Farashin man fetur ya sake tashi a Abuja, yayin da wasu gidajen mai a babban birnin tarayya suka ƙara kuɗin litar man fetur bayan ƙarin farashin da matatar Dangote ta yi.
Rahotanni sun nuna cewa ƙarin farashin ya biyo bayan sauye-sauyen farashin man da Matatar Dangote ke sayarwa ga ‘yan kasuwa, lamarin da ya sa wasu gidajen mai suka sake duba farashin da suke sayar da litar Fetur.
Wannan na zuwa ne bayan jerin sauye-sauyen farashin man da aka samu a watan Agusta. A baya, wasu gidajen mai a Abuja sun ƙara farashin lita daga kusan N1,250 zuwa N1,270, yayin da wasu suka kai kusan N1,275.
Masu sayar da man fetur sun ce ba za su iya ci gaba da sayar da man ƙasa da farashin da suke kashewa wajen sake cike tankunansu ba, yayin da sauye-sauyen farashin ke ƙara haifar da rashin tabbas ga ‘yan kasuwa da masu amfani.
Masana harkar makamashi sun yi gargaɗin cewa ƙarin farashin man fetur na iya ƙara tsadar sufuri da kuma farashin kayayyaki da ayyuka, yayin da abubuwan da suka haɗa da farashin ɗanyen mai a duniya, canjin darajar naira da yanayin samar da man ke ci gaba da tasiri kan farashin cikin gida.














