARAI MASU NASABA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Sai dai Mohammed ya yi zargin cewa matakin na da alaƙa da yunƙurin hana jama’a tattauna manufofin gwamnatin Tinubu. Ya kuma ce wasu otal-otal da aka nemi su karɓi taron a Kaduna sun ƙi amincewa, bisa zargin cewa an yi musu gargaɗi.

Saboda haka, masu shirya taron sun yanke shawarar mayar da ƙaddamar da littafin zuwa Abuja, inda za su sanar da sabon wuri da ranar gudanar da taron.

Littafin, mai taken “Tinubu: From Renewed Hope to Despair: A Critical Examination of President Bola Ahmed Tinubu’s Government”, ma’ana – “binciken halin da gwamnatin Tinubu ke ciki, daga sabunta fata zuwa cikin mawuyacin yanayi”. An yi nazari kan manufofin gwamnatin Tinubu da tasirinsu ga tattalin arzikin Nijeriya, tsaro, haɗin kan ƙasa da ci gaban dimokuraɗiyya.

Marubucin ya bayyana damuwarsa kan lamarin, yana mai cewa ya kamata cibiyoyin ilimi da bincike su ba da damar ’yancin tunani da gudanar da muhawara cikin walwala.

Arewa House
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori Biyar
  • Sulaiman
    Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Djibouti
  • Sulaiman
    Ta Yaya Ake Ci Gaba Da Fitar Da Sabbin Kayayyaki A Yayin Baje Koli Na Canton Fair
  • Sulaiman
    Darasi Daga Zuhudun Manzon Allah (SAW)

MASU ALAKA

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya
Labarai

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya
Ra'ayi Riga

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026
Next Post
Majalisar Dokoki Na Shirin Ɗaukar Matakan Daƙile Ƙarin Kuɗin Haya A Kano

Majalisar Dokoki Na Shirin Ɗaukar Matakan Daƙile Ƙarin Kuɗin Haya A Kano

LABARAI MASU NASABA

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026
Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

Sin Da Afirka Abokan Tafiya Ne Wajen Inganta Tsarin Jagorancin Duniya

October 23, 2026

Shugabar Jaridar LEADERSHIP Ta Halarci Bikin Aza Harsashin Cibiyar Ƙirƙire-Ƙirƙire Tare Da Remi Tinubu A Abuja

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

An Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Birnin Riyadh

October 23, 2026
Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

Kakakin Majalisar Nasarawa Ya Raba Naira Miliyan 6 da Atamfofi 1,100 a Taron APC

October 23, 2026
Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

Kamfanin Simintin Dangote Ya Ware Miliyoyi Don Tallafawa Karatun Al’ummar Gboko

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.