ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, September 13, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

CAN Ta Buƙaci A Sanya Dokar Ta-ɓaci Kan Tsaro, Ta Ayyana Zaman Makoki Na Kwana 3

by Sadiq
3 months ago

Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN), ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ayyana dokar ta-ɓaci kan harkokin tsaro sakamakon karuwar kashe-kashe, sace-sacen mutane da hare-haren ta’addanci da ke ci gaba da faruwa a sassan ƙasar.

An bayyana wannan buƙata ne a wani taron shugabannin majami’u da aka gudanar a Abuja, inda mahalarta taron suka nuna damuwa kan taɓarɓarewar tsaro da kuma yawaitar mutanen da aka tilasta wa barin gidajensu saboda rikice-rikice.

CAN ta ambaci hare-haren da suka faru a jihohin Oyo, Ogun, Borno, Benuwe da Kogi, tare da nuna damuwa kan sace ɗalibai da malamai, hare-haren da ake kai wa manoma da kuma yaɗuwar laifuffuka zuwa wuraren da a baya ake ganin suna da zaune lafiya.

ADVERTISEMENT

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnati ta ƙara ƙarfafa matakan tsaro, inganta tattara bayanan sirri da kuma hanzarta kafa ‘yansandan jihohi.

Haka kuma ta nemi a sako duk waɗanda aka sace ba tare da wani sharaɗi ba, tare da buƙatar jami’an tsaro su ƙara ƙaimi wajen ceto su.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

A cikin shawarwarin da ta fitar, CAN ta ayyana kwanaki uku na zaman makokin ƙasa daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Yunin 2026.

Ta kuma ware ranar 14 ga watan Yuni a matsayin “Ɓaƙar Rana” domin tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren tashin hankali da kuma nuna goyon baya ga iyalan da abin ya shafa.

Wannan kira na CAN ya zo ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan yawaitar sace ɗalibai a Nijeriya, musamman bayan hare-haren da suka faru a jihohin Oyo da Borno inda aka sace ɗalibai da malamai da dama.

MASU ALAKA

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola
Manyan Labarai

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa
Manyan Labarai

Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

September 13, 2026
Next Post
‘Yan Majalisar Wakilai 6 Daga Oyo Sun Fice Daga PDP Zuwa APM

'Yan Majalisar Wakilai 6 Daga Oyo Sun Fice Daga PDP Zuwa APM

LABARAI MASU NASABA

Yajin Aikin ASUU: Malaman Jami’ar Jihar Kaduna Sun Bijirewa El-rufa’i

Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan KASU

September 13, 2026
Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

Gwamna Fintiri, Dangote Da Sarakunan Gargajiya Sun Halarci Jana’izar Bamanga Tukur A Yola

September 13, 2026
Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

Xi Ya Gabatar Da Shawarwari Kan Hadin Gwiwar “Gawurtacciyar Kungiyar BRICS”

September 13, 2026
Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

Tsohon Kwamishina A Gombe, Ya Marawa Pantami Baya

September 13, 2026
Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba

Doma United Na Cigaba Da Jan Zarenta A Firimiyar Nijeriya Bayan Doke Enyimba

September 13, 2026
Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari

Hafsat Bakari Ta Sake Dawo Da Sarƙaƙƙen Al’amari

September 13, 2026
Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

Zan Yi Amfani Da Dukiyata Wajen Samun Nasarar Gwamnan Jihar Kano A 2027 – Amb Adesuwa

September 13, 2026
Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

Xi Ya Halarci Taron BRICS A New Delhi

September 12, 2026
Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

Ya Kamata A Rike Damar Kasar Sin Samfurin 2.0 A Taron CIFIT

September 12, 2026
jam'iyyu

An Buƙaci Ƴan Takara Su Sanya Tsare-tsaren Yaƙi Da Ɗumamar Yanayi A Jaddawalin Kamfen Ɗinsu

September 12, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.