ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buƙatar Mayar Da Hankali Wajen Kawo Ƙarshen Ciwon Sikila A Nijeriya

by Sulaiman
3 months ago
sikila

Amosanin Jini wanda aka fi sani da ciwon Sikila, abu ne da aka shafe shekaru ana fama da ita a cikin alumma, musamman duba da cewa, ana gadon ta ne, a cikin Jiini.

A saboda haka ne, aka keɓe ranar 19, na kowanne watan Juni, domin gudanar da zagoyarwar ranar, domin a tausayawa, masu fama da ita, a ɗaukacin faɗin duniya.

Taken taron na 2026, “ Cike Giɓin da ake Dashi da Baiwa Masu Fama da Cutar kulawar da ta kamata, musamman a ƙasar nan,”.

ADVERTISEMENT

Bincike ya nuna cewa, a Nijeriya, ana da masu fama da ciwon da dama, wanda hakan, ya ɗara na sauran ƙasashen duniya.

Wasu alƙaluma sun nuna cewa, a Nijeriya a duk shekara,  aƙalla ana haihuwar jarirai masu ɗauke da cwon da suka kai yawan150,000

LABARAI MASU NASABA

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

Wannan adadin, ya nuna cewa, sama da Jariran 100,000 da aka Haifa da ciwon, suna rasuwa, tun kafin su kai matakin binkin su na shekarar haiwa.

Wani abin dubi a nan, shi ne, wannan adadin na Jariran, ba fa wai suna rauswa saboda annobar ƙarancin abinci ko yanayi na yaƙi ba, amma kan lamarin ciwon da za a iya maganinsa, tun bayan da aka haifi Jariran.

Muna taɓa bayyana wa, a wannan shafin cewa, matsalar da fannin kiwon lafiyar ƙasar ke ci gaba da fuskanta, ba wai na rashin samar da kayan kiwon lafiya ba ne, amma batu ne, na rashin samar da kyakywan shugabanci, a ƙasar.

Kazalika, za a iya cewa, shakulatin ɓangaro da gwamnatocin baya da suka mulki ƙasar yi, han ya ƙara sanya ƙaruwar ciwon, a ƙasar.

A gafe ɗaya, idan aka yiwa Gwamnatin mai ci adalaci, a zagowar ranar ta 2026, ta fara gudanar da ranar ce, ta hanyar taron maneman labarai.

Misalili, Ministan Kiwon Lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate, a taron na manema labarai, ya bayyana ƙoƙarin da Gwamnatin ke yi, na inganta fannin kiwon lafiyar ƙasar, a ƙarƙashin shirin kula da kiwon lafiya na zuba jari wato RII.

Ya ce, an kafa Cibiyo shida na yaƙar ciwon a shiyyoyin ƙasar, tare da sanya masu kayan aiki na yin gwaje-gwaje, inda ya ƙara da cewa, an samar da tsarin yiwa Jariran da aka haifa gwaji a jihohin Legas, Kano da Abuja.

Ya ci gaba da cewa, an kuma horas da sama da masu bayar da horo, 700 kan sanin Jinsin Jini, inda kuma Ma;aikatasa, ta tantace Jarirai, sama da 38,000 a Abuja, tare da kafa guraren yin rijistar cututtuka guda 10,000 a ɗaukacin Cibiyoyi 25, da ke faɗin ƙasar.

Tabbas, wannan ɗaukar babban matakai ne da suka zo kan gaɓa, na yaƙi da ciwon, wanda hakan, ya sanya muke yabawa Ma’aikatarsa.

Sai dai, a gafe ɗaya, ba za mu yi rashin adalaci, ga masu karanta Jaridar mu ba, musamman duba da yadda miliyoyin ƴan ƙasar 40, musamman waɗanda ke ci gaba da ɗauke da ciwon,  matuƙar ba mu sanar da yawan adadin masu ciwon ba.

Mun ɗora hijjar mu ne, kan cewa, samar da shirin na ƙasa a jihohi uku kacal, tamkar tsoma Allura ce, a cikin Teku, duba da yawan ƙasar ƴan ƙasar, da suka mai sama da miliyan 220, wanda hakan ya nuna a zahiri cewa, waɗanna Cibiyoyin, ko kusa ba su wadaci ƙasar ba.

Kazalika, hakan ya ƙara nuna wa a zahiri, na irin giɓin da ake da shi, a fannin na kiwon lafiyar ƙasar.

Kusan dai, za a iya cewa, a duk matakin Ma’aikatun ƙasar an shafe shekaru, ana tattaunwa kan batun kiwon lafiyar ƙasar, amma har yanzu, lamarin, bai sauya Zani ba.

Wani bincike da Lancet Haematology ya wallafa ya nuna cewa, yaran da ke fama da larurar a ƙasar, sun kai ruɓi huhu, da za su iya mutuwa, kafin su kai shekaru niyar, da haihuwar su

Abin takaicin shi ne,  mahukuntan ƙasar ba su  mayar da hankali, kan ciowan, musamman wajen tattaunawa a matakin ƙasa, musamman lamarin da za a ɗauka, na gaggawa.

Misali,  ana gudanar da yin gamgamin a yi amfani da Ragar gidan Sauro, domin daƙile kamuwa da zazzaɓin cizon Sauro, haka ciwon shan Inna wato Foliyo da cutar Sida, ana ware maƙudan biliyoyin kuɗaɗe a faɗin duniya, domin yaƙar cutar.

Amma abin baƙin ciki  shi ne, larurar ta Sikila da ke hallaka sama da yara ƴan Nijeriya masu shekaru biyar da haihuwa, an mayar da ita Mowa, musamman duba da cewa, idan aka gudanar da taron manema labarai kan gangamin wayar da kai a kanta, daga baya sai kaji, shiru, kamar an shuka Dosa.

Ba za a lumaunci hakan, ya kuma zama wajbi, mahukuntan ƙasar, su sake yin tuninin kan batun.

Abinda aka fi buƙata a  mayar da hankali a yanzu shi ne, dole samar da kuɗaɗe tare da ci gaba da sanya ido, domin a ɗauki, matakan da suka dace, na magance ciwon.

Kazalika, ya zama wajbi, a ƙara faɗaɗa shirin yin gwaji ga Jariran da aka haifa wanda zai wuce, tsayar da shi, a jihiho uku kacal na ƙasar.

Haka zalika, dole a samar da magin rage raɗaɗin ciwon wato Hydroɗyurea, a matakan hukumomin duba lafiya na matakin farko da ke a ɗaukacin faɗin ƙasar.

Dole ne, Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa wato NHISA, ta sanya ciwon na Sikila a cikin jerin jaddawalin da za yiwa masu larurar magani.

Bugu da ƙari, akwai babban nauyin kan matakan gwamnatin jihohi da na ƙananan hukumomi, na su mayar da hankali kan magance ciwon, ta hanyar samar da shirye-shirye.

A ɓangaren ƴan Nijeriya, suma ya zama wajbi a kansu, su cire batun soyayya a gafe, amma su tabbatar da sun je sun yi gwajin sanin Jinsu na Jini, kafin su yi aure.

A ɓanagen guarren ibada, kamar su Masallatai da Ikilisiyya, ya wajaba, su ƙara ƙaimi, wajen jan hankalin mabiyansu, kan mahimmancin yin gwajin Jini, kafin yin aure.

Ba wai za a iya ciki giɓin da ake da shi a ƙasar nan na ciwon bane, ta hanyar yin taron manema labarai, kaɗai ba, inda kuma a gafe ɗaya, a duk shekara ake samu yaran da suka kamu da ciwon 100000, suna rasa rayukansu.

sikila
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa
  • Sulaiman
    Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

MASU ALAKA

sikila
Ra'ayinmu

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

August 14, 2026
Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG
Ra'ayinmu

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

July 31, 2026
Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
Ra'ayinmu

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

July 10, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya Da Cibiyar IITA Za Su Bunkasa Noma Ta Fasahar Zamani

Bankin Duniya Ya Ɗora Tashoshin Apapa Da Tincan Kan Sikelin Maki Na 20 A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.