ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ba Mu Yarda Da Maƙiyanmu Ba, A Shirye Muke —Iran

by Idris Aliyu Daudawa
2 months ago

Ministan tsaron Iran na riƙo ya ce ƙasar ba ta yarda da maƙiyanta ba, kuma zaune ƙasar take a shirye wajen fuskantar duk wani hari, yana gargaɗin cewa idan aka karya yarjejeniyar tsagaita wuta za su mayar da martani cikin gaggawa da ƙarfi.

A cewarsa, Iran a shirye take ta kare kanta a kowane lokaci, inda ya jaddada cewa rundunar ƙasar na cikin cikakken shirin tunkarar duk wani hari daga waje.

Wannan jawabi ya zo ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da mataimakin firaministan Ƙatar kuma ministan tsaro, inda ɓangarorin biyu suka tattauna batutuwan tsaro da kuma yiwuwar ƙara haɗin gwiwar tsaro tsakaninsu.

ADVERTISEMENT

Ministan ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu ƙasashen waje ke shiga harkokin yankin, yana mai cewa hakan ba ya samar da tsaro sai dai yana ƙara rikici da rashin amincewa tsakanin ƙasashe, yana mai kira da a bar ƙasashen yankin su kula da tsaronsu da kansu.

Wannan dai na zuwa ne yayin da rikici ya ƙaru tun bayan hare‑haren Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, wanda ya sa Iran ta mayar da martani har da kai farmaki kan wasu wurare a Ƙatar.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

A yanzu haka, Ƙatar tare da Pakistan na ƙoƙarin shiga tsakani domin samar da yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin tsakanin Iran da Amurka.

Ba mu tsara wata tattaunawa da Amurka ba a Doha

Iran ta musanta iƙirarin Trump cewa za a fara sabbin tattaunawa da Amurka a Doha, tana mai cewa ba ta tsara wata ganawa ko tattaunawa da Amurka ba a wannan lokaci ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce wakilan ƙasar da ke tafiya Doha ba don tattaunawa ba ne, sai dai domin bibiyar batun kuɗaɗen ƙasar da aka ƙwace a ƙasashen waje.

Wannan matsaya na Tehran ya zo ne duk da cewa Trump ya bayyana cewa za a gudanar da ganawa tsakanin wakilan ƙasashen biyu a babban birnin Ƙatar.

Sai dai jami’an Iran sun musanta wannan batu, suna jaddada cewa babu wani shiri na ganawa ko tattaunawa da suka shirya yi da Amurka a kwanaki masu zuwa.

A wani ɓangare, Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kimanin dala biliyan 6 daga cikin biliyan 12 na kuɗaɗen Iran da aka ƙwace za su sake dawowa da su hannun gwamnati nan ba da jimawa ba.

Ya ce ana ci gaba da bin matakan da suka dace domin ganin an saki kuɗaɗen, wanda ake ganin zai taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar.

Haka kuma, Iran ta yi martani ga bayanan da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi, inda ta jaddada cewa ita kaɗai ce ke da ikon gudanar harkokin mashigin Hormuz.

Idris Aliyu Daudawa
+ postsBio
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tarihin Rayuwar Galadiman Kano Alhaji Tijjani Hashim (2)
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kyamar Baƙi: An Sake Kwaso Ƴan Nijeriya 83 Daga Afirka Ta Kudu
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Kamfanin Simintin Dangote Ya Tallafa Wa Manoma 60 Da Kayan Aiki A Edo
  • Idris Aliyu Daudawa
    https://hausa.leadership.ng/author/idris-aliyu-daudawa/
    Tsohon Shugaban Ƙasa Jonathan Ya Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Ƙasa 18 A Jihar Bauchi

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Muhimmancin Shan Ruwa Ga Kyawun Fata

Muhimmancin Shan Ruwa Ga Kyawun Fata

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.