ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Kula Da Tarihi A Musulunci

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
4 months ago
Tarihi

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah Ta’ala wa Barakatuhu. Mauludi ma’anarsa tuna haihuwar wani shugaba, wani gwarzo, wani babba, da ya kawo wani taimako a cikin ‘yan-Adam gaba daya ta ko wacce hanya; hanyar ilmi, hanyar cigaba, hanyar tattalin arziki, da sauransu, har ya koma zuwa ga Allah, ‘yan-Adam suka yi amfani da wannan abu da ya kawo kuma suka amfana. To yana daga cikin gode masa, yana daga cikin abin da zai sa wadanda za su zo daga baya su yi koyi dashi, a rika tunawa dashi ana fadar wadannan abubuwan da yayi.

Haka kuma Mauludi yana iya daukar tuna wata rana da aka sami wani alheri a kasa ko a gari ko a yanki (misali: ranar samun ‘yancin kai), masanan a nan Nijeriya muna yin Mauludi duk ranar 1 ga watan Oktoba saboda tunawa da ranar samun ƴancin kai namu, domin a tuna gwarazan da suka yi gwagwarmayar samo mana wannan ƴanci, domin mu fahimci meye ma yancin kai, don mu san ya za a yi mu kawo cigaba ga kasarmu, mu san ya za a yi mu rike kasarmu da kyau ba tare da sakaci ba. Wani misali kuma, idan an taba samun wani tashin hankali ko rashin zaman lafiya (Allah ya kiyaye) sai kuma daga baya aka samu yin sulhu, to wannan ranar sulhun ma za a iya kiyaye ta a rika tunawa da ita. Alkur’ani ya fada mana cewa, bani Isra’ila sun nemi Annabi Isah AS, ya nema daga Ubangijinsa cewa, a saukar musu da abinci daga sama, ya yi musu fada akan cewa “me ya kai ku neman wannan? Kuna shakkar Allah ne?” Sai suka ce “A’a ba haka bane, kawai muna so muga gaskiyar ka ne!”. Sai Annabi Isah ya roki Allah, yace “Allah ga abin da mutane na suka fada, Ni dai na yi imani”. Sai al’ummar Annabi Isah din suka ce masa “muna so mu riki wannan rana da abincin zai sauka ta zama, ‘idan li awwalina wa akhirina wa aayatan minka…, – ma’ana zamu riketa ranar wani taro babba (idi babba)’, Annabi Isah ya gaya ma Ubangiji, sai Allah SWT yace “to zan saukar da shi, kuma na yadda su riki wannan rana ranar idi, amma duk wanda ya yi butulci bayan haka zan azabtar da shi azabar da ban yi ma wani irinta ba”.

To in dai saukar abinci ta kai matsayin a rika tunawa da ita, kuma Alkur’aninmu ne ya fada, har ma akwai sura mai sunan saukar abincin, “Suratul Ma’idah” to ina ga tunawa da Annabawan Allah baki daya? Ina ga tunawa da shugabansu kuma cikamakon Annabawa gaba daya, wanda yazo da wayewa da kwarewa, wanda duk abinda aka ga bai cika ba to ba daga shi ba ne SAW, daga mune wanda muka dauko abin, amma ba daga shi tawaya tazo ba.

ADVERTISEMENT

An haifi Annabi SAW kamar yadda yazo, 12 ga watan Rabi’ul Auwal (mafi rinjayen riwaya), shekarar Giwa, ya yi shekara 40 sannan Allah ya aiko shi, ya yi shekara 13 a Makkah, sannan ya yi hijira, kaga yanzu idan ka dora wadannan shekaru 13 akan 40 zaka ga ya zama 53 kenan, to mun fara tarihi da kalandar mu ta hijira, yau hijira tana 1447, idan ka hada 53 da 1447 ya zama 1,500 kenan daidai.

A bana Mauludin Manzon Allah SAW yana da wani girma na daban, na cewa Manzo SAW ya cika shekara 1500 kenan da haihuwa. Ya dace duk Musulmi, kai kowane dan Adam ma, tunda Manzo SAW ba namu ne mu kadai ba, da fadin Ubangiji, “wama arsalnaka illa rahmatan lil’alamin – ba mu aikoka ba, face ka zama rahama ga duk halitta”, karatu ne mai girma mai tsawo mai fadi. Ubangiji ya yi gaskiya.

LABARAI MASU NASABA

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)

Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani

Manzon Allah SAW abun kowa ya yi murna da shi ne, mun gode Allah, duk wanda yake da shekara 30 yaga yadda duniya ta yi murnar cikar Annabi Isah shekara 2000 da haihuwa, an yi bukukuwa, kuma ba wai Kiristoci kadai ne a lokacin suka yi bikin ba, domin Annabi Isah ba nasu ne su kadai ba. To ya dace duk Musulmi, mu yi kokari mu ke yin murnar na mu, zancen cewa yana da kyau ko bashi da kyau wannan dakikanci ne, an wuce wannan lokacin. Babban littafin mu da muke dogaro da shi, Alkur’ani, shi ne wanda Allah ya hado Manzo SAW da shi. Duk muhimmin abu idan ka saya (kamar rediyo, talabijin, wayar salula, da sauransu) sai kaga littafin da zai koya maka yadda ake amfani da wannan abun da ka siya (manual) a ciki, in kaki bin wannan littafi, ka bi son ranka, duk abin da ya faru babu ruwan kamfani. To muma ga littafin da Allah ya hado Annabinmu da shi, wanda duk ka’idojin addininmu suna ciki.

Allah ya yi mana Mauludin Annabawa wajen guda biyar a ciki. Allah SWT ya yi mana Mauludin farkon dan Adam ma, kuma ya ce mu yi yawo a kan kasa don muga yadda ya fara halitta, wannan ita ce ayar da ta nuna mana mu yi ilimin binciken kasa sanin tsarinta (Archeology da Geology), don muga yadda Allah ya fara halittar dan Adam, da mazauninsa, da duk sana’arsa, da wayewarsa, ma’ana al’adunsa (culture), da cigabansa, da gine-ginensa. Sannan Allah ya yi mana maganar halittar Adamu, haka zalika kuma Allah yayi mana maganar farkon ciki da aka fara yi a doron kasa “HUWAL LAZI KHALAKAKUM MIN NAFSIN WAAHIDA, WA JA’ALA MINHA ZAUJAHA LI YASKUNA ILAIHA. FALAMMA TAGASSHA HAMALAT HAMLAN KAFIFA…” , sannan Allah ya yi mana maganar haihuwar Annabi Musa da abubuwan da suka faru tsakaninsa da Fir’auna, ya yi mana maganar haihuwar Sayyida Maryam da sanya mata suna, ya yi mana maganar haihuwar Annabi Yahya, da Annabi Zakariyya, ya bamu labarin ya yi, shi Yahya din nan Allah yayi masa ni’ima yace aminci ya tabbata a gare shi ranar da aka haifeshi da ranar da zai mutu, da ranar da za’a tasheshi ranar tashin kiyama.

Har ila yau, Allah ya yi mana magana a fadade ta zancen haihuwar Annabi Isa (AS) da duk abinda ya faru. Annabi Isah shi ma ranar da aka haifeshi (ranar haihuwa fa ba wasa bace, rana ce mai hadari domin dan zai iya mutuwa a ranar, Sannan kuma rana ce ta murna), Allah ya ce, “aminci ya tabbata a gare shi (Annabi Isa) ranar da aka haifeshi, da ranar mutuwarsa, da kuma ranar da za’a tashe shi (Ranar mutuwa ma rana ce mai girma, domin rana ce ta bakin cikin an rabu da mamaci, amma shi kuma rana ce ta farin ciki a wajensa saboda rana ce da ya sadu da Allah).

Allah (SWT) ya fada mana Annabi Ibrahim (AS) ya roki Allah yazo da Annabi Muhammad (SAW), a lokacin da ya gina Makkah yayi roko Allah ya ba mutanen Makkah da duniya ma gaba daya Annabi Muhammadu. Kuma Allah ya tabbatar da hakan a cikin Al’kurani mai girma. Sannan Allah yayi mana maganar haihuwar wanda ba Annabi ba ma, Sayyidina Ali Allah ya girmama fuskarsa ba Annabi bane, amma kuma Allah ya bamu labarin haihuwarsa a cikin Al’kurani “HUWAL LAZII KHALAKA MINAL MAA’I BASHARAN, FA JA’ALAHUU NASABAN WA SIHRA, WA KAANA RABBUKA KADIIRA” duk tafsirin duniya sunce maganar sayyiduna Ali ce. Sannan duk aron da muke yi ranar juma’a, da duk wannan Sallar juma’a da ake yi, saboda an halicci Adamu ne a cikinta.

Sannan kuma Allah yace yana fada ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama labarin Annabawa domin ya nutsar da zuciyarsa; ka dubi duk irin kyakkyawar zuciyar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama amma ana bashi labarin Annabawa domin wannan zuciya tasa ta nutsu. Ka duba rukunnan hajji da muke yi idan munje, Safa da marwa, kifar shedan, da duk sauransu kai kace wasan kwaikwayo ne muke yi na yadda labarin Hajarah da Annabi Isma’il ya faru, amma kuma ibada ce muke yi, kaga kuwa tarihinsu ne. Ashe ba wasa bane kenan!

Ina kira ga al’ummar Musulmi mu guji yin maganganu wadanda basu da tushe, shi dai mauludi ana yine domin girmama Annabi Muhammad SAW, to tunda haka ne, akwai Shehi babba, wanda a kasara Makkah yake, Shehu Alawiy Malikiy, ya fada cewa “ace sai ranar Sha biyu ga Rabi’ul Awwal za’a yi Mauludi to in akwai bidi’a a ciki ma shi a wajensa wannan ne bidi’ar” akwai manyan waliyyai wadanda suma sun dauki duk ranar Litinin a matsayin ranar da suka kebanta da azumi da yabon Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da niyyar Mauludi. Mu ma Alhamdu Lillahi duk ranar Litinin muna karanta suratun Najmi saboda abubuwan kebanta na Manzon Allah da aka ambata a cikinta, mu ma muna karanta ta da niyyar Mauludi. Amma fa duk da haka ita ranar haihuwar tasa tana da wani kebantaccen bambanci na musamman akan sauran ranaku.

Tarihi
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Ganin Girma Da Kwarjinin Annabi (SAW)

MASU ALAKA

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)
Dausayin Musulunci

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)

September 4, 2026
Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani
Dausayin Musulunci

Maulidin Bana:Babu Wanda Ya Fi Cancanta Da Soyayya Saboda Gwarzontaka Kamar Annabi (SAW) —Mai Diwani

August 28, 2026
Tarihi
Dausayin Musulunci

Hikimomin Kalaman Manzon Allah (SAW)

August 21, 2026
Next Post
Shirin APC Na Fidda ‘Yan Takara Ta Hanyar Sulhu Ya Gamu Da Cikas A  Jihar Adamawa

Shirin APC Na Fidda ‘Yan Takara Ta Hanyar Sulhu Ya Gamu Da Cikas A Jihar Adamawa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.