Sin Da Kasashen Afrika Sun Gudanar Da Taron Tattaunawa Mai Taken Dunkule Harkokin Ciniki Da Zuba Jari A WTO
Yayin taron bita da nazari karo na 10 kan tallafawa harkokin ciniki da Kungiyar Ciniki ta Duniya ke gudanarwa, kasar...
Yayin taron bita da nazari karo na 10 kan tallafawa harkokin ciniki da Kungiyar Ciniki ta Duniya ke gudanarwa, kasar...
Kwamitin tsakiya na 20 na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ya gudanar da cikakken zamansa na biyar, daga ranar...
An gudanar da babban taro kan kirkire-kirkire da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba na Ziri Daya da...
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ko NBS, ta fitar da wasu alkaluma dake nuna yadda bunkasar samar da kayayyakin laturoni,...
Daga ranar Litinin 26 zuwa Alhamis 29 ga watan nan, kwamitin tsakiya na 20 na jamiyyar kwaminis ta kasar Sin, zai gudanar da cikakken zama na biyar a birnin Beijing. Zaman na wannan karo zai karkata ga tattauna manyan batutuwa dake shafar wanzar da cikakken ci gaba, da aiki tukuru a fannin jagorancin kashin kai na jamiyyar kwaminis. A matsayinta na jamiyya mai mulkin kasa, JKS na gudanar da taron kasa a duk shekaru biyar domin zaben sabbin membobin kwamitin koli, wadanda ke daukar nauyin jagorancin aikin dukkanin jamiyyar tsakanin tarukanta. Kazalika, taron na yin nazari da gabatar da manyan batutuwan jamiyya da kasa ta hanyar kiran cikakken zama na kwamitin tsakiya. Bisa tanadin kundin mulkin jamiyyar, kwamitin tsakiya yana gudanar da cikakken zama a kalla sau daya a duk shekara. Cikakken zama na biyar na kwamitin tsakiya na 20 na jamiyyar kwaminis ta kasar Sin, shi ne cikakken zama karo na biyar da membobin kwamitin kolin JKS da aka zaba a yayin cikakken zaman jamiyyar na shekarar 2022 suka kira. A shekarar nan ta 2026 ne ake bikin cika shekaru 105 da kafuwar JKS, kana a banan aka fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar biyar karo na 15, a gabar da ake dada ingiza cikakkun ayyukan sauye-sauye da samar da ci gaba a dukkanin sassa. Kiran cikakken zama na biyar a wannan muhimmin lokaci, mai jigon "cikakken ci gaba da aiki tukuru a fannin jagorancin kashin kai na jamiyyar kwaminis" a matsayin babbar ajandarsa, na nuni ga yadda jamiyyar kwaminis ta kasar Sin ke wanzar da muhimmin tsari na dogon lokaci da nufin karfafa gina kai. Bayan tafiya mai tsayi ta shekaru dari, JKS ta wanzar da ingiza ci gaba, da aiki tukuru a fannin jagorancin kashin kai, tana iza kanta, da samarwa kai karfi na hakika, mai ruhin yiwa kai kwaskwarima. Wannan ba wai tabbaci ne kadai na asali a fannin nasarar siyasa ga JKS wajen sarrafa akalar aikin zamanantarwa mai halayyar musamman na Sin, da kare babban kudurin sake farfado da kasa ba ne, har ma wani muhimman sirri ne ga duniya, ta yadda za ta iya fahimtar fifikon tsarin jagorancin kasar Sin, da cikakken salon ci gaban kasar na dogon lokaci da daidaito dake gudana bisa tsari. (Saminu Alhassan)
Manzon Allah (SAW), ya takaita cikin abincinshi da tufafinsa da wurin kwanansa a kan abin da ya zama darurar rayuwarsa (abin da dole ne da su za a rayu). Kudi in za ka iya ajiye su a inda ya dace, ya zama alkairi amma akasin haka sai tara kudin ya zama sharri. Manzon Allah (SAW) ya kasance mai tsantsaeni, bai dauwara wa rayursa cewa sai tufafi iri kaza zai sanya a jikinsa ba, duk irin wanda ya samu, shi yake amfani da shi. A zamanin rayuwar Annabi (SAW), ya kasance yana sanya abaya (duk rigar da take da tsagi a gaba, tun daga wuya har kasa) da zani, sabida ba al’adar larabawa ba ce sanya wando, wata rana Annabi (SAW) ya je kasuwar bani kainuka’a ya ga wando, sai ya ce wannan zai yi wa mata kyau, sabida ya fi suturce su a kan zani, ba laifi ne mace ta sanya wando ba sannan ta sa zani daga baya, sabida yanzun wando ya zama na maza duk da cewa, yanzun akwai nau’in wando irin na mata. Amma al’adar Larabawa, zani suke sawa, har yanzun mutanen Yamen, zani suke sawa. Manzon Allah (SAW) yana sa tufafi mai kauri mara santsi. Amma duk da haka, Annabi (SAW) yakan raba wa Sahabbai da bakinsa alkyabba ta afarma mai hula a baya, wata rana kuma ya raba alkyabba ta dibaje mai alhariri shi kuma ya dauki wacce ko kwalliya ba ta da shi. Yana rarraba kayayyakin da aka kawo masa na ganima ga wadanda suke kusa da shi da wadanda suke nesa da shi. Manzon Allah (SAW) ya hana maza sanya kayan alhariri, wata rana wani sarki ya aiko masa da alkyabba ta alhariri duk an mata kwalliya da zinari, sai Annabi (SAW) ya ce, wannan irin kayan wanda bai da rabo a lahira ne. sai Annabi (SAW) ya ce akai wa Sayyadina Umar, dan aike na zuwa ya mika wa Sayyadina Umar, sai ya amsa ya yo wurin Annabi (SAW) yana kuka, ya ce ya Rasulallahi ka ce irin wannan riga, ta wanda bai da rabo a lahira ne, Annabi ya yi murmushi ya ce, Ya Umar! Ba kai nace ka sa ba, dan’uwanka da ke Kafirci nake so ka ba wa. Malamai, sabida wannan suka yi fatawa cewa, in kana da aboki wanda ba Musulmi ba, za ka iya ba shi kyautar abin da Musulunci ya haramta, yanzun ba kai ka yi amfani da shi ba ake nufi. Alfahari da kayan sawa, ba su cikin dabi’un girma da daukaka, wannan sunnar mata ce, ado da kayan sawa sabida maigida ya gani ya ce ya yi kyau ba namiji ba. Ma’anar wannan shi ne, kar Mutum ya ga cewa, da kayan sawa yake samun daraja, kar ka yi wa wanda bai da shi alfahari, kar ka ki neman Ilimi sabida alfahari da tufafi, wannan ake nufi. Amma lallai, kaya suna daga cikin abubuwan da suke tsare mutunci. Shehu Sukairija ya ce wa Shehu Ibrahim Inyas “kar ka kara sanya kaya marasa kyau, na hore ka da sanya kaya masu kyau, duk wanda zai kalle ka, kayan jikinka kawai yake fara kallo”, Shehu Sukairija ya rasu tun wuraren 1953 amma tun a wannan zamani dabi’ar mutane ta canza. Amma alhamdu lillah… duk wanda ya ga hotunan Shehu na farko zai ga hakan amma daga baya hotunan Shehu sun sauya da kayan alfarma. Abin nufi a nan, kar mutum ya ga cewan, kayan ne ya ba shi daraja sai dai kawai al’ada. An ruwaito cikin wani Hadisi, Annabi (SAW), ya sanya wasu kaya, idan za a kiyasta kudinsu, za su yi kayan rakumi Tara (9). Lallai wannan kaya ne masu tsada da alfarma. Don haka, kowa ya sanya tufafi masu kyau amma kar ya ga darajarsa kadai a cikin tufafin. Abul Hasanil Shazali, shi ya fara wa Sufaye fada kan su fara sanya tufafi masu kyau, sabida al’adar Sufaye, sanya tufafi marasa kyau. Ya sha wuya sosai kan kokarin sauya tunanin sufaye kan fara amfani da tufafi masu kyau. Shehu Tijjani Abul Abas, ya kasance yana horar almajiransa da su dinga yi wa kayansu Bula (Ma’ana su dinga sabunta tufafinsu). Amru bin Hisham ya ruwaito hadisi daga Mahaifinsa, ya ce, Annabi (SAW) ya ce, “Innallaha yuhibbu an yara asra ni’imatihi ala abdihi” cewa, lallai Allah yana so ya ga gurbin ni’imarsa a jikin bawansa. In Allah ya yi maka ni’ima, yana so ya gan ta a tare da ita, wannan ita ce godiyar ni’ima, amma Allah ya yi maka ni’imah ka boye, kamar ka nuna wa Ubangiji cewa ba ka son Ni’imar ne, kana ce masa bai yi maka komai ba ko kuma nau’i ne na rowa. Ba laifi ba ne face alamun girma ne mutum ya yi sana’a ko aiki ya samu kudi ya sa tufafi mai kyau. Wata rana Annabi (SAW) ya yi wa’azi mai zafi ya zargi girman kai, sai wani sahabi ya tashi ya ce, ya Rasulallahi, Allah ya yi ni Mutum ne mai son ganin rawanina ya fi na kowa kyau da alkyabbata ta fi ta kowa kyau da takalmina ya fi na kowa kyau, sai Annabi (SAW) ya ce masa wannan ba shine girman kai ba, girman kai shi ne kin gaskiya da danne hakkin mutane. Amma halal dinka, duk tufafin da kasa mai kyau ba laifi. Abin da ake yabo a tufafi shi ne tsaftarsu, kazanta ba ta da mahalli a addini. Sai dai, ana son mutum ya dinga sanya tufafi tsaka-tsaki, in kai ba sarki ba ne, kar ka yi shiga irin ta sarakai, an so ka yi tsaka-tsaki, kai ba babban Alhaji ba, kar ka yi ta Asusu don ka sayi kaya irin na Babban Alhaji. Duk abin da ya zama a al’ada mutum mai wani girma ko wata daraja bai dace ya aikata ba ko ya sanya a jikinshi, to kar ka aikata hakan misali (A al’adar kabilar Hausa, Malami ba za a ganshi da gajeren wando ba). Shari’a ta zargi kaiwa kololuwa ko zama na karshe a kan sanya tufafi. Wanda Allah ya ba shi rufin asiri ya gode wa Allah ta hanyar amfani da abin da Allah Ya rufa masa asiri da shi, wannan zamani, ma’aunin bin Allah a wurin ‘yan duniya shi ne su ga duniya a tare da kai, don haka duk wanda Allah ya bai wa ni’imah ya gode masa ya yi amfani da ita ta hanyar yadda ya dace ba don neman girma a cikin ni’imar ba. Ya Allah ka ba mu ni’imarka a hannunmu ba a zuciyarmu ba! Aminn. An karbo Hadisi daga Sa’adu bin Abi Wakkas ya ce, Annabi (SAW) ya fada cewa “Arba’un minas sa’adati: Almar’atus salihatu wal marhalul wasi’u wal jarussalihu wal markabul hamiru” Abu guda Hudu (4) suna daga cikin arziki: Mace mai halin kirki ba na tsiya ba, da gida mayalwaci, da makwabci nagari mai halin kirki, da abin hawa mai sanya hutu ba mai rikici ba. “Arba’un minash shaka’i: “Almar’atus su’i wal jarussu’i wal markabus su’i wal maskanud dayyiku” Abu guda hudu (4) suna daga cikin tsiya: Mace mai halin banza, da makwabci mai halin banza kuma mai wuyar hali, da abin hawa mai wahalarwa, da gida kuntatacce. Ibn hibban ya ruwaito a cikin sahihansa. ...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya tattauna da takwaransa na Jamhuriyar Congo da kasashe masu amfani da harshen Faransanci, kuma Jami’i dake kula da ’yan Congo mazauna kasashen waje, Constant-Serge Bounda a jiya Alhamis, a Beijing babban birnin kasar Sin. A jawabin da ya gabatar, Wang ya yi kira ga bangarorin biyu da su yi kyakkyawan shiri game da taron kungiyar ministoci kan alakar hadin gwiwa tsakanin Afrika da Sin, wanda aka shirya gudanarwa a kasar Congo a shekara mai zuwa. Ya kuma kara da cewa Sin a shirye take ta yi aiki da kasashen Afrika, domin gina tsarin jagorancin duniya na gaskiya da adalci bisa daidai da muradun bai daya na kasashen kudancin duniya. A nasa jawabin Bounda ya ce, jamhuriyyar Congo, na goyon bayan jerin shirye-shiryen hadin gwiwa na duniya da kasar Sin ta bijiro da su, tare da tabbatar da cikakken goyon bayanta ga ka’idojin Sin. Ya kara da cewa, jamhuriyyar Congo na yabawa kasar Sin bisa gudummawar da take bai wa Afrika a fannin kula da lafiya, da taimakon da take ba ta, wajen yaki da cutar annobar Ebola da kuma karfafa ayyyukan bunkasa fannin kula da lafiya. Yana mai cewa, Congo a shirye take ta yi aiki tare da Sin domin hada hannu wajen karfafa ci gaban dangantakar Sin da Afrika. (Suleiman Suleiman)
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya buƙaci sabbin manyan sakatarorin da aka naɗa a jihar da su gudanar da ayyukansu...
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na Djibouti, Abdoulkader Houssein Omar, jiya Laraba a birnin Beijing. Yayin ganawar, Wang Yi ya ce Sin na daukar dangantakar abota bisa manyan tsare tsare tsakanin Sin da Djibouti da muhimmanci, kuma a shirye take ta zurfafa wannan dangantaka da Djibouti, yana cewa, ya kamata bangarorin biyu su ba manufar Sin ta soke haraji da fa’idjojin kasa na Djibouti, cikakkiyar damar taka rawar da ta kamata. A nasa bangare, Abdoulkader Omar ya ce tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, Djibouti take ta raya dangantakarta da Sin bisa ka’idojin aminci da girmama muradun juna. Ya ce a shirye kasarsa take ta ci gaba da bunkasa muhimmiyar dangantakar abota bisa manyan tsare tsare tsakanin kasashen biyu. Ministoci biyu sun kuma yi musayar ra’ayi mai zurfi kan yanayin da yankin kahon Afrika ke ciki da tsaron hanyoyin jiragen ruwa a tekun Bahr Maliya tare kuma da fitar da sanarwar hadin gwiwa kan tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kahon Afrika da tabbatar da tsaro a hanyoyin sufurin jiragen ruwa a tekun Bahr Maliya da gabar Tekun Aden. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
An gabatar da dimbin sabbin kayayyakin dake wakiltar sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, kamar mutum-mutumin injuna masu fasahar Kungfu, da na'urorin da aka kera domin taimakawa masu fama da matsalolin tafiya, da gilashin da ke amfani da fasahar AI, wadanda ke iya fassara da daukar hoto, a yayin bikin baje kolin hada-hadar cinikayya mafi girma da ake gudanarwa a kasar Sin, wanda aka fi sani da Canton Fair, lamarin da ya nuna himmar da aka yi wajen sabunta kayayyakin da ake nunawa yayin bikin na Canton Fair. To ko ta yaya aka kai ga dada sabunta kayayyakin da ake nunawa a yayin bikin da a bana ke cika shekaru 70 da kaddamarwa? Dalili na farko shi ne, kokarin da kasar Sin ke yi wajen ci gaba da yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, da kuma raya sabon karfi na neman bunkasa. A 'yan shekarun nan, kamfanonin kasar Sin da dama sun hada kafar intanet ta masana'antu da fasahar AI, cikin tsarin samar da kayayyaki, lamarin da ya janyo hankalin yan kasuwa daga sassan duniya. Ban da haka kuma, Sin tana da cikakken tsarin masana'antu, wanda ke tabbatar da samar da sabbin kayayyaki a kai a kai, tare da daidaita kayayyakin da aka kera a kasar Sin da bukatun kasuwannin duniya yadda ya kamata. Haka zalika, yadda kasar Sin ke ci gaba da kara bude kofa ga waje, da kafa dandalin hadin gwiwar tattalin arziki, da cinikayya mai inganci a tsakanin kasa da kasa dake dogaro ga Canton Fair, sun samar da karin damammakin samun sakamako mai gamsarwa ga dukkan bangarorin da ke harkar kasuwanci a duniya. Cikin shekaru 70 da suka gabata, bisa bunkasar kasar Sin, da yadda ta kara bude kofa ga waje, an ci gaba da sabunta kayayyakin da ake nunawa yayin Canton Fair, amma aniyar kasar ta kafa wannan dandali ba ta sauya ba, wato Hada kan kasa da kasa, domin cimma moriyar juna. A nan gaba kuma, Yayin da ake ci gaba da gudanar da shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15, kasashen duniya za su kara fahimtar kudurin kasar Sin na inganta manufar bude kofa ga waje, da kuma fadada fannonin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin kasa da kasa, wanda zai amfani dukkan bangarorin da abin ya shafa. Hakan ya nuna cewa, Canton Fair ba zai kare ba, kuma labarin hadin gwiwa da cimma moriyar juna a tsakanin kasa da kasa na ci gaba da bayyana. (Mai Fassara: Maryam Yang)
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.
© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.