ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, June 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
22 seconds ago
Tsari

Alhamdullilahi, wannan shafin namu mai albarka wanda ya saba zakulo mana abubuwa da za su amfane mu duniyarmu da lahirarmu, yau ya zo mana da falalar neman tsari daga duk wani sharri na sharri na duniya da wanda ke yi mana barazana ga ibadunmu da muke fatan haduwa da ubangijinmu lafiya.

Shehu Tijjani yake cewa, mu tabi’in mu Muhammadi ne. Mu darikarmu Annabi Muhammad SAW ya kulla ta, ya dan kata a hannun Shehu Tijjani. Shehu Tijjani ya ce, “hatta ni suna na dan darikar”. Darikar ta Manzon Allah SAW ce.

Shehu Tijjani ya ce, “to, ba wani hatimi da zai iya hawa kan hatiminmu”. Za ka iya barin Darikar sauran bayin Allah, in kazo wurin Shehu Tijjani zai dauke ka, amma babu wanda zai dauke ka in kabar tas. To dan haka, in ta wani zaka je ka je, ta wani ita ma ta Allah ce. Zaka sadar da kai da duk abin da ake so, amma, “bil hisabi wal ikabi”. Amma shehu Tijjani in ka bi sa, zaka sadu da dukkan muradi, “bil hisabi wala ikabi”. In kana so, zo ka shiga, amma dole ka bi sharadi.

ADVERTISEMENT

Yana daga cikin sharadin Darikar Shehu Tijjani: ba ziyarar wani waliyyi mai rai ko matacce, sai dan cikin Darikar – ziyarar ka je neman wani abu wajan sa, ya sada ka da Allah, ko albarkarsa. Ma’ana, kamar ka raina abubuwan da Allah ya baka a darikar Shehu Tijjani.

Idan mutum ya karba da wannan sharadi, shike nan ya zama dan Darikar Shehu Tijjani. Duk abinda Manzon Allah ya lamunce wa Shehu Tijjani, shi ma zai samu. Duk wani alheri da yake samun mutane cikin ta zai samu. Mun gode Allah, Allah ya cika mana wadannan sharuda. Allah ya tabbatar da mu a kan darikar Tijjaniyya.

LABARAI MASU NASABA

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

Ayyukan ‘yan Darikar Tijjaniya sune kamar haka: istighfari, wuridin safe, wuridin yamma, wazifa, da zikirin juma’a.

Me ake karanta a wuridan nan? A duk wurdan nan da ake karantawa idan an zauna, farkon abinda za a fara, neman tsari da iblis da fadin cewa, “a’u’dhubillahi minashaitanirrajim”. Wannan saboda za a karanta fatiha, fatiha kur’ani ce gabaki daya. Allah ya shar’anta duk wanda zai karanta kur’ani ya ce, “a’u’dhubillahi minashaitanirrajim”.

Shiga fadar Allah sai da tsarki, Dan wai yanzu ka san fada, shi yasa za a kurkure baki daga duk zunubi da fadin, “a’u’dhubillahi minashaitanirrajim”. Allah tabaraka wa ta’ala ya yi horo da ita, Allah tabaraka wa ta’ala yake cewa, “Fa’ iza kara’atal kur’ana fasta’iz billahi minashaitanirrajim.” In dai zaka karanta kur’anin nan to ka nemi tsari daga Allah ya tsare ka sharrin shedan.

Sannan wata aya take cewa, “Wa imma yanzagannaka minashaitani nazghun fasta’id billah.” In kaji wani mai waswasin banza na daga shetani, ya fara yi maka waswasin nan, maza-maza ka ce “a’u’zubillahi minashaitanirrajim”.

Toh, wannan kenan. Sannan ya zo a cikin hadisi cewa, hanyoyin neman tsari da shedan suna da yawa. Abdullahi bin Mas’ud, Manzon Allah ya koya masa. Da ya zo gaban Manzon Allah SAW sai ya ce “Audhubillahi sami’ul alim minashaitanirrajim.” Sai Manzon Allah ya ce ba haka na koya ma ba. Ce ma nayi “Audhubillahi minashaitanirrajim.”

(Haka za’a allamani Jibril – ni ma haka Jibril ya sanar da ni) shi kuma daga allo (lauhil mahfuzi) ya dauko ta, shi kuwa lau’il mahfuz alkalami ya rubuta masa haka, shi kuma daga rabbil izzati.

“Audhubillahi minashaitanirrajim.” Dan haka, ta zama daga cikin abinda ‘yan Darikar Shehu Tijjani ke karantawa. Duk in an zauna, ko wuridin safe, ko wuridin yamma, ko wazifa, ko zikirin Juma’a, sai an ce, “a’u’dhubillahi minashaitanirrajim”.

Toh, kuma Allah yana gaya mana, “Innashaitana lakum aduwwun fattakhizu hu aduwwa – Shedan makiyin ku ne, to ku rike shi, makiyi”. An ce mu rike shi makiyi don mu tsaro daga sharrinsa, amma ta yaya? Duk abinda ka san, yana yi maka horo da shi, ka san na banza ne ka bari. Toh, wannan yana daga cikin rukon makiyi. Shi Iblis, wani irin makiyi ne da ya fi karfin mu. Makiyi ne da ya girmi iyayen mu gabaki daya na daga Annabawa, don kowa-da-kowa ma zuwa yayi, ya tarar da shi.

Makiyi ne da shi yana ganin ka, kai ba ka ganin sa, ta yaya za ka iya fada da wannan makiyi. Makiyi ne kuma malamini ne a kan ka. An ce ba wata shari’a ta Allah sai da Iblis ya haddace ta don kar ya yi horo da ita. Duk abinda zai horo da shi, ba alheri bane, saboda ya haddace alheri duka. Don kada a ce bai sani ba, ya zo ya yi horo da wani sharri, ashe kuma alheri ne, don haka ya haddace alherai duka.

In yanzu wannan makiyi, da ya fi karfin ka, kuma malamini ne, yana ganin ka, kai ba ka ganin sa. Wannan makiyi, ya za’a yi da shi? Za ka yi fada da shi ne? Sai masana suka ce “Toh, wannan makiyi ka zama kamar in ka zo gida, akwai kare, kana zuwa za ka yi sallama, karan nan sai ya taso maka da fada, ya ya zaka yi? Za ka tsaya fada da shi ne ko kuwa za ka kirawo mai gidansa ne?” Ka kira mai gida.

Wai saboda gigicewar dan’Adam da sannin girman mugun makiyin nan Iblis, dan’Adam ma sai ya ga in ya kira Rahmanu, kamar bai isa ba, in ya kira Rahimu, kamar bai isa ba, in ya kira Maliku, kamar bai isa ba, kuma duk sunnan Allah ne, duk suna da karfi, sai ya kira matattara sunnan gaba daya, ya ce, “A’uzu billahi minash-shaitanir-rajeem.” Bai ce, “A’uzu bil-maliki” ba, ko a’uzu bir-rahmani.

Saboda yanzu idan ka tambayi mutum, “Waye al-maliku?” Zai ce ma, “Allahu.” “Waye ar-rahmanu?” Zai ce ma, “Allahu.” “Waye al-latifu?” Zai ce ma, “Allahu.” In ka ce, “Waye allahu fa?” Zai gigice. Eh, dama kila sunnan ma mushtaki ne na gigice wa din, don haka, da an ambaci sunan, sai a gigice. To wai saboda girman sharrin nan na shetan, dan’Adam sai ya ga ma kamar duk wani suna da ya kirawo ma bai isa ba. Sai ya kira matattara sunan ma gabaki daya. Ya ce, “A’uzu billahi minash-shaitanir-rajeem.” Haka Jibril ya sanar da Manzon Allah SAW daga Lauhil Mahfuuzi, daga kuma Al-Kalami, daga Rabbal-izzah. To duk wannan sai an fade safa da yamma, da wazifa, da zikirin Juma’a. Banda sauran kuma ibadun sa da yake.

To, “A’uzu billahi minash-shaitanir-rajeem” ma’ana, ka roki Allah ya kiyaye ka daga shaitan da sharrin sa. Kuma wannan kalma alhairanta da yawa sun tattara a karkashin ta.

An ce sharrirruka guda uku ne: Akwai sharrin da ya rataye da addinin mutum, wannan sharrin su ne kamar kafirci, kaman hawa bidio’i da addini bai yarda da su ba, kaman fasikanci, aikata manya manyan laifuka, da sauransu. Wadannan in suka taru sai su zama babba. Ana cewa, sarkin yawa ya fi sarkin karfi.

Wadannan su ne sharrikan da suka rataya da addinin mutum.

Sai sharrin da ya rataya da jikin dan’Adam. Na daga masifa da ta rataye da jikin sa, kamar rashin lafiya ko tsamin jiki ko rauni da ya samo sanadiyyar fada, Allah ya kiyaye, har ya zama jikin ya nakasa ba zai iya yin komai ba, ko kuma kwarauniya ta tsufa, Ko kasala – kana da lafiyan, kana da komai, amma ba zai iya tashi ya yi wani abu na kirki ba. Duk sharri ne da ya rataye da jikin dan’Adam. Kasala kenan. Ko kuwa kana da karfin, kana da komai, amma ga ragwontaka, Allah ya zuba ma a cikin zuciya. Shi kenan duk ba zaka iya komai din nan ba. To wannan ma sharri ne da ya rataye da jikin danAdam.

Sharri na uku kuma, shi ne abin da Allah ya bai wa danAdam ta rataye da dukiya. Kamar dukiya, danAdam bai san a taba masa. Kaman rashin lafiyan ‘ya’ya. Dole sai ka kai su asibiti, ka fitar da kudin ka. Ko mutuwar ‘ya’ya, ko kuwa rashin kudin ma, wannan duk sharri ne da ya rataye da dukiya.

To wai duk in ka ce, “A’uzu billahi minash-shaitanir-rajeem,” Allah ya isar ma wannan. In ka iya ka halarto su gabaki daya. In ma ba zaka iya ba, ka kudure kai dai duk wani sharri ma na shedan ma da duk abin da ya rataye da shedan din ka nemi tsari da Allah da shi. Kuma Allah tabaraka wa ta’ala zai tsare ka a cikin wannan.

Tsari
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Buƙatar Komawa Ga Allah Ta Hanyar Yawaita Istigfari
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Bukatar Kula Da Tarihi A Musulunci

MASU ALAKA

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Bukatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

June 5, 2026
Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
Dausayin Musulunci

Buƙatar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

May 29, 2026
Buƙatar Komawa Ga Allah Ta Hanyar Yawaita Istigfari
Dausayin Musulunci

Buƙatar Komawa Ga Allah Ta Hanyar Yawaita Istigfari

May 22, 2026

Discussion about this post

LABARAI MASU NASABA

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

Falalar Neman Tsari Daga Sharrin Shaidan

June 12, 2026
Gwamnatin Tarayya Za Ta Dauki Sabbin Ƴansanda 50,000 Da Karin Sojoji — Tinubu

Gwamnatin Tarayya Za Ta Dauki Sabbin Ƴansanda 50,000 Da Karin Sojoji — Tinubu

June 12, 2026
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 51, 876 Sun Mika Wuya A Arewa Maso Gabas

Tinubu Ya Jinjina Wa Jami’an Tsaro Kan Jajircewarsu Wajen Kawo Karshen Ta’addanci

June 12, 2026
Tsari

June 12, 2026
Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

Yayin Da Dangote Ya Bayyana A Ganawar Neman Aiki

June 12, 2026
A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

A Karshe Jamilu Gwamna Ya Samu Babbar Damar Yin Takara

June 12, 2026
Takaitaccen Jawabin Shugaban Ƙasa Tinubu Na Ranar Dimokuraɗiyya

Takaitaccen Jawabin Shugaban Ƙasa Tinubu Na Ranar Dimokuraɗiyya

June 12, 2026
Dimokuradiyyar Nijeriya A Shekara 27:Ba Yabo Ba Fallasa

Dimokuradiyyar Nijeriya A Shekara 27:Ba Yabo Ba Fallasa

June 12, 2026
Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya

Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya

June 12, 2026
Sin Ta Fitar Da “Shirin Aiki Na Kasa Kan Hakkin Dan Adam Na (2026-2030)”  

Sin Ta Fitar Da “Shirin Aiki Na Kasa Kan Hakkin Dan Adam Na (2026-2030)”  

June 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.