Kudin Sayen Tikitin Kallon Fina-Finai A Lokacin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin Ya Kai Yuan Miliyan 800
Alkaluma daga dandamalin sayar da tikitin kallon fina-finai sun nuna cewa, zuwa rana ta 5 ta hutun bikin kafuwar kasar...
Alkaluma daga dandamalin sayar da tikitin kallon fina-finai sun nuna cewa, zuwa rana ta 5 ta hutun bikin kafuwar kasar...
Rundunar sojin ’yantar da jama’ar kasar Sin ta PLA da ke yankin kudancin kasar, ta bayyana a yau Litinin cewa,...
Yanayin sayayya a fadin kasar Sin na tafiya yadda ya kamata yayin da aka kai tsakiyar lokacin hutun ranar kafuwar kasar na kwanaki 7, inda alkaluma na farko-farko ke nuna bunkasar da ke bayyana kuzarin da ke tattare da tattalin arzikin kasar. Cikin kwanaki 3 na farkon hutun, daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Oktoba, yawan masu shiga kantuna su yi sayayya ya karu da kaso 3.4, kana kudin shiga a manyan tituna da cibiyoyin sayayya 78 da ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar ke bibiya, ya karu da kaso 5.3, a mizanin shekara-shekara. Haka kuma, shirin gwamnati na bayar da rangwame yayin musayar tsoffin kayayyaki da sabbi, ya samu cinikin yuan biliyan 19.63, kwatankwacin dala biliyan 2.91 a lokacin, inda masu sayayya miliyan 3.48 suka ci gajiya. Hutun bikin ranar kafuwar kasar Sin daya ne daga cikin lokutan da aka fi yin tafiye-tafiye da sayayya da yawon bude. Hukumomi sun yi hasashen za a yi jimillar tafiye-tafiye biliyan 2.13 tsakanin lardunan kasar cikin kwanaki 7, inda matsakaicin na kowace rana zai kai miliyan 300. Alkaluma na baya sun nuna karfin bukatar tafiye-tafiye, inda a ranar 1 ga watan Oktoba kadai, yawan tafiye-tafiyen jiragen kasa ya kai miliyan 25.2, adadi mafi yawa a rana guda. (Fa’iza Mustapha)
Wani shirin hadin gwiwa tsakanin hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al’adu ta MDD (UNESCO) da dandalin Codemao na kasar Sin, mai koyar da ilimin sarrafa fasahohi ko Coding, na samun nasara wajen shigar da ilimin fasahar AI cikin makarantun da ke fadin nahiyar Afrika. A cewar Mary Nyasimi, kwararriyar mai tsara shiri a ofishin UNESCO da ke gabashin Afrika, AI da fasahohin dijital na sauya tsarin koyo da koyarwa a fadin nahiyar Afrika, inda suke samar wa dalibai muhimman dabarun da za su amfane su a nan gaba a bangarorin sana’o’i da kirkire-kirkire. Shirin na koyar da matasa ilimin sarrafa fasahohi ko Coding, wanda UNESCO da Codemao suka kaddamar a shekara ta 2021, na da nufin samar da ilimin fasahar AI da na Coding, mai aminci bisa daidaito da tafiya tare da kowa, a fadin nahiyar Asiya da Afrika. A cewar jami’ar, tsakanin shekarar 2021 da 2022, sama da malamai 200 daga kasashen Jamhuriyar Congo da Kenya da Namibia da Thailand, da suka hada da kaso 45 na mata, sun kammala shirin UNESCO na kasa da kasa na farko, na karbar horo kan Coding. Ta kara da cewa, shirin na amfani ne da dabarar koyar da mai koyarwa, inda sabbin malamai da aka horar suke koyar da dubban takwarorinsu da dalibai ilimin fasahohin Coding da dijital, a fadin nahiyar. (Fa’iza Mustapha)
Babban jirgin sama samfurin AG600 mai suna Kunlong da Sin ta kera a cikin gida, wanda ke iya tashi da sauka a kan doron kasa da cikin ruwa, ya kammala aikinsa na bana a Jiagedaqi da ke lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin. Kamfanin kera jiragen sama na kasar Sin wato AVIC ya bayyana a yau Litinin cewa, jirgin ya yi nasarar kammala ayyukan kai daukin gaggawa da na kare gobarar daji, na tsawon watanni 4 a sararin samaniya. Kuma yayin aikin na watanni 4, ya yi tafiye-tafiye domin sintiri sau 35, inda ya kwashe tsawon sa’o’i 100 na tafiya lami lafiya, ya kuma zubo da ruwa kimanin ton 390. Bisa la’akari da yadda yake iya shawagi a kusa da doron kasa kuma ba tare da gudu sosai ba, da karfinsa na daukar ruwa mai yawa da saukin sauya alkibla, jirgin ya nuna karfinsa na kai daukin gaggawa da kashe gobara a dazuka masu sarkakiya. Kasar Sin ce ta kera jirgin na Kunlong da kanta, domin biyan bukatun kasar na kashe gobarar daji da ayyukan ceto a cikin ruwa. Kuma shi ne irinsa mafi girma a duniya da ba na aikin soja ba, idan aka kwatanta da nauyin da yake iya tashi da shi. Nan gaba, jirgin zai shiga matakin aiki na yau da kullum, inda zai taimaka wa wani sabon samfuri mai karewa da kashe gobarar daji. (Fa’iza Mustapha)
Shugaban kasar Mozambique, Daniel Francisco Chapo, ya ce aikin gona yana da matukar muhimmanci ga Mozambique, don haka yana fatan...
A yau Lahadi aka kammala gasar wasanni ta nahiyar Asiya ta Aichi-Nagoya, bayan shafe makonni 2 ana fafatawa, inda Sin ta kankane teburin lambar yabo ta zinare, karo na 12 a jere. Kasar Sin ta kammala da lambobin zinare 169 da na azurfa 89 sai tagulla 83, karo na farko da ta nuna irin wannan bajinta a gasar ta nahiyar Asiya da aka yi a ketare. Kasar Japan ce ta zo a matsayi na 2 da zinare 83 da azurfa 95 sai tagulla 91, sai Koriya ta Kudu da ta rufa mata baya da zinare 39 da azurfa 43 da tagulla 68. ‘Yan wasa da jami’ai sama da 17,000 daga kasashe da yankuna 45 ne suka shiga gasar yayin da aka karya matsayin bajinta na duniya fiye da 50. Dan wasan tsere na kasar Thailand Puripol Boonson da ‘yar wasan ninkaya ta Sin Yu Zidi ne suka samu karramawar ‘yan wasa mafi daraja a gasar, a ajin maza da na mata. An mika tutar gasar daga hannun Aichi-Nagoya zuwa birnin Doha, da zai karbi bakuncin gasar wasannin ta nahiyar Asiya karo na 21.(Fa’iza Mustapha)
Asibitin tafi da gidanka na jirgin sojin ruwan Sin na Auspicious Ark, ya isa Conakry, babban birnin kasar Guinea jiya Asabar, domin fara ziyarar sada zumunta na kwanaki 7 da bayar da hidimomin kiwon lafiya. Wannan shi ne karo na farko da asibitin jirgin ruwan ya je kasar Guinea. Jirgin, wanda ke gudanar da shirin kiwon lafiya mai taken Mission Harmony-2026, ya isa tashar ruwa ta Conakry da misalin karfe 10 na safe agogon kasar. Jami’an gwamnati da na rundunar sojin Guinea da jakadan Sin a kasar da babban jami’in soji na ofishin jakadancin Sin da sauran ma’aikatan ofishin da mazauna birnin da wakilan Sinawa mazauna ketare da na kamfanonin Sin, sun taru a tashar domin tarbar jirgin. Yayin ziyarar shugaban shirin na Mission Harmony-2026, zai tattauna da shugabannin rundunonin sojin kasar Guinea. (Fa’iza Mustapha) )
Wakiliyar dindindin ta kungiyoyin agaji na Red Cross da Red Crescent na kasa da kasa (IFRC) a kungiyar Tarayyar Afrika da hukumomin kasa da kasa Asha Mohammed, ta ce suna daukar ayyukan hadin gwiwa da kasar Sin a matsayin mai matukar ma’ana kuma suna sa ran kara karfafawa da fadada hadin gwiwa da kasar a karin bangarori. Asha Mohammed wadda kuma ke jagorantar tawagogin IFRC na kasashen Habasha da Djibouti, ta bayyana haka ne yayin hirar da ta yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a gefen taron kara wa juna sani kan karfafa juriyar al’umma ga kungiyoyin agaji na Red Cross da Red Crescent, karkashin tsarin hadin gwiwar Sin da Afrika da ya gudana a Beijing. Cibiyar horo ta kungiyar Red Cross ta Sin ce ta karbi bakuncin taron na makonni 2 a watan Satumba, wanda kuma ya samu goyon bayan kungiyar IFRC Wakilai 26 daga kungiyoyin Red Cross da Red Crescent na kasashen Afrika 19, tare da wakilan IFRC, sun halarci lakcoci tare da yin ziyarce-ziyarce da tattaunawa yayin taron, inda suka yi musayar dabaru da daukar darusa daga dabarun Sin wajen rage barazanar annoba da kara juriyar al’ummomi da samar da ci gaba mai dorewa. A cewar Asha Mohammed, kasar Sin tana shiga ayyukan karfafa kwarewa a matakin Kungiyar Tarayyar Afrika, ciki har da wadanda ke mayar da hankali kan wadatar abinci da tsare-tsaren kiwon lafiyar al’umma, kuma tana gabatar da dabarunta masu daraja. (Fa’iza Mustapha)
Kasar Sin ta kammala aikin samar da babban bangaren tashar tura iskar carbon dioxide cikin kasa, da ke cikin teku, yayin da sabon dandalin rijiyar hakar iskar gas ta Dongfang1-1 ta shiga matakin kaddamarwa a yau Lahadi. Wannan aiki na gwaji, an tsara ta yadda zai rika tura iskar carbon dioxide da aka tara zuwa karkashin kasa domin bunkasa samar da iskar gas. Da zarar tashar ta fara aiki, za ta ba da damar adana ton sama da miliyan 1 na carbon dioxide a kowacce shekara, lamarin da zai rage fitar da hayaki mai guba a babban mataki, a masana’antar makamashi ta Sin ta cikin teku. Dandalin zai tara tare da tace carbon dioxide da aka samar tare da iskar gas, sannan ya matse, ya mayar da shi karkashin kasa. Wannan aiki zai inganta hakar iskar gas da kuma adana iskar carbon dioxide har abada. Rijiyar hakar iskar gas ta Dongfang 1-1, ita ce irinta ta farko da Sin ta samar da kanta, wadda ke cikin teku, kuma babbar rijiyar hakar gas mafi yawan iskar Carbon dioxide. Tun bayan fara aiki a 2003, ta samar da iskar gas cubic mita sama da biliyan 50. (Fa’iza Mustapha)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.