ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Buƙatar Taka-tsan-tsan Wajen Koya Wa Yara Ƙanana Azumi

by Rabi'at Sidi Bala
3 months ago
Azumi

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban, waɗanda suka shafi al’umma. Ciki sun haɗar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba game da abin da ya shafi yadda za a koyawa ƙananan yara yin azumin Ramadan. Duba da yadda wasu iyayen ke tilastawa ƙananan yara yin azumi har su kai dare, duk da irin ƙarancin shekarun yaron da kuma galabaitar da yaro ya yi, a haka za a tilasta ya kai dare. A wani ɓangaren kuma, akwai matasan da sun wuce ace koyo za su yi, amma ba za su yi azumin ba, duk da irin ingantacciyar lafiyar da suke da ita. A cewar iyayensu idan sun yi aure sa yi, ko kuma idan sun ƙara hankali sa yi.

  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 10
  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 8

Dalilin hakan ya sa shafin TASKIRA jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu; “Ta wacce hanya ya kamata iyaye su koyawa yaransu ƙanana yin azumi?, Daga shekara nawa ya kamata a fara koyawa yara azumi?, Wacce shawara ya kamata a bawa iyayen da suke zbaa ido ‘yaƴansu ba sa yin azumi alhalin sun girma?.

ADVERTISEMENT

Ga dai bayanan nasu kamar haka;

Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta, Ƙaura-Namoda, Jihar Zamfara:

LABARAI MASU NASABA

Sharrin Da Ke Tattare Da Jifan Iyali Da Munanan Kalamai

Ra’ayin Matasa Game Da Auren Kusa Da Na Nesa

Yin azumi tilas ne ga kowane Musulmi, yana da kyau iyaye su koya wa ‘yaƴansu yin sa ta hanyar dabara tun suna ƙananu. Misali; za a ce yaro ya ɗauki azumi daga safe zuwa ƙarfe sha biyun rana, sai a kife kwano ko roba a ce masa an ajiye masa azuminsa ya ci abinci, wata rana kuma sai a saka shi yin na safe zuwa ƙarfe ɗaya ko biyu na rana, a haka za a dinga koya masa dangana da juriyar yin azumin, har zuwa lokacin da girmansa ya kai yin sa kamar yadda kowa yake yi babu ‘break’. Yara ƴan shekara bakwai zuwa sama, su ya dace a dinga koya wa azumi, saboda ko sallah daga lokacin aka ce iyaye su tsayu a kan ‘yaƴansu idan ba su yi ba a dake su. Gaskiya duk iyayen da ke hana yara azumi da niyyar sai sun yi aure su yi ko a ce sai sun ƙara hankali; illa ce babba suke yi wa ‘yaƴansu. Saboda komai na duniya idan ana son ganin alfanunsa da sannu-sannu ake farawa kafin a cinma matakin nasara. Domin ba lalle ne su iya yin azumin a lokacin da ake son su yi ba, matuƙar tun farko ba a koya musu yadda ake yin shi a daidai gaƙar da ya dace ba.

Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, Rijiyar Lemo, Ƙaramar hukumar Dala, Jihar Kano:

Azumi na daga cikin manyan ibadu masu gwaggwaɓan lada, saboda matsayin azumi ko adadin ladansa ba a bayyana ƙarara ba kamar yadda aka bayyana wasu ibadun. Hanyar da za a fara koya wa yara azumi ita ce, a riƙa tashin su lokacin yin sahur, a yi sahur ɗin tare da su. Yawanci ma mu a ƙasar Hausa yara sukan nuna zaƙuwa da yin azumin, to a nan iyaye sai su ƙarfafa musu gwiwa, su bar su su yi. Idan kamar lokacin zafi ne bayan kamar wani lokaci misalin ƙarfe 1 zuwa 2 idan an ga yaro zai galafaita, ana cewa ya karya azumin. Su kuma iyaye masu nuna so ga ‘yaƴansu, suna hana su yin azumin, su sani kuskure ne suke yi ba.

Sunana Hafsat Sa’eed, daga Jihar Neja:

Yaro tun yana shekara shida zuwa 7 ya kamata a koya masa yin azumi, ko da ya yi rabi ne sai ya ajjiye. Hanyar koyawa yaro shi ne, a tashe shi yayi sahur, kar a barshi ya ci komai ko ya sha komai da zarar gari ya waye har sai ya kai rabin ranar. Wanda kuma suke yin shekaru amma ba sa azumi ya danganta da tarbiyyar gida, ko rashin kular iyaye, ko kuma rashin takurawa yaro.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano:

Da farko ko da ace ba a tashi yaron a lokacin sahur ba to, ko da safe ne za a iya gaya masa ya ci wannan abincin yayi sahur yanzu, kuma a faɗa masa idan ya ci ya ɗauki azmi, don haka babu ci ko shan wani abun har sai ya kai azmin. Sannan ban da mugun zagi ban da cin zali, sannan ya dinga sallah akan lokaci da sauransu. Kamar ƴan shekara 5 ma zuwa sama. Gaskiya ba sa kyautawa kuma an fi samun haka ga mata, shawarata a nan ita ce dole iyaye su nuna musu cewa azumi fa yana daga cikin shika-shikan musulunci, kuma dole iyaye su riƙa nunawa yara shi azumi wata rahama ce a gare mu, domin har ƙara mana lafiya yake yi. Allah kasa mudace.

Sunana Hassana Iyayi Yahaya, daga Kano:

Hanya ta farko su fara ɗana rabin rana, idan 12pm ta yi a bawa yaro abinci ya ci, a haka- a haka har zai iya gwada yi wata rana. Daga shekara bakwai haka shida duk za su iya gwadawa na rabin rana. Allah ya kyauta wannan babu lissafi a cikinsa gaskiya na rasa abin faɗa a nan.

Sunana Muktari Sabo, Jahun, Jihar Jigawa:

A fara kwaɗaitar dasu irin ladan da me azumi zai samu da kuma irin abubuwan da Allah yake rabawa a wannan watan, Addini dai yana so a fara koyawa yara addini tun suna ƙanana wato kamar shekara bakwai zuwa goma, amma ya danganta da yanayin da yaron yake rayuwa. Matsalar da ke janyo wa, wasa da addini sakamakon rashin sanin addinin ta hanyar watsi da karatun addini tun suna yara sun fifita wasanni da neman duniya fiye da neman ilimin addini. Wanda wannan matsalar ita ce take kai matasanmu har su girma babu ruhin addini a tare da su, kuma shi ke saka su wasa da ibada Allah ya shiryar damu.

Sunana Muhammad Isah, Zareku Miga, A Jihar Jigawa:

Kar a bawa yaro abinici da safe sai kamar 11am wasu ma suna ganin jariri maishan nono za ka iya ƙin bashi nono sai lokaci zuwa lokaci, musamman idan ya sha da dare sai a ɗan bashi lokaci zuwa 10am safe ko 11am. Daga shekara 7 ya kamata a fara koya wa yaro Azumi. Eh, hakan na faruwa mafi akasari yafi ƙarfi a wajen ƴan’uwanmu Fulani, ka ga mutum ya girma amma ba ya Sallah ballatana Azumi. Shawara, iyaye su koyawa yaransu addini tun suna yara su tashi da shi. Kuma a riƙa tura su makarantar addini da ta zamani.

Sunana Nura Garba, Tsanyawa, A Jihar Kano:

Cikin zantukansu su riƙa faɗar falala da daɗin azumin, ba wai wahalar sa ba. Sannan sai su riƙa ƙarfafa gwiwar yara wajen yin azumi ko da 12 na rana suka yi a haka za su dage wataran. Yara a ƙalla ɗan shekaru 5 zuwa 7 har sama, domin shekaru ne da yara ke saurin ɗaukar abu akan su ba tare da ya goge ba. Shawara iyaye masu irin wannan rashin hankalin, su sani ‘ya’ya nauyi ne akan iyaye, ci da tarbiyya da ilmantarwa, ba gata bane ka bar ɗanka yana ƙin yin addini alhalin zai iya, domin idan bai saba ba, ko ya girma ba zai yi ba.

Sunana Anas Bin Malik Achilafiya, Ɗankwashi, Jihar Jigawa:

Abu na farko shi ne su zama abin koyi, domin yara sukan fi koyo ta ganin abin da manya ke yi. A fara da azumin rabin yini ko Ƴan sa’o’i, a riƙa ƙarfafa su da yabo maimakon tsawa, sannan a bayyana musu ma’anar azumi a hankali da haƙuri, ladabi, da tausayi. Haka kuma, kula da lafiyar yaro yana da muhimmanci, musamman a sahur da iftar. Ana sabawa yara yin azumi tun daga shekara 7 zuwa 10, gwargwadon ƙarfinsu. A wannan mataki ba dole ba ne su cika yini, amma a koya musu a hankali. Idan suka kai balaga, azumi ya zama wajibi a gare su idan babu uzuri na lafiya. Iyaye su guji watsi da al’amarin, ya dace su yi nasiha cikin tausayi, su fahimci dalilin ƙin azumin, su kuma haɗa tattaunawa da addu’a da ƙarfafawa. Matasa ya kamata su gane cewa azumi ibada ce mai girma wadda ke gina haƙuri da kamun kai.

 

Azumi
Rabi'at Sidi Bala
+ postsBio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A 29-05-2027
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa

MASU ALAKA

Azumi
Taskira

Sharrin Da Ke Tattare Da Jifan Iyali Da Munanan Kalamai

May 10, 2026
Ra’ayin Matasa Game Da Auren Kusa Da Na Nesa
Labarai

Ra’ayin Matasa Game Da Auren Kusa Da Na Nesa

April 19, 2026
Yaudara
Taskira

Yawaitar Yaudara Tsakanin Masoya A Wannan Zamanin

February 15, 2026
Next Post
Me Ya Sa Ake Yawan Nuna Wa Vinicius Wariyar Launin Fata?

Me Ya Sa Ake Yawan Nuna Wa Vinicius Wariyar Launin Fata?

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026
An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Magadan Gari Na 2026 A Beijing

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.