ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Tsaro Da Tsadar Kayan Noma Na Barazana Ga Samar Da Abinci A Daminar Bana

by Yusuf Shuaibu
3 months ago
Tsaro

Kungiyar manoman Nijeriya (AFAN), sashen Jihar Kaduna ta nuna damuwa kan karuwar rashin tsaro da hauhawar farashin takin zamani, wanda ta ce matsalar tsaro da tsadar kayan noma na barazana ga samar da abincii a daminar bana.

A wani hira da shugaban kungiyar na jihar, Nuhu Aminu, ya ce manoma da dama a wasu kananan hukumomi suna fuskantar kalubale wajen samun damar zuwa gonakinsu saboda karuwar hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Aminu ya bayyana wasu sassa na Giwa, Kauru, Kubau, Kudan, Kajuru, Sanga, da Kachia a matsayin yankunan da ke fuskantar manyan matsalolin tsaro da ke shafar ayyukan noma.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, al’ummomin karkara da yawa yanzu suna cikin tsoro yayin da ‘yan ta’adda ke ci gaba da kai hari kan kauyuka da gonaki, suna tilasta wa manoma su daina girbe amfanin gonarsu.

Rashin tsaro na shafar ayyukan noma sosai. Wasu manoma ba za su iya zuwa gonakinsu ba saboda kai hare-hare da sace-sacen mutane a yankunansu.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Aminu ya kara da cewa lamarin ya rage karfin gwiwar manoma kuma zai iya shafar samar da abinci idan ba a dauki matakan gaggawa don inganta tsaro a cikin al’ummomin da ke gudanar da harkokin manoma.

Ya kuma bayyana hauhawar farashin taki a matsayin wani babban kalubale da manoma ke fuskanta kafin lokacin shuka.

Shugaban AFAN ya ce mafi yawancin kananan noma ba za su iya siyan takin zamani ba, saboda tsadar farashi, inda ya kara da cewa kungiyar na karfafa amfani shara a matsayin taki.

A cewarsa, yayin da takin gida yake da rahusa, yawancin manoma har yanzu suna fuskantar wahala wajen sayen isassun takin da suke bukata don gudanar da harkokin nomansu.

Ya yi kira ga gwamnatoci a duk matakai su tallafa wa manoma da taki da kayan gona tun kafin lokacin noma ya kai kololuwa.

Aminu ya ce akwai bukatar gwamnati da ta bayar da karin kulawa ga aikin noma ta hanyar samar da goyon baya ga manoma, yana jaddada cewa aikin noma na ci gaba da zama daya daga cikin manyan sassan da ke daukar nauyin tattalin arzikin kasar nan.

Haka kuma, a Jihar Katsina kuwa, ta’azzarar hare-hare ya kara tada tsoro a tsakanin mazauna yankuna, da dama daga cikinsu suna cewa rashin tsaro ya ci gaba da tabarbare ayyukan noma da kasuwanci a sassan Jihar Katsina da dama.

Shugabannin al’umma sun ce hare-hare da garkuwa da mutane masu maimaitawa a kan titin Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da sauran hanyoyin karkara sun tilasta wa manoma da dama barin gonakinsu, lamarin da ya kara tsananta rashin abinci da kuncin tattalin arziki.

Shugaban al’umma a Matazu, Malam Ibrahim Yusuf, ya ce mazauna yankin suna kara samun fargaba a lokacin da tafiya ta kama su.

“Mutanenmu suna rayuwa cikin tsoro. Manoma ba za su iya zuwa gonakinsu cikin ‘yanci ba, kuma matafiya a ko da yaushe suna cikin damuwa game da yiwuwar kai musu hari. Kowane sabon garkuwa da mutane na zurfafa damuwa da rashin tabbas a cikin al’ummominmu,” in ji shi.

Mambobin kungiyoyin al’umma a kananan hukumomin Matazu da Batsari sun bayyana al’amarin a matsayin babbar matsala da jihar ke fuskanta.

A yayin da yake zantawa da manema labarai, Musa Lawal, wani mamba a daya daga cikin kungiyoyin, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi su kara kokari wajen yakar ‘yan bindiga.

“Sace tsohon janar na soja ya nuna a fili cewa babu wanda yake da kariya. Muna bukatar a dauki mataki na gaggawa tare da karfafa bayanai sirri da kuma ci gaba da ayyukan soja don rusa wadannan kungiyoyin masu laifi,” in ji shi.

Wata mai fafutukar kare hakkin al’umma, Aisha Bello Sani, ta ce tasirin rashin tsaro a kan tattalin arzikin yankin ya zama mai tsanani.

“Yawancin kasuwanni ba sa aiki kamar yadda ya kamata, an rufe harkokin kasuwanci, kuma samar da kayan amfanin gona ya ragu saboda mutane na jin tsoron zuwa gonakinsu. Tsaro yana da alaka kai tsaye da tattalin arziki,” in ji ta.

Tsaro
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Sin Tana Adawa Da Karin Takunkumin Da Amurka Ta Sanya Wa Cuba

Sin Tana Adawa Da Karin Takunkumin Da Amurka Ta Sanya Wa Cuba

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.