ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Enekweci Ne Zai Jagoranci Tawagar Nijeriya A Wasannin Commonwealth Na Bana

by Abubakar Sulaiman
2 months ago

Hukumar wasanni ta ƙasa (NSC) ta naɗa fitaccen ɗan wasan Nijeriya, Chukwuebuka Enekwechi, a matsayin kyaftin na tawagar Nijeriya a wasannin Commonwealth na wannan shekarar ta 2026 a birnin Glasgow na ƙasar Scotland, saboda girmama nasarorin da ya samu da kuma kyakkyawan wakilcin da ya yi wa Nijeriya a wasannin ƙasa da ƙasa, an sanar da naɗin ne a cikin wata sanarwa da Kola Daniel, mataimaki na musamman kan kafafen yaɗa labarai ga Darakta Janar na NSC, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai a ranar Talata.

Enekwechi zai jagoranci tawagar Nijeriya tare da Folashade Oluwafemiayo, wacce ta lashe kyautar zinare sau biyu a gasar Paralympic, wacce za ta kasance kyaftin a ɓangaren mata a wasannin da za’a fara a ranar 23 ga watan Yuli, ɗan wasan mai shekaru 33 da ke zaune a ƙasar Amurka ya kasance ɗaya daga cikin fitattun yan wasa daga nahiyar Afirika da za su fafata a gasar, shi ne zakaran da ya lashe kyautar gwarzon Afirka, ya lashe zinare a gasar wasannin Afirka ta 2019, ya kuma lashe kyautar azurfa a gasar Commonwealth ta shekarar 2018, inda ya zama ɗaya daga cikin yan wasa mafi nasara daga wannan ɓangaren a Nijeriya.

Darakta Janar na hukumar wasanni ta ƙasa (NSC), Hon. Bukola Olopade, ya ce naɗin ya nuna jajircewar hukumar wajen kyautatawa waɗanda suka bayar da gudunmawarsu wajen samun kyaututtuka a wasannin ƙasa da ƙasa ta hanyar bayar da jagoranci ga waɗanda suka cancanta, a cewar Olopade, dukkan kyaftin ɗin na wannan karon sun nuna ɗabi’un ladabi, juriya, kishin ƙasa da mutuntawa, inda halayyarsu ya zama abin koyi ga matasan yan wasa.

ADVERTISEMENT

“Mun zaɓi mutane waɗanda ba kawai tarihi mai kyau garesu a wasanninsu ba, sun nuna alama na iya jagoranci kuma sun yi aiki a matsayin masu ba da shawara ga matasan yan wasa ta hanyar ƙwarewa, jajircewarsu da kuma sadaukarwarsu ga Nijeriya,” in ji Olopade, ya ƙara da cewa naɗin ya kuma zama girmamawa ga sadaukarwar da ƴan wasan biyu suka yi wajen wakiltar ƙasar a wasannin ƙasa da ƙasa.

“Shawarar da muka yanke na ba su jagorancin tawagar Nijeriya ita ce kuma hanyarmu ta yaba wa ga gudummawar da suka bayar wajen ɗaga martabar Nijeriya a wasannin Duniya, NSC ta yi imanin cewa ƙwararrun ƴan wasan biyu za su taka muhimmiyar rawa a jagoranci a ciki da wajen filin wasa, inda za su taimaka wa matasan yan wasa su jure matsin lamba na shiga ɗaya daga cikin manyan wasannin Commonwealth.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

An shirya cewa tawagar Nijeriya za ta bar ƙasar a ranar 2 ga watan Yuli domin yin atisayen makonni uku kafin wasannin a birnin Aberdeen, inda ƴan wasan za su kammala shirye-shiryensu na ƙarshe kafin su tafi Glasgow, hakazalika tawagar ta bayyana cewar ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin PUMA wajen samarwa yan wasan tufafin wasa, za a gabatar da kayan wasan ga tawagar a ranar 1 ga watan Yuli.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 

LeBron James Zai Bar Los Angeles Lakers 

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.