Xi Jinping Ya Mika Sakon Murnar Cika Shekaru 61 Da Samun ‘Yancin Kai Ga Shugaban Maldives
A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mikawa shugaban kasar Maldives Mohamed Muizzu, sakon murnar cika shekaru...
A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mikawa shugaban kasar Maldives Mohamed Muizzu, sakon murnar cika shekaru...
A yau Lahadi, hukumar lura da ayyukan kandagarkin bala’o’i, da rage tasirinsu da samar da tallafi ta kasar Sin, ta sanar da shirin ko-ta-kwana a mataki na hudu, da nufin tunkarar tasirin ibtila’in da mahaukaciyar guguwa, da ruwan sama kamar da bakin kwarya suka yi a lardin Guangdong na kudancin kasar, a karo na 12 cikin shekarar nan. Bayan aukuwar mahaukaciyar guguwar da aka yiwa lakabi da Typhoon Noul, yanzu haka an aike da tawagogin jami’ai zuwa yankunan da ibtila’in ya shafa, don nazartar halin da ake ciki, tare da taimakawa mahukuntan wuraren da ayyukan sauyawa jama’a matsugunai, da tabbatar da samar musu abubuwan bukata. Rahotanni sun tabbatar da cewa, a yau Lahadi hukumar tsara ayyukan ci gaba da aiwatar da sauye-sauye ta kasar Sin, ta bukaci a samar da kudi har yuan miliyan 100 daga kasafin kudin kasa don tallafawa lardin na Guangdong, ta yadda za a iya gudanar da ayyukan farfado da kayan more rayuwa bayan ibtila’in. Ana kuma sa ran amfani da kudaden wajen gyara hanyoyin mota, da wuraren adana ruwa, da kayayyakin hidimtawa jama’a irinsu makarantu da asibitoci. Ta hanyar aiwatar da wadannan matakai, ana fatan gaggauta sake farfado da harkokin masana’antu, da zamantakewar al’umma kamar yadda aka saba. Mahaukaciyar guguwar mai lakabin Typhoon Noul, ta aukawa lardin Guangdong da safiyar Lahadin nan, inda karfin iskar a kusa da tsakiya ya kai maki 14. Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka karfinta ya ragu daga matakin koli. (Saminu Alhassan)
Ya zuwa jiya Asabar 25 ga watan nan na Yuli, kudaden shigar gidajen sinima na kasar Sin a zangon lokacin...
Yanzu haka saura kusan kwanaki 100 a bude gasar wasannin Olympics ta matasa ta birnin Dakar ta shekarar 2026, kuma...
A ranar 23 ga watan Yulin nan, ofishin jakadancin Sin a Nijeriya ya shirya wani karamin taro a Abuja domin...
A ranar 8 ga watan Yulin 2026, an gudanar da babban taron bayar da lambobin yabo na kasar Sin a...
An fara watsa shirin talabijin na musamman mai kashi uku da ke da taken “Yiwu ta duniya –Yadda Xi Jinping...
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a jiya Juma’a, inda mataimakin ministan...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya halarci taron kwamitin ministocin harkokin waje na kasashen kungiyar hadin gwiwa ta...
An sanya wuraren sana’ar kayan tangaran na hannu na Jingdezhen da ke kasar Sin, a cikin jerin wuraren tarihi na...
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.