Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150
Ma’aikatar aikin gona da kula da harkokin yankunan karkara ta kasar Sin ta sanar a yau Jumma’a cewa, yawan hatsin da kasar ta girbe da lokacin zafin bana ya kai wani sabon matsayi na tan miliyan 150.75, inda ya zarce adadin tan miliyan 150 a karon farko. Mataimakin ministan aikin gona da kula da harkokin yankunan karkara, Zhang Xingwang, ya fada wa wani taron manema labarai cewa, ya zuwa yanzu kasar ta samar da jimillar filayen noma masu inganci da suka haura hekta miliyan 66.7, lamarin da ya ba da damar girbe amfanin gona mai yawa da ke samun karuwa a jere. A rabin farko na shekarar, kasar Sin ta kuma kara kaimi wajen bunkasa masana’antarta ta samar da iri. A halin yanzu dai, nau’o’in amfanin gona da aka samar a cikin gida sun kai fiye da kashi 95% na jimillar wadanda aka shuka a filayen noma. (Abdulrazaq Yahuza Jere)



















