Li Qiang Ya Gana Da Shugaban Kungiyar Sana’o’in Fasaha Ta Duniya Da Babban Jami’in Gudanarwarta
Da yammacin yau Talata 22 ga watan Satumba, firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya gana da Francis Hourant, shugaban kungiyar sana’o’in fasaha ta kasa da kasa, da David Hoey, babban jami’in gudanarwarta a birnin Shanghai, wadanda suka zo kasar Sin domin halartar gasar sana’o’in fasaha ta kasa da kasa karo na 48. Li Qiang ya bayyana cewa, kasar Sin na da kwarin gwiwar yin aiki tare da dukkan bangarori domin gabatar wa duniya wani babban bikin sana’o’in fasaha na musamman. Kasar Sin a shirye take ta kara zurfafa hadin gwiwa da kungiyar sana’o’in fasahar, da yin hadin gwiwar zurfafa ci gaban fannin sana’o’in fasaha a duniya, da bunkasa tattalin arzikin duniya mai dorewa cikin kwanciyar hankali, kana da kyautata jin dadin al’ummomin dukkan kasashe. Za a gudanar da gasar sana’o’in fasaha ta kasa da kasa karo na 48 ne a birnin Shanghai daga ranar 22 zuwa 27 ga watan Satumba, yayin da za a gudanar da bikin baje kolin kasuwancin fasahohin zamani na duniya karo na biyar a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang, daga ranar 23 zuwa 27 ga watan Satumba. Bisa gayyatar kasar Sin, firaministan kasar Malaysia, Anwar Ibrahim, zai halarci bikin bude gasar ta sana’o’in fasaha ta kasa da kasa da kuma bikin kaddamar da baje kolin kasuwancin fasahohin zamani na duniya. Bugu da kari, shugaban majalisar ministocin kasar Kyrgyzstan, Adylbek Aleshovich Kasymaliev, zai halarci bikin kaddamar da baje kolin kasuwancin fasahohin zamanin na duniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere)



















