ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

by Shuaibu Shuaibu
2 months ago
NDLEA

Baya ga yawan mutanen da ake kamawa da gurfanarwa a gaba kotu da kuma kwace miyagun kwayoyi, yana da wuya a iya auna nasarar da shugaban hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Mohammed Marwa, ya samu wajen yaki da miyagun kwayoyi a Nijeriya.

Cikakken bincike da bayanai sun tabbatar da cewa miyagun kwayoyi da ke yawo a kasa nan ba su da yawa idan aka kwatanta rukunin mutane da yankin da miyagun kwayoyi suka fi shafa.

Rashin tsaro da ke addabar kasar nan an danganta shi da ayyukan ma’adinai, talauci, ta’addanci, canjin yanayi da kuma takaddama a tsakanin manoma da makiyayi.

ADVERTISEMENT

Dangantaka da kasuwancin miyagun kwayoyi, duk da haka ba a ba ta kulawar da ta dace. Ta’ammuli da miyagun kwayoyi da safarar miyagun kwayoyi na taka muhimmiyar rawa a manufofin kan yadda za a warware matsalolin tsaro na kasar nan.

A duk duniya, haramtacciyar kasuwancin miyagun kwayoyi na tafiyar da hanyar sadarwa da ta shafi nahiyoyi biyar, yana samar da biliyoyin daloli a matsayin kudaden shiga kuma yana hallaka rayukan miliyoyin mutane.

LABARAI MASU NASABA

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

Mafi yawan masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi na yankin Arewacin Amurka da Turai. Amma a Nijeriya, kamar sauran kasashen Yammacin Afirka, tana kara zama wurin kasuwaci har ma da masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi, wanda hakan ke kara haddasa tashin hankali da rashin tsaro.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da miyagun kwayoyi da laifuka ya kiyasta cewa tan 50 na hotar Iblis daga kudancin Amurka yake fitowa, musamman kasar Colombiya, wanda ake safarar shi zuwa Yammacin Afirka a kowace shekara.

Amma a sabon bincike, an kwato kusan tan 31 na hotar Iblis daga wata jirgi a bakin tekun Yammacin Afirka.

Sai dai NDLEA tana ganin babu shaidar cewa manyan masu safarar miyagun kwayoyi na Kudancin Amurka suna aiki yanzu a Nijeriya, amma ta amincewa cewa wasu na iya kokarin samun wasu miyagun kwayoyi hanyar abokan hulda na cikin gida.

Shugaban hukumar NDLEA, ya fusata da wadannan matakan. Hukumar ta bayar da rahoto a cikin ‘yan makonnin da suka gabata game da rushewar tsarin hadin gwiwar mutanen, kafin lamarin ya ta’azzara.

An tarwatsa dakunan sarrafa kwayar methamphetamine guda biyu a cikin dazuzzukan jihohin Ogun da Oyo, in ji mai magana da yawun hukumar NDLEA, Femi Babafemi.

Abin da yake bayyana a matsayin sabon abu shi ne, har da ‘yan kasar Medico a cikin wadada aka kama a dakunan sarrafa miyagun kwayoyi. An kama su tare da manyan dillalan miyagun kwayoyi da ke Nijeriya.

Da yawa ‘yan Nijeriya na son karin bayani game da wadannan baki da ke kafa dakunan sarrafa miyagun kwayoyi a kasar, ko za a gurfanar da su a kotu ko kuma a ba su damar komawa kasashensu lafiya.

NDLEA ta ce tana da cibiyar sadarwa ta duniya na abokan hulda da abokan aiki inda ake raba bayanan sirri akai-akai kan motsin mutanen.

Babafemi yana yawan cewa NDLEA na aiki tare da mafi yawancin manyan hukumomin tsaro na duniya, musamman takwarorinsu na Amurka, Birtaniya, Kanada, Faransa, Jamus, Brazil, Indiya, Saudiyya, Switzerland, Girka, Afirka ta Kudu, Gambiya da Ghana.

Amma yadda wasu daga cikin ‘yan Medican da aka kama kwanan nan suna sarrafa da miyagun kwayoyi tare da safararsu suka shigo Nijeriya har yanzu ba a bayyana ba. NDLEA na cewa suna samun taimako mai yawa daga ofisoshin jakadancin Nijeriya a kasashen waje.

Amma a bayyane yake ana son jami’an NDLEA su kasance wakilan kasar a wasu daga kasashen waje, musamman a kasashen da ake sarrafa miyagun kwayoyi, kamar yadda wasu kasashe suke da jami’an wakilansu a Nijeriya.

NDLEA
Shuaibu Shuaibu
+ postsBio
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Akwai Ayar Tabaya Kan Zuba Hannun Jarin Dala Miliyan 750 Na Yari
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Wa Tanimu Turaki Ke Fafutukar Karewa?

MASU ALAKA

Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
Bakon Marubuci

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

August 28, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Bakon Marubuci

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Next Post
Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.