Li Qiang Ya Gana Da Shugaba Da Firaminista Na Kasar Tajikistan
Da safiyar yau Litinin 19 ga watan Oktoba, firaministan Sin Li Qiang ya gana da shugaban Tajikistan Emomali Rahmon da kuma takwaransa na kasar Kokhir Rasulzoda a Dushanbe, babban birnin kasar. A yayin da yake ganawa da shugaba Emomali Rahmon, Li Qiang ya ce, a halin yanzu, Sin da Tajikistan na ingiza gina kyakkyawar makomar al’ummarsu ta bai daya. Kuma Sin na fatan fadada cinikayyar shige da fice tsakanin kasashen biyu, da karfafa hadin gwiwa a fannin ababen more rayuwa, da hakar ma’adanai ba tare da gurbata muhali ba, da kara tuntubar juna, da fadada hadin gwiwa a sabbin masana’antu kamar tattalin arzikin yanar gizo da fasahar AI da sauransu, domin karfafa ci gaban tattalin arzikinsu. Ya kara da cewa, ya kamata bangarorin biyu su zurfafa hadin gwiwa wajen aiwatar da doka a fannin tsaro, da karfafa musayar bayanai, da yaki da “’yan ta’adda da masu tsatsauran ra’ayin addini da ’yan aware”, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin. Bugu da kari, Li Qiang ya ce, Sin na fatan karfafa mu’ammala da hadin gwiwa da Tajikistan karkashin tsarin gudanar da harkoki tsakanin mabambantan bangarori kamar su MDD da tsarin Sin da Asiya ta tsakiya, ta yadda za a aiwatar da manyan shawarwarin duniya guda hudu da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, da kuma gina kyakkyawar makomar al’ummar bil’adama ta bai daya. A nasa bangaren, shugaba Rahmon ya ce, Tajikistan na fatan kara zurfafa hadin gwiwa da Sin a fannin cinikayya da masana’antu, da noma, da makamashi da ma’adinai da zirga-zirga, da fasahar AI, da ingiza musayar al’adu. Haka kuma, Tajikistan tana goyon bayan manyan shawarwarin duniya guda hudu da shugaba Xi ya gabatar, kuma tana fatan karfafa hadin gwiwa da Sin a MDD da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai SCO, da tsarin Sin da Asiya ta tsakiya da sauransu, domin ingiza dangantakar hadin gwiwar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni ta sabon zamani tsakanin Tajikistan da Sin, da gina kyakkyawar makomar al’ummar kasashen biyu ta bai daya. Kazalika, a wannan rana kuwa, Li Qiang ya gana da takwaransa na kasar Tajikistan Kokhir Rasulzoda. A ganawar tasu Li ya ce, Sin a shirye take domin yin aiki da Tajikistan wajen bunkasa shirin hadin gwiwar ayyukan ci gaba mai inganci a tsakaninsu. Ya kuma kara da cewa, kasar Sin, na da niyyar daidaita dabarunta na ci gaba da Tajikistan, da karfafa hadin gwiwa ta fuskar cinikayya da zuba jari, da kyautata alaka, da ma’adanai marasa illa ga muhalli, da makamashi mai tsafta, da fasahar kirkirarriyar basira ta AI, da dai sauransu. Yayin da yake la'akari da halin da kasashe ke ci gaba da fuskanta na samun sauye-sauye masu sarkakiya, Li ya ce kasancewar su mambobi masu muhimmanci a kasashe masu tasowa, Sin da Tajikistan za su ci gaba da hada kai da kulla alakar kut da kut, domin kare muradun bai daya na kasashen biyu, da kare adalci da gaskiya a mu'amalar kasa da kasa. (Amina Xu, Suleiman Suleiman)



















