ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana

by Abubakar Abba
2 months ago
Gwamnatin

Masu Masana’antun Kiwon Kajin Gidan Gona a ƙasar nan, sun soki haɗakar gwamnatin ƙasar da ƙasar Chana, ta kimanin dala miliyan 900.

Sun yi gargaɗin cewa, wannan haɗaka, za ta iya durƙusar da fannin kiwon kaji a ƙasar, matuƙar ba a wanzar da ita yadda ya kamata ba.

Sun yi sukar ce, a jihar Legas, a hirarsu daban-daban a ƙarƙashin ƙungiyarsu ta masu kiwon ta ƙasa (PAN).

ADVERTISEMENT

Sukar tasu na zuwa ne, bayan samun rahoton cewa; gwamnatin ƙasar, na kan ƙoƙarin yin haɗaka da ƙasar Chana ta dala miliyan 900, domin yin aikin kiwon kajin gidan gona a ƙasar nan, wanda hakan zai bayar da damar samar da ƙwan kaji miliyan shida a kowace rana.

Gwamnatin na shirin yin hakan ne, domin cike giɓin da ake da shi a ƙasar na samar da wadataccen abinci.

LABARAI MASU NASABA

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

Sai dai, ƴaƴan ƙungiyar ta PAN, sun jaddada cewa; ya zama wajibi gwamnatin mai makon shiga wannan haɗa, ta mayar da hankali wajen ƙara bunƙasa fannin a ƙasar.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na Jihar Legas, Foluso Adams ya ce; matuƙar gwamnatin ta wanzar da wannan haɗaka, za ta yi wa fannin ƙasar illa.

Ya yi kira ga gwamnatin, da ta mayar da hankali wajen haɓaka fannin na ƙasar, musamman domin riƙa samar da ƙwai mai yawa a ƙasar.

Shi ma sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar ta PAN na ƙasa, Godwin Egbebe, ya yi gargaɗi kan wannan haɗaka, wanda ya ce; za ta iya haifar da gagarumar koma baya ga fannin a faɗin wannan ƙasa.

“Kamata ya yi gwamnatin ƙasar ta fara yin tunini, kan illar da za ta shafi lafiyar ƴan Nijeriya, kafin ta fara tuninin yin wannan haɗaka,” a cewar Egbebe.

Kazalika, ya sanar da cewa; ya kamata gwamnatin ta yi tunini kan ƙarfin samun kuɗaɗen shigar da ƴan Nijeriya ke samu, wanda wannan haɗakar za ta iya shafar hakan.

Gwamnatin
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Abin Da Ya Sa Gidauniyar NADF Da Bankin Manoma Suka Yi Haḍaka
Noma Da Kiwo

Kha’amuna Khadi Ta Karɓi Jagorancin Gudanarwa Ta Bankin Noma

August 1, 2026
Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya
Noma Da Kiwo

Dalilin Da Ya Sa Aka Horar Da Manoman Tumatir 100 A Garin Zariya

July 18, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Next Post
CGTN Ta Gudanar Da Nazari Kan Yadda Jama’Ar Duniya Ke Kallon Amurka

CGTN Ta Gudanar Da Nazari Kan Yadda Jama’Ar Duniya Ke Kallon Amurka

LABARAI MASU NASABA

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.