Shugaba Xi Ya Sha Alwashin Yin Aiki Tare Da Shugaba Trump Wajen Tafiyar Da Alakar Sin Da Amurka Bisa Turba Ta Gari
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da takwaransa na Amurka Donald Trump, wajen sarrafa babbar alakar dake tsakanin Sin da Amurka kan turba mai dacewa da makomarsu ta nan gaba. Shugaba Xi, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, cikin jawabin da ya gabatar bayan isarsa Amurka, yayin bikin tarba da shugaba Trump ya shirya masa a fadar White House, ya kuma yi kira game da bukatar karfafa tuntubar juna, da hadin gwiwa na hakika da kuma zama tare bisa jituwa. Xi, ya kuma ce a wannan karo yana gudanar da ziyara ce ta kawance, da hadin gwiwa, da kuma fatan kyautata rayuwar daukacin al’ummun kasashen biyu. Ya ce shi da takwaransa na Amurka na karfafa gwiwar hukumomin gwamnatocinsu, wadanda suka hada da masu nauyin gudanar da harkokin diflomasiyya, da tattalin arziki, da hadin gwiwar hada-hadar kudi, da na kare doka da musayar al’ummu, da su kara azamar karfafa tuntuba, da tallafawa majalisun dokokinsu a fannin yaukaka musaya da juna. Da yammacin ranar Laraba ne shugaba Xi ya sauka a sansanin sojojin sama na Joint Base Andrews, domin fara ziyarar aiki ta yini uku a Amurka. (SAMINU ALHASSAN)



















