Mu Leka Sabbin Damammakin Cinikayyar Waje Na Sin Ta Hanyar Muhimman Bayanai Guda Hudu
Sin ta fitar da bayanan cinikin shige da fice na watanni tara na farkon bana a jiya Laraba, inda kafofin yada labarai na kasa da kasa, kamar Reuters suka yi sharhi kan hakan. Bayanan sun nuna cewa, a watanni tara na farkon bana, cinikayyar shige da fice ta Sin ta kai yuan tiriliyan 39.94, wanda ya karu da kashi 18.8% idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar da ta gabata. Daga cikinsu, yawan darajar kayayyakin da aka fitar daga kasar Sin zuwa ketare ya karu da kashi 16.4 %, yayin da yawan darajar kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin daga ketare ya karu da kashi 22.3%. A watan Satumba kadai, yawan cinikin waje ya kai yuan tiriliyan 5.16, wanda shi ne karon farko da ya zarta yuan tiriliyan 5 cikin wata daya kawai, kuma ya karu da kashi 27.5%. Matakin da ya bayyana ci gaba a bangaren yawan kayayyaki da ingancinsu baki daya, kuma an ci gaba da samun kyakkyawan ci gaba. Cinikayyar waje wata muhimmiyar kafa ce ta duba kuzarin tattalin arzikin Sin. A watanni tara na farkon bana, karfi da kuzarin ci gaban cinikayyar waje sun kara habaka, wanda hakan ya nuna cewa ginshikan tattalin arzikin Sin na ci gaba cikin dogon lokaci ba tare da sauyawa ba, kuma Sin na da kwarin gwiwa, da ikon cimma muradun ci gaban tattalin arziki da zamantakewa na duk shekara. A wannan rana kuwa, an bude bikin baje kolin cinikayyar shige da fice na Sin wato “Canton Fair” karo na 140 a birnin Guangzhou. Bayan shekaru 70, bikin “Canton Fair” ya zama muhimmin dandali mai amfani na Sin, a fannin fadada bude kofarta ga ketare, da ingiza gina tsarin tattalin arzikin duniya mai hade da kowa da kowa. A watan Nuwamban bana, za a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa kasar Sin daga ketare karo na 9 a birnin Shanghai dake gabashin kasar, yayin da za a gudanar da kwarya-kwaryar taron shugabannin mambobin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki na Asiya da tekun Pasifik wato APEC karo na 33 a birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin. Duniya na kara ganin yadda kofar Sin a bude take, kuma tafiya tare da Sin tafiya ce tare da damammaki. (Amina Xu)



















