An Bude Gasar Wasannin Asiya Ajin Masu Bukata Ta Musamman Karo Na Biyar A Nagoya
Da yammacin yau Lahadi ne aka bude gasar wasannin Asiya ajin masu bukata ta musamman karo na biyar a birnin Nagoya na kasar Japan. Kasar Sin ta aike da tawagar yan wasan motsa jiki 312, wadanda za su fafata a rukunonin wasanni 335 a sassan gasar 17. (Saminu Alhassan)



















