An Sanya Wuraren Sana’ar Kayan Tangaran Na Jingdezhen Cikin Jerin Wuraren Tarihi Na Duniya Na UNESCO
An sanya wuraren sana’ar kayan tangaran na hannu na Jingdezhen da ke kasar Sin, a cikin jerin wuraren tarihi na...
An sanya wuraren sana’ar kayan tangaran na hannu na Jingdezhen da ke kasar Sin, a cikin jerin wuraren tarihi na...
An kira taron ministocin kungiyar hadin gwiwa kan tattalin arziki ta nahiyar Asiya da tekun Pasific (APEC), kan harkar raya fasahohin dijital da kirkirarriyar basira ko AI na shekarar 2026, jiya Alhamis a birnin Chengdu na kasar Sin, inda aka zartas da sanarwar ministocin kungiyar APEC na shekarar 2026 game da ayyukan raya fasahohin dijital da AI, ko kuma sanarwar Chengdu a takaice. Cikin sanarwar, an cimma matsaya daya ta kafa kungiyar hadin gwiwar raya fasahohin digital da AI ta yankin Asiya da Pasifik, domin kafa tsarin zurfafa hadin gwiwa a fannin raya fasahohin tsakanin mambobin kungiyar APEC a nan gaba. Shugaban taron, kana ministan harkokin masana’antu da sadarwa na kasar Sin Li Lecheng ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da mambobin kungiyar ta APEC, ta hanyar amfani da tsarin kungiyar, da aiwatar da ra’ayi daya da aka cimma yayin taron na wannan karo, ta yadda za a zurfafa hadin gwiwa da mu’amalar dake tsakanin bangarori daban daban, don cimma moriyar bunkasuwar fasahohin dijital da AI, da kafa makoma mai haske cikin hadin gwiwa. (Mai Fassara: Maryam Yang)
A yau Jumma’a, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar da matakin sanya kamfanoni 14 na Tarayyar Turai (EU) cikin...
Lamarin gibi ta fuskar ci gaba tsakanin gabashin da yammacin Sin wani batu ne da ake yawan tattauna a kansa...
Wani bincike kan ra'ayoyin jama'a da cibiyar bincike ta Pew ta kasar Amurka ta gudanar kwanan nan ya nuna cewa,...
A watan Yulin shekara ta 2026, a birnin Shanghai. A wurin taron raya kirkirarriyar basira ko AI na duniya, mahalarta...
Kasar Sin ta ci gaba da kasancewa wuri mai jan hankulan masu zuba jari daga kasashen waje, inda kamfanoni kusan 4,800 masu jarin waje suka kara yawan jarin da suke zubawa a kasar a rabin farko na shekarar 2026, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gabatar a yau Alhamis. A cikin watanni shida na farko na shekarar, kasar Sin ta samu karuwar kafa sabbin kamfanoni masu jarin waje da kashi 5.3% a mizanin shekara-shekara, inda jarin waje da ake zubawa kai-tsaye (FDI) wanda ake amfani da shi a zahiri ya kai yuan biliyan 402.1, watau kwatankwacin dala biliyan 59.2. Tsarin zuba jarin waje ya ci gaba da samun bunkasa, inda jarin da aka zuba a masana’antun manyan fasahohin zamani ya karu da kashi 33.2% a mizanin shekara-shekara, wanda ya kai kashi 42.4% na daukacin jimillar da aka zuba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Kwanan nan, Wang Yi, mamba a ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma ministan harkokin...
A shekarun baya bayan nan, jerin sakamakon binciken jin ra’ayoyin jama’a daga cibiyoyi mabanbanta, na kara shaida karbuwa, da gamsuwar...
Hukumar makamashi ta kasar Sin ko NEA a takaice, ta kaddamar da shirin bunkasa amfani da makamashi da ake iya sabuntawa, karkashin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15, wanda kasar ke aiwatarwa tun daga shekarar nan ta 2026 zuwa 2030. Kundin da hukumar ta NEA ta fitar da hadin gwiwar hukumar raya kasa da aiwatar da sauye-sauye a yau Alhamis a hukumance, ya nuna cewa ya zuwa shekarar 2030, jimillar karfin samar da makamashin da cibiyoyin da aka kafa na iya kaiwa kusan kilowat biliyan 3.5, inda a duk shekara ake hasashen samar da jimillar lantarkin da ta kai kusan kilowat-awa tiriliyan 6. Kazalika, adadin karfin samar da makamashi ta iska da hasken rana na iya haura kilowat biliyan 2.8, yayin da jimillar lantarkin da za a samar duk shekara za ta haura kusan kilowat-awa tiriliyan 4. Makamashi da ake iya sabunta amfani da shi na nufin wanda ake iya ci gaba da maimaita amfani da shi, da sake sarrafawa ta hanyoyin dabi’a cikin kankanen lokaci. Wadanda suka hada da wanda ake samu daga karfin ruwa, da iska, da hasken rana, da tururin halittu, da dumin karkashin kasa, da wanda ake samarwa daga teku. A daya bangaren kuma, sabbin makamashi na nufin wadanda ake iya samarwa daga sauran fannoni ban da ta karfin ruwa, kamar dai yadda kundin bayanin shirin ya fayyace. (Saminu Alhassan)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.