ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yawaitar Yaudara Tsakanin Masoya A Wannan Zamanin

by Rabi'at Sidi Bala and Sulaiman
4 months ago
Yaudara

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban, wadanda duka shafi al’umma.

Tsokacinmu na yau, zai yi duba game da abin da ya shafi yaudara. Inda shafin TASKIRA ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da yadda alamomin yaudara suke, tare da abin da ke janyo yaudara, da kuma neman sanin wata hanya da idan aka yi yaudara za ta zama ba komai ba, har ma da shawarwari ga masu aikata yaudara.

Ga dai bayanan nasu kamar haka:

ADVERTISEMENT

 

Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano, A Jihar Kano:

LABARAI MASU NASABA

Sharrin Da Ke Tattare Da Jifan Iyali Da Munanan Kalamai

Ra’ayin Matasa Game Da Auren Kusa Da Na Nesa

Son rai da son zuciya, wasu kuma daukar fansa. Hakuri da kuma addu’a. An taba yaudara ta, na ji babu dadi sosai, domin har yanzu idan na tuna raina yana matukar baci, sai idan na tuna cewa duniyar ma barinta za mu yi sai na ji sauki a raina. Shawarata ita ce, mu ji tsoron Allah, domin wallahi mu sani duk wanda muka yaudara akwai hisabi, sannan duk abin da kasan baka so ko idan an yi maka za ka ji babu dadi to kada ka yi wa wani. Allah ya sa mu dace, amin.

 

Sunana Princess Fatima Mazadu, Goben Nageria:

Yaudara kala-kala ce, duk da dai ita yaudara aba ce marar kyau, amma akwai wacce ake yinta dan fidda kai, akwai wacce ake yinta sabanin shari’a, wato ta sabawa al’adu da shari’a. Yadda mutum zai ta zakewa wajen kalamai, da yadda zai ta bibiyar mutum ko ina dan son cimma burinsa. Kamar irin biyan bukata ta karatu ko ta sana’a dan a koya maka yadda za ka yi za ka biya, sannan ka daura mutumin akan kalaman yaudara, yadda mafi akasari ake samu da an cimma buri babu sauran karkafa mutunci ko zumunci. An taba yaudara ta sosai a fannin kasuwa da soyayya, na sha kalubale wanda har yanzu ba na ganin akwai mai share min wanann hawayen, sai ubangijina. Yaudara a soyayya kam cuta ce da zalunci babba, amma a fannin kasuwa ko wasu abubawan da sauki, saboda illar dukiya ce, amma ta zuciya cuta ce babba. Ni dai a wuri na yaudara-yaudara ce, Allah ya tsare mu da masu yinta, ya dada kare mana zuriyarmu bakidaya.

 

Sunana Aminu Adamu, Malam Madori, A Jihar Jigawa:

To ita dai yaudara tana faruwa ta kowane bangaren maza da mata, kuma a lokuta da dama tana faruwa ne a lokacin da aka gina soyayyar akan karya da kuma son abun duniya, wanda hakan ke jawo a samu canjin ra’ayi a kowane lokaci. Eh gaskiya ni a nawa tunanin babu, domin yaudara tana iya jawo wa a rasa rayuwa, don haka babu yadda za a yi abin da zai iya yiwa mutum silar rabuwa da rayuwar sa ya zama babu komai yin sa. To magana ta gaskiya an yaudare ni ba sau daya ba, kuma yanayin da nake samun kai na a ciki babu dadi. To shawarata, ya kamata mu ji tsoron Allah mu sani yaudara mummunar dabi’a ce wadda ka iya cutar da mutum, don haka mu guje ta.

 

Sunana Fatima Nura Kila, Jihar Jigawa:

Da yawan lokuta namiji kan makance a kan soyayya har idanuwansa su rufe, ya gaza gane macen da ta ke son shi dan abun hannunsa, sannnan wasu mazan akwai dadin baki. Gaskiya kusan babu, sabioda yaudara ba ta da dadi ga mace ko namiji, mutum ya gama sa ran shi zai samu abun, amma a zuciyar daya daga ciki ba haka bane, sai tsantsar yaudara. Gaskiya ba a taba yaudara ta ba, saboda yawanci ‘yan yaudara ma ana gane su, amma wani lokacin mu mata sai mu rufe Ido akan hakan. Masu yi maza ko mata su ji tsoron Allah, kome za su yi su rika tuna wa da Allah yana kallonsu, hakan zai sa wasu su daina aikata haka.

 

Sunana Labaran Jibrin, Zareku Miga, Jihar Jigawa:

Yaudara wata aba ce mara kyau da ‘yan mata da samarin zamani kan yi a soyayya. San rai da nacin sai an biya wa kai bukatar zuci, ya sa ake amfani da wasu abubuwa kamar; kudade, da ababen hawa, da kuma sutura. Rashin bayyana asali yana daya daga cikin alamun yaudara duba da yadda yawancin masu yaudara ke boye asalinsu ya yin gabatar da kai a wurin bayyana soyayya, sukan kokarin martaba kawunan su, su samu karbuwa. Boye asalin halayya yana daga cikin yaudara, idan mutum na son wani, ya kan tsarawa kansa sauye-sauyen halayya ta yadda zai yi amfani da wasu halayyar da ba nasa ba, domin ya yi nasarar sace zuciyar wanda zai yaudara. An taba yaudarata, amma ban ji da dadi ba, wannan dalilin ya sa bana sha’awar inga wani yana niyyar aikatawa.

 

Sunana Hafsat Sa’eed, Jihar Neja:

Rashin gaskiya shi yake janyo yaudara, kana tare da mutum ashe ba sonka yake dan Allah ba, ko kuma ba zai iya taimakonka da zuciya daya ba, in har ba ka yi masa karya ko yaudara ba, ko a soyayya ka nuna babu wani sai shi kadai, ko ta wani abu tukunna zai iya dauka ya baka. Kai kuma kana cikin matsuwa ba lallai mutum yayi maka abun a lokacin da kake so ko kuma ya baka ba, sai ka yi masa karya da yaudara. A nawa ganin babu laifi idan ka yi yaudara tunda zamani ne ya taho a haka, kuma su ma masu yin ba za su yi ba, sai ka saka yaudarar a ciki. Allah ya sa mu dace.

 

Sunana Anas Bn Malik, Achilafia Yankwashi, A Jihar Jigawa:

Yaudara tana bayyana ne ta hanyar karya, boye gaskiya, da rashin rikon amana, tana jawo lalacewar dangantaka da rashin yarda tsakanin mutane. Abubuwan da ke janyo yaudara sun hada da; son zuciya, kwadayi, hassada, rashin tsoron Allah, da matsin rayuwa. Wasu na aikata wa ne saboda rashin ilimi ko sakaci da illar da ke tattare da ita. Idan aka yi yaudara, tuba ta gaskiya, neman afuwa, da gyara kuskure na iya rage illarta, amma ba kasafai ta zama ba komai ba gabadaya, domin amana tana wahalar dawowa. Shawara ita ce, su sani cewa gaskiya tana daukaka mutum, ya yin da yaudara ke kawo riba ta dan lokaci, amma tana haifar da asara mai girma a karshe.

 

Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Jihar Kano:

Alamar yaudara dai bata wuce a zo wa mutum da abu gan-gan kamar da gaske, sai tafiya ta yi tafiya ka ji shiru kamar an shuka dusa. To, abubuwa da yawa ka iya jawo wa, wani kuma tsautsayin a yaudare shi ne kawai. Ai duk yaudara -yaudara ce gaskiya, ba’a taba yaudara ta ba.

 

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos a Jihar Filato:

Batun yaudara a soyayya ko tsakanin manema abu ne mai tsananin sosa rai, da birkita hankali. Yaudara tana nuna cin amana da rashin cika alkawari. A yayin da ka sallama zuciyarka ga wanda ku ke soyayya tare da tunanin shi ne zai zama abokin rayuwarsa na har abada, idan daga baya ta bayyana cewa wanda ka ke so din nan ba haka ya dauka a zuciyarsa ba. Abin da matukar daga hankali. Karya da rashin cika alkawari, da kwadayi, da cin amana su ne suke sa a samu yaudara a tsakanin masoya. Don haka ya kamata mu sani cewa, idan har Allah Ya yi alkawarin sakantawa masoya masu nuna wa juna kauna tsakani da Allah to, babu shakka maciya amana da mayaudara ma za su samu nasu sakamakon.

 

Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:

Yaudara wasu maza na zuwa gun mata ba da niyar aure ba sai dan yaudara, za su nuna maka cewa da gaske suke suna sanka, amma ba haka bane yaudare ce ta kawo su, ba sa nuna wata alama da za ka gane yaudara ce. Yaudara a wanan zamani ya zama rowan dare gun maza da mata amma maza sun fi yaudara. Shawara, masu irin wanan hali yaudara su ji tsoron Allah, kuma su tuna duk abin da ka yi wa wata ko wani za a yi maka, babu makawa. Allah ya ba mu dacewa.

 

Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, Rijiyar Lemo, karama hukumar Dala, Jihar Kano:

Abubuwan da ke jawo yaudara suna da yawa, kuma sun bambanta daga mutum zuwa mutum. Muhimmai daga ciki akwai, rashin shiryawa da niyyar yin aure. Akwai mummunanar manufa a zukatan wasu mazan, sukan yaudari mata ba ta fuskar bata musu lokaci, sukan yaudare su sosai da dukkan wani abu na jan hankalin mutum, sawa’un abin duniya, kyautatawa, tausayawa, kalamai masu dadi ko kuma wani abin da zai sa mace ta nutsu da mutum har ta saki jiki da shi, daga karshe kuma ya bayyana bakar manufarsa idan ba a yi sa’a ba ma macen ta ba da kai bori ya hau. Akwai yaudara ta kiyayya ko daukar fansa. Alamomin yaudara sun hada: yawaita yabon abokin soyayya a gabansa da gaban wani nasa, kin fada masa gaskiya ko kuskurensa don kada ya ji haushi, yi masa dukkan abin da ya bukata da sauransu. Babu wata hanya ta yaudara da za ta zama ba ta illa.

Yaudara
Rabi'at Sidi Bala
+ posts Bio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Al’umma Suka Gudanar Da Bukukuwan Sallah Duk Da Matsin Tattalin Arziki
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A 29-05-2027
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Yadda Za Ku Tattala Kuɗaɗen Da Ke Shigowa Hannu Domin Ci Gaban Rayuwa
Yaudara
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili
  • Sulaiman
    Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo
  • Sulaiman
    Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli
  • Sulaiman
    Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

MASU ALAKA

Yaudara
Taskira

Sharrin Da Ke Tattare Da Jifan Iyali Da Munanan Kalamai

May 10, 2026
Ra’ayin Matasa Game Da Auren Kusa Da Na Nesa
Labarai

Ra’ayin Matasa Game Da Auren Kusa Da Na Nesa

April 19, 2026
Buƙatar Taka-tsan-tsan Wajen Koya Wa Yara Ƙanana Azumi
Taskira

Buƙatar Taka-tsan-tsan Wajen Koya Wa Yara Ƙanana Azumi

February 28, 2026
Next Post
CMG Ya Shirya Bikin Kade-Kaden Fim Na Kasashen Sin Da Italiya A Birnin Rome

CMG Ya Shirya Bikin Kade-Kaden Fim Na Kasashen Sin Da Italiya A Birnin Rome

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026
Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

Za A Fara Buga Gasar Kofin Sarkin Gombe Bayan Masu Ruwa Da Tsaki Sun Cimma Matsaya

June 3, 2026
Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

Hada Kai Da ’Yan Awaren Yankin Taiwan Ba Zai Haifar Da Ɗa Mai Ido Ba

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.