Asibitin Tafi Da Gidanka Na Jirgin Ruwan Sin Ya Nufi Kasashen Afrika Da Kudancin Asiya Domin Bayar Da Hidimomin Jin Kai
Yau Laraba, asibitin tafi da gidanka na jirgin sojin ruwan rundunar PLA ta Sin watau Auspicious Ark, ya tashi daga...
Yau Laraba, asibitin tafi da gidanka na jirgin sojin ruwan rundunar PLA ta Sin watau Auspicious Ark, ya tashi daga...
A yau Laraba ne aka kafa cibiyar binciken wayewar kai ta duniya a hukumance, wani dandali da aka tsara domin binciken ilimi a mabambantan bangarori, mai babban matsayi, wanda cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin ta kafa. A nan gaba kuma, cibiyar za ta aiwatar da ayyukan nazari, da bayyana shawara kan wayewar kan duniya, kuma za ta rubuta "Littafi mai bayyana ra’ayoyin manazarta game da musayar al'adu", da samar da dakin adana bayanai na binciken wayewar kan duniya da sauransu. Har ila yau, cibiyar za ta ci gaba da samar da sakamakon bincike mai inganci a fannoni masu muhimmanci, kamar ka'idodin wayewar kai, da kwatancen al'adu, da fasahar AI, da ci gaban al'adun duniya, da dogaro da manyan bukatun kasa bisa manyan tsare-tsare, domin samar da tushen tunani, da goyon bayan basira ga gina kyakkyawar makomar bil-Adam ta bai daya. (Amina Xu)
Hukumar kula da makamashi ta kasar Sin ta ce jimilar man fetur da gas da Sin ta samar ya kai...
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya yi kira da a kara kaimi wajen aiwatar da muhimmin aikin gina halaye nagari...
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, kasar ta nuna matukar rashin amincewarta ga jakadan kasar Philippines bisa tsokanar...
Firaministan Sin Li Qiang, ya aike da sakon taya Andy Burnham murnar hawa mukamin firaministan Birtaniya jiya Litinin. Li Qiang...
Ma’aikatar kula da cinikayya da wasu sassan gwamnati 8 na kasar Sin, sun fitar da wasu matakai 19 na inganta...
Kasar Sin ta bayar da tallafin sama da ton 3,000 na alkama da shinkafa, domin taimaka wa mutane masu rauni...
A ranar Juma’ar da ta gabata, aka kaddamar da Kimi K3, wani samfurin kirkirrarriyar basira ta AI da kamfanin Moonshot...
Tawaga ta 27 ta jami’an lafiya ta Sin a Saliyo, ta kaddamar da shirin horar da ma’aikatan jinya ko nas-nas dabarun likitancin gargajiya na Sin, wanda ya hada lakcoci daga masanan Sin ta hanyar na’urori da kuma wadanda jami’an lafiya na Sin da ke kasar za su gabatar kai tsaye, domin karfafa karfin tsarin kiwon lafiya a kasar. Ma’aikatan jinya sama da 40 ne suka halarci lakca ta farko da ta gudana ranar Asabar a cibiyar kiwon lafiya daga nesa, watau Telemedicine Centre da ke asibitin abota na Sin da Saliyo da ke birnin Freetown. Shirin wanda aka tsara karkashin cibiyar horar da ma’aikatan jinya ta Sin da Saliyo, ta hada da koyarwa daga masana lafiya na Sin da ke lardin Hunan da kuma nune-nune da koyarwa daga tawagar jami’an lafiya na Sin da ke Saliyo. Domin shawo kan karuwar matsalolin ciwon wuya da kafada da mahadar kasusuwa, wata tawagar jami’an lafiya ta nuna yadda ake jinya ta hanyar dabarar nan ta sossoka allura ta Fu, watau acupuncture ta zamani. Tawagar ta ce za ta ci gaba da bayar da horo cikin harsuna biyu ta hanyar cibiyar Telemedicine domin ganin dorewar kwarewar ma’aikatan jinya da fadada ingancin hidimomin maganin radadin ciwo a fadin Saliyo. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.