ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

by Shuaibu Shuaibu
2 months ago
Kano

Bisa ga abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar adawa ta ADC, rushe shugabancin jam’iyyar a jihar da bakon fuska da aka gani a matsayin dan takarar gwamnan jam’iyyar a Kano, zaben shekarar 2027 na bayyana kamar wacce za ta kasance mai cike da tashin rudani, gasa da rashin tabbas kamar yadda zabukan baya suka kasance a jihar.

Shahararriyar ‘yar jam’iyyar ADC, Naja’atu Mohammed, ta fito karara ta bayyana cewa jam’iyyar ba ta da niyyar ba Ibrahim Khalil tikitin takarar gwamna saboda yana da alaka da Shugaban kasa Bola Tinubu.

Wannan ya sa jam’iyyar ta bai wa babban abokin takararsa, Ibrahim Al Amin, wanda aka fi sani da Ibrahim Little. Idan ADC ta ci gaba ta bai wa Little tikitin takarar jam’iyyar, hakan zai zama babban rarrabuwar kai a jam’iyyar.

ADVERTISEMENT

Little bai taba lashe zaben fitar da gwani ba, ma’ana bai taba samun nasara a zabe ba. Ibrahim Shekarau ya yi nasara a kansa a 2003 waje samun tikitin takarar jam’iyyar APP, kuma Rabiu Kwankwaso ya yi nasara a kansa a 2007 na samun tikitin takarar a jam’iyyar PDP, sannan ya sake rasa tikitin a jam’iyyar a 2023.

Dalili daya shi ne, bai taba samun goyon bayan wakilan jam’iyyar da manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyya ba.

LABARAI MASU NASABA

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

Amma wannan ba shi ne duka labarin siyasar Ibrahim Little ba, yana da kuzari da fasahar jan hankali, musamman ga matasa. A cewar mutane da dama da ya yi mu’amaloli da su, sun ce yana daya daga cikin ‘yan siyasa masu bai wa a Nijeriya da ba su taba samun nasara a zabe ba.

Watakila a karon farko a siyasarsa, Little zai samu damar gwada tashirinsa a wajen jam’iyya da ya dade yana hana shi samun tikitin takarar gwamna.

Jam’iyyun adawa a kasar nan sun sau rarrabuwan kai. Ya dangane da wanda aka tambaya, laifin hakan yana kan Atiku Abubakar ne, wanda ke dage wajen neman shugabanci duk da ya san cewa wa’adin na yanki kudu ne.

Wasu suna zargin Peter Obi da Kwankwaso da karya hadin kan ‘yan adawa da kuma komawa jam’iyyar NDC. Haka kuma wani bangare na laifin an dora wa Shugaba Tinubu don jawo rikici da kuma kawo cikas a bangaren shari’a ga jam’iyyun adawa.

Amma duk da wannan hayaniyar, siyasar Kano ba ta taba rashin samun gazawa ba wajen yin tsananin gasa. Hanyar da Gwamna Abba Yusuf da Rabiu Kwankwaso suka rabu da juna da kuma canjin jam’iyoyinsu daban-daban ya kunna wutar gasar kujerar gwamna a 2027.

Amma sai dai zabin Kwankwaso na sanya sunan dan takarar gwamnan NDC da abokin takararsa ya rage kwarin giwa.

Akwai yiwuwar fitowar Little a matsayin dan takarar ADC ya kara sabon sauyi a siyasar 2027 a jihar. Yanzu gwagwarmaya ta rabu zuwa gida uku, inda gwamna mai mulkin Abba ke fafatawa da bangaren Kwankwaso da kuma kokarin Little na jawo jama’a daga tushe.

Kano
Shuaibu Shuaibu
+ postsBio
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Akwai Ayar Tabaya Kan Zuba Hannun Jarin Dala Miliyan 750 Na Yari
  • Shuaibu Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/shuaibu-shuaibu/
    Wa Tanimu Turaki Ke Fafutukar Karewa?

MASU ALAKA

Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
Bakon Marubuci

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

August 28, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Bakon Marubuci

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Next Post
Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.