ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?

by Ra'ayinmu
3 months ago
Nijeriya

Bayan ɓarkewar annobar Ebola, Afirka ta Yamma, shekaru sha biyu da suka, gabata, ƙwayoyin cutar sun kuma sake ɓulla, a yankin.

Sai dai, sake ɓullar cutar, wannan sabuwar cutar, ta zo da wani irin yanayi, na da ban, duba da yadda annobar, ke ci gaba da haifar da fargaba, ga masauna yankin.

Irin wannan fargabar, suma ƴan Nijeriya, sun faɗa a cikinta, duba da cewa, ƙasar, ita ma, ƙasar, ta taɓa tsintar kanta, a cikin annobar, wadda ta sha da ƙyar.

ADVERTISEMENT

Tuni dai, Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO, ta yi gargaɗin cewa, duba da yadda cutar ke ƙaruwa, tamkar wutar dare, akwai yuuwar, ƙara ƙaruwa, a Afirka ta Tsakiya.

An ruwaito Darakta Janar na Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce, akwai wasu ƙyaoyin cutar, kimanin 600 da suka ɓulla, yankin.

LABARAI MASU NASABA

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

Kazalika, an ƙiyasta cewa, mutane 139 da suka kamu da cutar, sun mutu, a sassa da ban da ban, na Jamuriyar Dimokiraɗiyyar Kango, da kuma a Uganda.

An dai yi hasashen cewa, wannan adadin, mai yuwa ya ƙaru, saboda gaza gano ƙwayoyin cutar.

Hukumar ta tabbatar da ƙaruwar cutar, zuwa 51, musamman wadda aka riga, aka tabbatar da ita, a Knogo.

A Kongon ne, dai, aka fara sanar da ɓarkewar cutar, inda kuma maƙwabciyarta, Uganda, aka tabbatar da wasu ƙyayoyin cutar, tare da mutuwar mutum ɗaya, a birnin Kampala.

An ruwaito cewa, cutar ta fara ɓulla ne, a Ituri da kuma a Kiɓu, ta tsaiya, da ke a Kongo.

Sabuwar cutar, mai nau’in da ake kira a turance Bundibugyo, har yanzu, ba a gano magungunan da za a iya warkar da ita ba.

Wannan na ƙara haifar da wata fargaba, a tsakanin ƙwararrun kiwon lafiya, musamman duba cewa, fannin kiwon lafiya a yankin, na fuskantar ƙalubale.

Kado yake dai, Gwamnatin Tarayya, ta yunƙoro, wajen bai wa ƴan Nijeriya tabbacin cewa, har yanzu, ba a samu ɓullar ƙyayar cutar, a ƙasar ba.

Farfesa Muhammad Ali Pate, Ministan kula da Kiwon Lafiya ya ce, tuni Gwamnatin, ta ɗaukan kota kwana, na daƙile yuwar ɓullar annobar.

A cewar Hukumomin Kula da Kiwon Lafiya na ƙasar kamar irinsu cibiyar daƙile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa, na kan ci gaba da bibiyar lamarin.

Kazalika ya ce, an kuma gabatar da tsare-tsaren ɗaukar matakan yin gwaje-gwaje, a ɗaukacin mashigar ƙasar, ciki har da Filayen saukar Jiragen sama da Tashohin Jiragen Ruwa da  a iyakokin ƙasar.

An kuma ƙara ƙarfafa ɗakunann gwaje-gwaje, na duba marasa lafiya, domin a samu damar, saurin gwano ɓullar, ƙwayoyin cutar.

Ya ƙara da cewa, an kuma ankarar da jami’an kiwon lafiya, da kasance, masu sanya ido, da kuma ɗaukar matakan kariya na cutar, tare da saurin killace, duk wanda ya kamu da ita.

A ɓangaren matakan da Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa wato FAAN, ta tabbatar da cewa, ta ɗauki matakan kota kwana, na tantace duk fasinjan da shigo cikin ƙasar, daga ƙetare, musamaman wanɗa suka taso, daga yankunan da cutar, ta fi yin ƙamari.

 Ana kuma ci gaba da yin gangamin, wayar da kai da ilimantar da ƴan Nijeriya, musamman na wanke hannuwansu da nesantar, waɗanda suka kamau da annobar.

Har yanzu dai, ƴan Nijeriya, basu manta da annobar wadda ta ɓarke a 2014  a Afirka ta Yamma ba, inda ta .annobar dai, ta fara ɓulla ne, a Kongo, a 1976.

Kazalika, ta kuma ɓulla a ƙasar Guinea before, daga bisani, ta yaɗu zuwa ƙasashen Sierra Leone da Liberia, ta kuma ba zu, zuwa wasu ƙasashe, ciki har da Nijeriya Birtaniya, Amurka, da kuma Spaniya.

Bayan ayyana annobar, a 2016, sama da mutane 28,600 ne, suka kamu da ita, inda kuma sama da mutane 11,000, suka mutu.

Ɓarkewar cutar, a waɗancan shekarun, ya nuna a zahri, irin raunin da tsaron kiwon lafiya ya yi ƙamari, a ɗaukacin ƙasashen da ke Afirka

Sai dai, a wancan lokacin, irin namijin ƙoƙarin da tsohon Ministan Kiwon Lafiya na ƙasar Farfesa Onyebuchi Chukwu da kuma a ɓangaren hukumomin Kiwon Lafiya na ƙasar, hakan ya taƙaita, ƙazantar yaɗuwar cutar a ƙasar.

An dai samu ɓullar annobar guda 20 ne, kacal, a Legas da garin Fatakwal, inda mutane takwas, suka rasu.

Bugu da ƙari, mahukuntan ƙasar, sun yi nasar, gano sama da ƙwayin cutar guda 1,400, inda suka samu nasara, daƙile yaɗuwarsu

Bisa namijin ƙoƙarin ɗaukar matakan gaggawa da Nijeriya ta yi a wancan lokacin, ta samun ɗimbin yabo, daga wasu ƙasashen duniya.

Haka zalika, tarihin ɓarkewar ƙwayoyin cutar a 2014 a ƙasar, ba zai cika ba, ba tare da tuna sadaukarwar da ƙwarar Likita, Stella Ameyo Adadeɓoh, ta yi, na sadaukar da ta yii ba, musamman wajen daƙile yaɗuwar ta.

Stella dai, ta dage kai da fata, na hana Jakadan ƙasar Liberiya Patrick Sawyer, wanda ya shigo cikin ƙasar da ƙwayar cutar, daga barin Asibitin da aka kwantar da shi.

Sai dai, a ƙarshe, Stella, ta kamu da cutar, daga baya, ta mutu.

Ya zama wajibi, cutar ta zama izina ba wai ga ƙasar nan ba kawai, har da ɗaukacin Afirka.

Akwai buƙatar, a ci gaba da zuba jari a ɓangaren binciken kiwon lafiya da samar da ingantattun kayan aiki da kuma inganta walwala, da jin daɗin malaman kiwon lafiya.

Har ila yau, akwai buƙatar a rinƙa ɗaukar matakan gaggawa, tun kafin annobar ta ɓarke

Koda yake dai, Hukumar WHO, ta ce, cutar ba ta kai ga yin ƙamari ba, amma ta yi gargaɗin cewa, shafe watanni, kafin  maganinta, ƙwayar cutar na Bundibugyo, ya wadata.

Nijeriya
Ra'ayinmu
+ postsBio
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Buƙatar Samar Da Alƙibla Ta Musamman Ga Gidajen Gyaran Hali Na Ƙasar Nan

MASU ALAKA

Nijeriya
Ra'ayinmu

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

August 14, 2026
Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG
Ra'ayinmu

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

July 31, 2026
Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
Ra'ayinmu

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

July 10, 2026
Next Post
Yadda Siyasar 2027 Ta Ƙara Zafafa Harkokin Daba A Kano

Yadda Siyasar 2027 Ta Ƙara Zafafa Harkokin Daba A Kano

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.