ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba

by Ra'ayinmu
2 months ago
Jos

Lolaci ya yi da za a kawo ƙarshen yadda wasu marasa imani, a ƙasar nan, ke ɗaukar doka a hannun domin ɗaukar rayukan ƴan Nijeriya, alhali ba tare da sun aikata wani laifi ba.

Wannan batun, yazo dai dai da yadda a ranar 21 ga watan Yunin 2026, gungugun wasu fusatattun mutane, a kan hanyar  Maraban Jos zuwa garin Zariya a jihar Kaduna, suka yiwa wata Malamar addinin Musulunci Malama Malama Ummulkhair, Usman Aliyu, kisan gilla, ta hanyar ƙone ta da ranta.

Mariganyiyar, mai ƴaƴa biyar, fusatattun mutanen, sun ƙone ta ne, bisa zargin wai, ta saci yara.

ADVERTISEMENT

Wani ƙarin abin baƙin ciki shi ne, kisan gillar ba wai ya auku kai tsaye, a kan titi bane, domin baiwar Allah tuni an miƙa ta a ofishin ƴansanda, kan zargin satar yara, amma duk da haka, gungun marasa imanin suka yiwa ofishin na ƴansandan na Maraban Jos ƙawanya.

An yi zargin cewa, yawan gungun mutanen ne, ya sa suka fi ƙarfin jami’ian ƴansanda da ke a ofishin, wanda hakan ya tilasata su, miƙa matar ga fusatatun mutanen, inda su kuma suka ɗauki doka a hannun su, ta hanyar babbake ta, inda za a iya haka, ya nuna cewa, akwai gazawar samun bayanin sirri.

LABARAI MASU NASABA

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

Kazalika, aukuwar wannan mummunan yanayi, ya nuna zahirance, na irin sakaci a ɓangaren mahukunta na kare rayuwar waɗanda suke mulka, musamman wanɗada ake tsare da su, a hannun su.

Bayanan da masu gani da ido, a lokacin da lamarin ya auku, musamman kan zargin da aka yiwa DPO ɗin ofishin, na cewa,  shi da kansa ne, ya miƙa matar ga gungun fusatattun muatene da suka yi cirko-cirko a a wajen ofishin, ya nuna irin rashin iya ƙwarewar aiki, na ƴansanda.

Kazalika,  duk da ankararwar da wani ganau a wajen ya yi, na cewa, miƙa matar ga mutanen, zai iya sanya ta rasa ranta, amma DPO ɗin, ya yi ƙememe da shawarar tata.

Haka zalika, ita wata mata a wajen ta yi ƙoƙarin shiga tsakani, amma mutanen suka yi barazar ƙona ta.

Waɗanan zarge-zargen, sun yi hannun Riga da iƙirarin da da DPO ɗin ya yi, na cewa, gungun mutanen sun yi yunƙurin nuna ƙarfin Tuwo, na kaɓar matar da tsiya.

A ɓangaren rundunar ƴansandan jihar ta kawai yi tir da aukuwar lamarin ne, tare da cafko mutane 24 tare da kuma kamo ƙarin wasu, da ake zargi, da aikata wannan  halin na dabbacin tare.

Ya zama wajbi, a gaggauta  gudanar da bincike, zargin rawar da DPO ɗin ya taka da kuma sauran jami’ansa, da ake zargi da hannun kan lamarin, indan an same su da laifi, a hukunta su, kamar yadda dokar ƙasa ta tana.

A ɓangaren mijinta Malam Muhammad Aliyu kuwa, ya bayyana cewa, bayan aukuwar lamarin, ƴaƴansu, sun ci gaba da tambayarasa, shin, ina Mamansu take.

Lamarin ya jefa rayuwar ɗansu mai shekaru 14, a cikin ƙuncin damuwa, tare da yawan furta sai ƙwatowa mahaifiarsu, haƙƙinta.

Ya zama wajibi, rundunar ƴansanda ta ƙasa, ta biya isashiya diyya ga iyalan mariganyiyar.

Gazawar da ƴansanda na rashin kare rauywar waɗanda suke tsare da su a ofis ɗinsu, hakan ne, bai wa ƴan Nijeriya damar, ɗaukar doka a hannun su, inda haka ke ci gaba da zama babar haɗari, musamman kan batun zargin satar yara.

Wannan lamarin zai kuma iya ci gaba da aukuwa, inda a wata rana, zai rkiɗe zuwa dabar siyasa, ko rikicin ƙabilanci, ko kuma addini, da sauran rikice-rikice.

Kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, ya bai wa kowanne ɗan ƙasa, damar yin rayuwa da kare ƴancinsa.

Sai dai, abin baƙin cikin shi ne, Malama Ummulkhairi, ba ta samu wannan kariyar daga gun ƴansanda na kare ranta ba

Ƙungiyoyin addnin Musulunci da dama, kamar irinsu, MULAN, sun yi tir da aukuwar lamarin, tare da yin kira, da a gudanar da cikakken bincike.

Bugu da ƙari, ya zama wajibi, Gwamnatin Kaduna da rundunar ƴansanda ta ƙasa, su ɗauki matakan gaggawa, musamman domin a gudanar da cikakken bincike, tare da tabatar da an hukunta DPO ɗin da wasu jami’ansa, da ake zargi.

Ba za ci gaba da lamuntar yadda wasu ƴan Nijeriya ke ɗaukar doka hannun su ko kuma yiwa dokar karan tsaye, ba tare da wasu ƙwararan hujoji ba, bai kuma kama ace, Jinin Malama Ummulkhairi, ya tafi a banza ba.

Jos
Ra'ayinmu
+ postsBio
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Buƙatar Samar Da Alƙibla Ta Musamman Ga Gidajen Gyaran Hali Na Ƙasar Nan

MASU ALAKA

Jos
Ra'ayinmu

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

August 14, 2026
Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG
Ra'ayinmu

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

July 31, 2026
Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
Ra'ayinmu

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

July 10, 2026
Next Post
Jos

Shekara 200 Bayan Shehu Ɗan Fodiyo: Hubbarensa Na Ci Gaba Zama Wajen Ziyara Da Neman Tabarruki

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.