Hanyoyin Kare Fata Daga Illar Hasken Rana
Hasken rana na da amfani ga jikin dan Adam, amma yawan fuskantar hasken ta, musamman ma hasken da ke dauke da hasken ultrabiolet (Ub), na iya cutar da fatar jikia Wannan yana iya haifar da konewar fata, saurin tsufanta da kuma kara hadarin kamuwa da cutar kansar fata. Saboda haka, yana da matukar muhimmanci a kula da fata ta hanyar amfani da hanyoyin kariya daga hasken rana. Ga wasu hanyoyin kare fata daga hasken rana: 1. Amfani da man kariya daga rana: Yana da kyau a yi amfani da man kariya hasken rana (sunscreen) mai SPF 30 ko sama da haka. A shafa shi kafin fita a waje, sannan a rika sake shafawa bayan awa biyu ko bayan an yi gumi mai yawa ko shiga ruwa. 2.Amfani da hula: Sa hula mai fadin baki na taimakawa wajen kare fuska, wuya da kuma kunnuwa daga hasken rana. 3. Sanya tufafi masu kariya: Tufafi masu rufe jiki da kuma tabarau masu kariya daga hasken Ub na taimakawa wajen rage fuskantar hasken rana kai tsaye. 4. Guje wa tsananin rana: A rage yawan zama a karkashin rana, musamman a lokutan da haskenta ya fi karfi. Neman inuwa ma yana daga cikin hanyoyin kariya. 5. Kula da fata bayan dawowa: Bayan dawowa daga rana, a wanke fata sannu a hankali, sannan a yi amfani da mai ma sa laushin fata domin taimakawa mata ta kasance cikin yanayi mai kyau. A karshe, kare fata daga hasken rana wani muhimmin bangare ne na kula da lafiya da kyawun fata. Bai kamata a jira sai an samu matsala ba kafin a fara kula da ita ba. Kula da fatarki yau domin lafiyar ta a gobe.



















