ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

by Sulaiman
4 hours ago
ubangiji

Istigfari ɗaya ta zubar da zunubinka, ina kuma wannan mai yawa. Aya tana cewa, “alif lam mim, kitabun uhkimat aya’atuhu summa fussilat min ladun hakimul kabir, allata’budu illallahu innani lakum min nazirun wa bashir, wa an istagfiru rabbakum summa tubu ilaihi”. Ku yi istigifari ku tuba zuwa ga Allah, za ku yafe muku. Ku yi istigifari ku tuba zuwa ga Allah. Sannan Allah yake cewa, “waman ya’amal su’an aw yazlim nafsuhu summa yastagfirullaha, yajidillaha gafuran rahima”. Duk wanda ya aikata mummuna ko ya zalunci kansa sannan ya nemi gafaran ubangiji zai samu Allah mai yawan gafara, zai samu Allah mai yawan jinkai.

Duk wanda ya yi zunubi, ko mai girmansa, istigifari tana share shi. Amma komai ƙanƙantar zunubi, in ba istigifari, babbane in ba a tuba ba.

Idan ka yi istigifari talatin (30) a wazifa, ɗari (100) da safe, ɗari (100) da yamma sai ka buga shi sau bakwai (7), zai baka istigifari dubu da ɗari shida da goma (1,610), a haɗa da guda uku (3) a zikirin juma’a, za a samu istigifari (1,613). Wannan aƙalla istigifarin batijjane kenan na sati.

ADVERTISEMENT

Wani ya ce, me ya sa Shehu Tijjani ya hana bai wa mai shantaba ɗariƙa, amma kuma bai hana miƙata ga masu aikata manya-manyan laifuffuka ba?

Shehu ya amsa masa da cewa, duk mai yin manyan laifi ya san laifi yake aikatawa, zuciyar sa zata karye, zai yi istigifari, sannan ya ƙanƙan da kai ga Allah, amma mai shan taba bai san ma laifi yake yi ba. Wata ƙila ma in an yi masa magana, ya nemi kare kansa da ayar Ƙur’ani. Wani ma zai ce, “kullu ma tunbitul ardu, halalukum – dukkan abin da ƙasa ta baku, halal ne agareku”.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

To anan ne, shehu Tijjani ya ce, “to ina jin tsoron waɗanda suka ce laifi ne shantaba, kar suna da gaskiya, ya zama mabiyina ya tafi wurin Allah bai tuba ga wani zunubi ba.

Abun da Shehu Tijjani RA ya faɗa kenan. Ma’ana, komai girman zunubi indai akwai istigifari, za ta wanke shi, amma komai ƙanƙantarsa in ba istigifari, yana da girma.

Sannan Allah tabaraka wa ta’ala yana faɗa, “walau annahum izzalamu anfusahum ja’uka fastagfarullaha wastagfara lahumur rasula, la wajadullaha tawwabar rahima”. Da dai idan mutane muka zalunci kanmu sannan muka zo wa manzon Allah SAW, idan yana nan. Idan baya nan mu zo wa kabarin sa. Idan bama kusa da inda kabarin yake, mu yi tawassuli dashi duk inda muke yana tare da mu. Idan muka yi tawassuli dashi muka nemi gafarar Allah Tabarak wa ta’ala, yanzu yanzu ne zai gafarta mana.

Falalar Allah tana dayawa. Allah tabaraka wa ta’ala yake fada a wata aya, “inna anzalna ilaikal kitab bil hakki litahkuma bainan nasi bima arakallahu wala takul lilkha’inina kasima. wastagfirullah”. Ka nemi gafarar ubangijinka.

Muyi tayin istigifari, muyi tayin istigifari. Mun gode Allah da Allah ya sa mu a cikin hanyar Istigifari. Wani zai ce ai ko ban karɓi Ɗariƙa ba, zan iya istigifari, gaskiya ne. Yanzu ma zaka iya yin dubu ka fimu amma kafin ka sake zama ka ƙara yi, shine rikicin.

Amma mu ba za muyi irin naka ba ma mu ce zamu zauna yanzu muyi dubu. Ƴan kaɗan-kaɗan ɗin mu, kafin sati sai kaga mun tara da yawa. Mun gode Allah.

To, mu riƙe ƙwarai da gaske. Sannan aya ta zo, “izaja’a nasrullahi wal fathi waraitannasa yadkuluna fi dinillahi afwaja fasabbih bihamdi rabbika wastagfirhu innahu kana tawwaba”. Wannan aya tana da munasaba ƙwarai da gaske. Da yawa jahili zai zaci hujja ya kawo, da faɗinsa, “ta yaya wani zai zo ya ce a dinga istigifari bayan Allah ya ce ‘alyawma akmaltu lakum dinakum'”? Da ya sani, da ya fahimci cewa, ai ita surar “Iza ja’a” ma bata sauka ba sai bayan ranar da Allah ya ce “alyawma akmaltu lakum dinakum”.

Yau Allah ya ce “alyawma akmaltu lakum dinakum” a lokacin aikin hajji, ranar jifa a mina, rana. Ka shegari kuma ayar “izaja’a nasrullahi wal fathi, wa ra aitannasa yadkuluna fi dinillahi afwaja, fasabbih bihamdi rabbika wastagfirhu, innahu kana tawwaba,” ta sauka. Ga horon istigifari ga horon tasbihi.

Amma horon sallah, da azumin Ramadana, da zakka, da hajji, wannan an rufe. Amma abubuwan istigifari, abubuwan takawa babu wanda ya rufe su? Ai karshen aya da ta sauka a Ƙur’ani “wattaƙu yawman turja’una fihi ilallahi summa tuwaffa kullu nafsin ma kasabat wahum la yuzlamun”. Ita ce karshen sauka.

Ƙila ta sauka da awa biyu, Annabi SAW ya koma zuwa ga Allah. Ko kuma da kwana biyu. Amma babu wanda ya ce da sati biyu ma ta sauka kafin wafatin Annabi SAW.

Duba da ayar da ubangiji ke cewa, “wa atmamtu alaikum ni’imati, Wa radiitu lakumul islami dinan”, ma’ana har ni’ima ma Allah yace ya cika. To sai a daina hawa su motoci, jiragen sama da duk abubuwan da zamani ya zo mana da su kenan? Sabida an riga an cika ni’imomi, A’a, ba haka ake nufi ba.

Istigifari yazo a cikin hadisi, Manzon Allah SAW yace “inni la astagfirullaha fil yaumi sab’ina marratan”. Ni kaina da yawa nakan nemi gafarar Ubangiji a cikin rana sau 70. A duk rana, Annabi yake istigifari 70. A cikin wata ruwaya kuma, 100. To ai ko dai Annabi SAW, ɗaya yake yi, ai ya isje mu hujja? Shi da “liyagfiralakallahu ma taƙaddama min zanbika wa ma ta’akhara – an gafarta masa zunubansa duka, da wanda ya yi, da wanda zai yi a nan gaba”, amma yanayin istigifari 100 a kullum. To don mu munyi miliyan ma, ai kadan muka yi. To bare shi kansa ya kan yi 70 din. Shi kansa ya kan yi 100, meye laifin wanda yace to mu ɗauki 100 ɗin?

Sannan hadisi yazo, Manzon Allah SAW yace “innahu layuganu ala ƙalbi – akan ɗan yi rufi a zuciya ta”. Shehunnan mu sun ce wannan rufin haske ne, ba rufi ne na duhu irin namu ba. Mu ne da yawa zuciyan mu ta kan yi duhu, ta yi rufi. Sai mun yi istigifari ne za’a goge ta.

Abunda ake nufi da rufi a zuciya, shi ne jin baƙin ciki a zuciya yayin da aikata wani abu na saɓo, sai kaji wata damuwa da zata rufe zuciya, amma shi Manzon Allah SAW, shehunnan mu sun ce wannan rufi ne na kara haske ne SAW. Duk lokacin da ya kara wata hauhawar daraja, sai ya ga kamar zaman da yayi a muƙamin baya, kamar wani zunubi ne ya yi. In ya kara hawa ma sai ya ga haka, SAW.

To, waɗansu malamai suka ce menene ma’anar “gayyu” wannan rufi? Suka ce ma’anarsa, idan mutum ya yi zunubi, za’a ɗiga baƙin ɗugo a cikin zuciyarsa. In za a rubuta masa zunubi, sai ɗayan Mala’ikan ya ce, ” tsaya tukunna, wata ƙila zai nemi gafara. To in baka nemi gafara ba har lokuta da yawa suka shige, shikenan sai yace “to ya za’ayi?” Rubuta, amma rubuta ɗaya. To shikenan sai ya ɗiga ma baƙin ɗugo a cikin zuciyar. Amma in mutumin nan ya tuna cewa, ya yi zunubi wata rana, sai ya nemi gafara, shi kenan sai Mala’ikan nan ya goge abin da ya ɗiga, amma duk yadda za a goge ba zai koma kamar yadda yake a baya ba. Misali, idan aka ɗiga baƙin tawada akan farin kaya, in an sanya sabulu an wanke, zai fita amma ba zai koma kamar yadda yake a baya ba, zai iya barin gurbi. To wannan zunubi ya wanke. Amma gurbinsa zai iya zama yana nan.

To haka, ana ɗigawa ana wankewa, gurbi yana nan har sai zuciya ta zama baƙin ƙirin da wannan gurbi, ba zunubi bane amma gurbinsa ne. To shi kuma wanke wannan gurbi, sai an yi amfani da sanpefa.

Komai yana da irin na shi sanpefar da ake goge shi, har tsatsar zuciya, amma sanpefar zuciya, itace ambaton Allah, “wa saƙalatul ƙalbi zikirullahi”. To, ƙila wannan shi ne “gayyu”.

Malamai sun ta yin magana akan wannan gayyu. Amma Manzon Allah SAW, Allah ya kiyaye shi da irin wannan, wannan irin gairun sauran bayi ne. Shi kuma Manzon Allah na sa na haske ne SAW. To, Manzon Allah yace ana rufi a zuciyata. “Fa astagfirullaha fil yaumi sab’ina marratan, Har sai na yi istigifari a rana sau 70. Sannan inji wannan rufi ya yaye. Muslim ne ya fitar da wannan hadisi.

Wani hadisi yazo cewa Manzon Allah yana yin 100. Abu Dauda ya fitar da shi. Imamul Bukhari ya fitar da hadisi daga Abu Huraira radiyallahu anhu. Manzon Allah SAW yace “wallahi na rantse da Allah inni la astagfirullaha, ni ina neman gafaran Allah “wa atubu ilai” ina tuba zuwa gare shi “aksara min sab’ina” yafi 70 ma. Ni kullum sai na yi istigifari yafi 70. yanzu don wani bawan Allah yazo yace mun wannan, “wani hadisin yace 70. Wani hadisin yace 100. Wani hadisin yace yafi 70. To ku rike 100”. Menene laifin sa? Menene laifin sa a ciki? To shi yasa mu ka rike 100, koyi da Manzon Allah SAW. To ko ba komai cikin istigifari, wannan ya ishe mu.

ubangiji
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Ƙa’idojin Gudanar Da Biyan Kuɗi Nan Take Domin Kare Kai Daga Zamba
  • Sulaiman
    Gwamna Lawal Ya Yi Alƙawarin Bayar Da Ƙarin Tallafi Ga Jami’an Tsaro A Zamfara
  • Sulaiman
    Salon Jagorancin Kasar Sin Na Ingiza Samar Da Ci Gaba Mai Nagarta
  • Sulaiman
    Dangote Ya Rage Farashin Fetur Zuwa N1,125 Kan Kowace Lita

MASU ALAKA

Manzon Allah
Dausayin Musulunci

Falalar Haɗa Basmala da Suratul Fatiha

June 19, 2026
Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan
Dausayin Musulunci

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

June 12, 2026
Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

June 5, 2026
Next Post
Noma

Ƙa'idojin Gudanar Da Biyan Kuɗi Nan Take Domin Kare Kai Daga Zamba

LABARAI MASU NASABA

Sowore Ya Sha Alwashin Ci Gaba Da Gwagwarmaya Duk Da Tsare Shi A Gidan Yarin Kuje

Jagoran Matasan AAC Kwamret Yahaya Soje Ya Nemi A Saki Sowore

June 26, 2026
Har Yanzu Ba Mu Karɓi Kuɗaɗen Da Aka Ware Mana Na Zaɓukan 2027 Ba – INEC

Har Yanzu Ba Mu Karɓi Kuɗaɗen Da Aka Ware Mana Na Zaɓukan 2027 Ba – INEC

June 26, 2026
Husaini Isa Ya Gargaɗi Ƴan Takarar NDC A Kano Kan Buƙatar Kiyaye Ƙa’dojin Jam’iyya

Husaini Isa Ya Gargaɗi Ƴan Takarar NDC A Kano Kan Buƙatar Kiyaye Ƙa’dojin Jam’iyya

June 26, 2026
Noma

Ƙa’idojin Gudanar Da Biyan Kuɗi Nan Take Domin Kare Kai Daga Zamba

June 26, 2026
Darussan Da Suka Fi Dacewa A Fahimta Daga Alkur’ani A Wannan Zamanin (2)

Falalar Yawaita Tuba Ga Ubangiji (Istigfari)

June 26, 2026
Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ɗaliba A Wata Sakandiren Kano

Gwamna Yusuf Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ɗaliba A Wata Sakandiren Kano

June 26, 2026
Birtaniya Da Nijeriya Sun Ƙulla Yarjejeniya Kan Yaƙi Da Ta’addanci

Birtaniya Da Nijeriya Sun Ƙulla Yarjejeniya Kan Yaƙi Da Ta’addanci

June 26, 2026
Rashin Tsaro: Ana Ƙoƙarin Ganin Ƙarshen Haƙurin Arewa – ACF

ACF Ta Ƙaddamar Da Gidauniyar Tallafa Wa Ilimi A Arewa

June 26, 2026
Damunar Bana: Yadda Gwamnati Da Manoma Ke Tunkarar Barazanar Ƴan Ta’adda

Damunar Bana: Yadda Gwamnati Da Manoma Ke Tunkarar Barazanar Ƴan Ta’adda

June 26, 2026
Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

Sin Da Amurka Sun Amince Da Kafa Majalisar Kasuwanci

June 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.