ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharrin Da Ke Tattare Da Jifan Iyali Da Munanan Kalamai

by Sulaiman and Rabi'at Sidi Bala
2 months ago
Iyali

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba game da maza masu jifan matansu da munanan kalamai. Wasu daga cikin maza idan matansu suka bata musu rai, sai su rika jifansu da munanan kalamai, kamar; jahila, dabba, mahaukaciya, jaka, da dai sauransu.

Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin TASKIRA  game da wannan batu; “Ko me ya sa suke yin hakan?, ko akwai wasu matsaloli da hakan zai iya haifarwa?, Ya namiji ya kamata ya kasance a duk lokacin da matarsa ta bata masa rai yake cikin fushi?”.

ADVERTISEMENT

Ga dai bayanan nasu kamar haka;

Sunana Princess Fatimah Mazadu, daga Gombe:

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Matasa Game Da Auren Kusa Da Na Nesa

Buƙatar Taka-tsan-tsan Wajen Koya Wa Yara Ƙanana Azumi

Zallar rashin hakuri ke damun wasu mazan, inda wasu kuma jahilci da karancin iya zamantakewa, inda wasu ke daukar hakan mataki ne na matan su rika jin tsoronsu a kowanni lokaci. Ba shida wani amfani sai karin bakin ciki da jefa abokin zaman cikin bakin ciki da da-na-sani mai yawa, wasu lokutan irin shi har fada mummuna ke shiga tsakani. Raini, jayayya, mace-macen aure da sauransu. Shawara ya kasance mai hakuri da nuna mazantaka wurin dauriya har ta sauko su daidaita, ba wai ya hau dokin zuciya ba. Dole watarana a saba amma a rika kiyaye harshe saboda mummunan furuci, su rika hakuri da mazajen nasu. Sannan su rika kokarin hakuri wajen mayar musu raddi ko mummunar addu’a, saboda ba a taru an zamo daya ba. Kuma mace ita ce ke neman aljannah a kasansa dole tayi masa biyayya da kaucewa yawan fushinsa gudun fadawa wahalar kiyama.

Sunana Samaila Muhammad MGN:

Hakika wannan ba dabi’a mai kyau ba ce, ba kuma za ta samar da al’umma nagari ba, ko da ba matanka ba bai kamata ka jefe ta da irin wadannan muna nan kalamai ba. Tabbas hakan zai sa yaran su tashi da mummunan tarbiyya, domin iyaye malamai ne masu koyar da iyalansu mai kyau ko mara kyau. Ba komai bane ake daga hankali har rai ya baci a rika fadin maganganun da basu dace ba a gaban iyali, a rika hakuri da juna.

Sunana Fatima Nura kila, Jihar jigawa:

Gaskiya kusan duk wanda zai rika aibata matar sa ko jifanta da wadannan kalaman tabbas akwai jahilci a tare da shi. Tabbas akwai matsala musamman a gaba, domin shi ma za a iya yi wa ‘ya’yansa ko ‘ya’yansa su daina ganin darajar sa a matsayinsa na mahaifinsu. Namiji yayi hakuri idan ya sakko sai su fahimci juna kowa ya fahimta abin da yayi ba daidai bane.

Sunana Aminu Adamu, Malam Madori A Jihar Jigawa:

To, magana ta gaskiya mutum mai Ilimi ba zai kira matarsa da irin wadanan sunaye ba, domin sam-sam hakan bai dace ba, ko da rai ya baci to, ya kamata a rika kai zuciya nesa. Tabbas akwai matsaloli ma da yawa domin zamantakewar auren kanta ta dauko hanyar lalacewa, domin zamantakewar aure tana dadi ne idan ana ganin mutuncin juna. To, shawarata a nan ita ce, dole ne mace ta zabi miji nagari kamar yadda namiji yake son auren mace tagari, domin shi ne zai san mutuncinta kuma yake mutunta ta a zamantakewar aure dama mutunta iyayenta da ‘yan’uwanta.

Sunana Munzali Bala Musa, Adakawa Dala LGA, Jihar Kano:

Duk namiji me irin wannan halin ya sani kamar yana rusa gidansa ne domin yana da ‘ya’ya, idan aka yi wa ‘ya’yansa zai ji dadi?. Shawara ga ‘ya’ya mata ku zamanto masu hakuri da biyayyar aure Allah ne zai biya ku da aljannah.

Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:

Gaskiya maza na irin wanan sosai, kuma na ji dadin wannan maudu’in gaskiya. Saboda ina jin ba dadi sosai ga masu irin wannan hali, haka ya faru da wata mata a gaba na sun yi fada sai ya fada mata magana mara dadi kuma har ya cire hannu zai mareta, gaskiya haka ba yi bane maza. Eh gaskiya haka na haifar da matsala musamman in yara suna ganin hakan na faruwa shi ne za su koya su kai gaba. Shawarata ga masu irin wanan hali su ji tsoron Allah su bari, kuma su tuna yara amana ce Allah ya basu duk abin da suka ga iyayensu nayi shi za su dauka. Allah ya bamu dacewa.

Sunana Anas Bin Malik, Achilafiya Ƴankwashi , A Jihar Jigawa:

Gaskiya wasu ba sa tunanin illar abin ga iyali da yara, ko yadda hakan ke lalata mutunci da soyayya. Wannan dabi’a na iya jawo matsaloli kamar rushewar aure, damuwa, rashin kwanciyar hankali, da kuma tasirin tunani ga yara. Haka kuma yana rage darajar mace da mutuncinta a gida. Namiji ya kamata ya koyi hakuri, ya dan janye kansa idan fushi ya taso, ya yi shiru na dan lokaci kafin magana. Yin magana cikin nutsuwa da mutunta juna shi ne hanya mafi dacewa.

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:

Dabi’ar dan’adam ce a lokacin da yake cikin fushi yana aikata abubuwa marasa kyau, daga ciki akwai fadar maganganu cikin zafafan kalamai, da daukar wasu matakai wadanda daga baya mutum yake nadamar abin da ya aikata, bayan ya huce. A saboda haka ne addinin Musulunci ya koyar da mu yin shiru a lokacin da ran mutum ya baci, ko ya zauna idan a tsaye yake, ko ya kishingiɗa idan yana zaune, ko kuma yayi alwala ya samu ya yi nafila, ya roki ubangiji ya sanyaya masa zuciya. Sai dai kuma ga magidanta, bai kamata suna tunzura juna da kalamai marasa dadin ji ba, alhalin akwai ‘ya’ya a tsakaninsu. Mace ta rika gaya wa miji duk abin da ya fito daga bakinta, ba tare da tunanin ya dace ko bai dace ba, yana tunzura namiji har idanunsa su rufe ya aikata wani abin da bai kamata ba. Don haka ina mai yi mana nasiha da mu guji barin zuciyarmu tana angiza mu muna aikata abin da bai dace ba.

Sunana Lawan Isma’il (Lisary):

Rashin sanin yakamata ne ya sa hakan, ai ba ma iya yaran da suka haifa za a iya yi wa haka ba, suma kansu za a iya yi musu ammafa wasu matan su ma suna jifan mazajensu da irin wadannan kalmomin. Matsala da dama kuwa domin hakan wulakanta dan’adam ne, sannan ko da mutum ba ya halin dabbobin to, kamar ana yi masa baki ne. Ana so namiji yayi hakuri ya ma fita daga cikin gidan idan ya dan huce sai ya nuna mata abin da tayi ko take yi ba shi da kyau. Shawarata a nan ita ce namiji bai kamata yana furtawa matar sa da ya nemi aurenta da kansa irin wadannan kalaman ba, kamata yayi maza da matan su riga hakuri.

Sunana Buwangal Taraba:

Fushi, rashin tarbiyya, da tunanin iko. da yawa ba sa tunanin za a iya yi wa ‘ya’yansu haka. Yana kashe soyayya, yana koyar da yara zagi, yana jawo rabuwa, kuma zunubi ne, lokacin fushi namiji ya yi shiru, ya fita, ko ya yi alwala. Maza ku ji tsoron Allah, matar ka amana ce,. ka tuna mahaifiyarka kafin ka zagi mace. Mata ku yi hakuri, ku yi addu’a, ku yi nasiha idan ya huce. idan ya huce ki nemi dattijai. Kalma tana karya zuciya. kada ka fadi abin da ba ka so a ce maka.

Iyali
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita
  • Sulaiman
    Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya
  • Sulaiman
    Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Sabon Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano
  • Sulaiman
    Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu
Iyali
Rabi'at Sidi Bala
+ posts Bio
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    Bukatar Rike Sirri A Tsakanin Ma’aurata
  • Rabi'at Sidi Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiat-sidi-bala/
    GORON JUMA’A

MASU ALAKA

Ra’ayin Matasa Game Da Auren Kusa Da Na Nesa
Labarai

Ra’ayin Matasa Game Da Auren Kusa Da Na Nesa

April 19, 2026
Buƙatar Taka-tsan-tsan Wajen Koya Wa Yara Ƙanana Azumi
Taskira

Buƙatar Taka-tsan-tsan Wajen Koya Wa Yara Ƙanana Azumi

February 28, 2026
Yaudara
Taskira

Yawaitar Yaudara Tsakanin Masoya A Wannan Zamanin

February 15, 2026
Next Post
Bayan Harkar Fim, Sayar Da Abinci Ne Babbar Sana’ata – Aisha Yola

Bayan Harkar Fim, Sayar Da Abinci Ne Babbar Sana’ata – Aisha Yola

LABARAI MASU NASABA

NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

June 25, 2026
Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

Adadin Injunan Samar Da Wutar Lantarki Da Sin Ya Wuce Kilowatts Awa Biliyan 4, Wato Ya Kai Ga Matsayi Na Farko A Duniya

June 25, 2026
Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Sabon Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

Gwamna Yusuf Ya Naɗa Muhuyi A Matsayin Shugaban Sabon Kwamitin Yaƙi Da Miyagun Ƙwayoyi A Kano

June 25, 2026
Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

Wani Gidan Adana Kayan Tarihi Na Sin Ya Fitar Da Rahoton Yadda Dakarun Japan Suka Rika Zubawa Mutane Jinin Dabbobi Yayin Yakin Duniya Na Biyu

June 25, 2026
Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

Wang Yi Ya Yi Kira Da A Gaggauta Bude Mashigin Hormuz

June 25, 2026
Ƙungiyar NPCF Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Ga Tinubu

Ƙungiyar NPCF Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Ga Tinubu

June 25, 2026
Firaministan Sin Ya Halarci Taron Tattaunawa Da Wakilan ‘Yan Kasuwa Mahalarta Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na DAVOS

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Tattaunawa Da Wakilan ‘Yan Kasuwa Mahalarta Dandalin Tattalin Arzikin Duniya Na DAVOS

June 25, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Kotu Ta Ɗege Shari’ar Ganduje Da Wasu Mutum 7 Zuwa 14 Ga Oktoba 2026

Kotu Ta Ɗege Shari’ar Ganduje Da Wasu Mutum 7 Zuwa 14 Ga Oktoba 2026

June 25, 2026
An Fara Gasar Tseren Dawakai Ta ‘Renewed Hope’ da Sabon Salo A Kano

An Fara Gasar Tseren Dawakai Ta ‘Renewed Hope’ da Sabon Salo A Kano

June 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.