ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wane Ne Gwarzo Tsakanin Pele Da Maradona Da Messi?

by Abba Ibrahim Wada
2 months ago
Messi

Masu karato za su ce tabbas wannan jerin sunayen bai cika ba tunda babu danwasa Cristiano Ronaldo, wanda shima yana daya daga cikin gwarazan ‘yanwasan duniya a yanzu.

Za a iya cewa Lionel Messi ya buga wasan karshe na gasar kofi duniya a karo na uku a rayuwarsa, wata tambaya da aka saba yi ta dawo: Shin zakakurin danwasan Aregentinan ya fi kowa zarra a tarihin kwallon kafa? Ya zarce dan kasarsa, Diego Maradona da kuma dan Brazil Pele?

Messi mai shekara 39, ya zamo danwasan Argentina da ya fi daukar hankali a gasar kofin duniya ta 2026. Masu sharhi sun ce duk da a yanzu ana iya cewa ya wuce zamaninsa, Messi na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen samun sakamako a wasanni ta hanyar jan ragamar sauran yanwasan tawagar tamkar wani koci na cikin fili.

ADVERTISEMENT

Masu cewa Messi ne ya fi kowanne danwasa a tarihin kwallon kafa suna kafa hujja ne da dalilai guda biyu: Karkon da danwasan ya yi yana jan zarensa da kuma bayar da sakamako a lokacin da ake bukata.

Ba kamar yadda tauraruwar ‘yanwasa ta saba dushewa da zarar sun yi tashe

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

na dan lokaci ba, Messi ya shafe kusan shekara 20 yana jan zarensa a wasan kwallo a Argentina da kungiyoyin da ya bugawa wasanni.

A cikin wadannan shekarun, ya lashe kyautar gwarzon danwasa ta Ballon d’Or har takwas, ya ci gasar kasashen Sifaniya da Faransa, da gasar zakarun Turai da Copa America da kuma kofin duniya a 2022, yayin da ya kafa wani tarihin a fannin cin kallaye da yawa.

Magoya bayan Messi suna kuma nuna kwarewar shi wajen iya buga wasa a duk inda ya samu kansa, daga yadda Barcelona ta mamaye Turai zuwa kane-kanen da Argentina ta yi a fagen kwallon kafa a duiya a ‘yan shekarun nan.

Masoyan Messi suna ganin karkon da ya yi, da basirarsa da gudunmuwar da ya ke bayarwa wajen samun nasarar kungiyoyin shi, su ne banbancin shi da sauran ‘yanwasa da aka yi a tarihi.

Tsohon danwasan Fransa, Thierry Henry ya zayyana wasu abubuwa na musamman kan tsohon abokin wasansa a Barcelona. A wata hira da jaridar Sifaniya Marca, Henry ya tuna yadda a lokacin, da zarar an tunzura Messi to shi kenan an kira ruwa don kuwa nan take yake canza akalar wasa.

A Argentina, idan ana kwatancen ‘yanwasa ba a mayar da hankali kan Pele da sauran manyan ‘yanwasa da suka yi fice a duniya, don kuwa an fi mayar da hankali ga Diego Maradona, kyaftin din kasar da ya jagoranci kungiyar da ta lashe kofin duniya a 1986.

Tasirin Maradona ya wuce kwallon kafa. Ga ‘yan Argentina da yawa, ya zama wani jigo na hadin kan kasa.

Shekaru da dama, wasu ‘yan Argentina na matukar kaunar Messi, amma duk da haka suna kallon Maradona a matsayin wanda ya fi dacewa a kira jagora a kasar. Maradona wanda ya rasu a 2020, ya tashi ne a cikin talauci amma ya fito karara ya kalubalanci mahukunta inda ya shiga harkokin siyasa, tare da samun goyon bayan jama’a.

A nasa bangaren Messi ya zabi ya zama na daban, ba ya shiga harkar siyasa kuma babu ruwansa da duk wani abu da ba wasan kwallo ba.

Martabar Messi ta karu bayan Argentina ta lashe Copa America a 2021, ta kawo karshen jiran shekara 28 ba tare da ta lashe gasar kwallon ƙafa ba. Tasirinsa ya karu a gasar kofin duniya ta 2022, inda ya taimakawa. Argentina ta lashe gasar karo na uku.

A lokacin gasar Messi ta Copa America, ya nuna kwarewa a fanni jagoranci da tafiya tare da kowa, lamarin da a baya magoya bayan kungiyar ke ganin cewa Maradona ne kawai zai iya yi. Wasu ‘yan Argentina suna ganin cewa Messi ya zarce Maradona a tasirin kwallon kafa a kasar.

Wasu masu sharhi na ganin cewa ba Maradona kadai Messi ya yi wa zarra ba, har ma da Pelé, gwarzon danwasan Brazil da ake wa lakabi da ”Sarkin Kwallon kafa”, wanda ya rasu a shekarar 2022.

Pelé ya kasance danwasa daya tilo da ya taba lashe kofin duniya sau uku, inda ya taimakawa Brazl ta ci kofin a 1958 da 1962 da kuma 1970. A wata hira da jaridar Folha de S.Paulo, ta yi da shi a 2018, Pelé ya ce Maradona ya zarce Messi nesa ba kusa ba.

Ya ce Messi ya dogara ne ga kafarsa ta hagu kacal, don haka ba ya cikin zaratan ‘yanwasan da ake kira ”sun cika kowacce ka’ida ta kwarewar iya buga kwallon kafa”.

Bayanan da ke kasa na nuni da cewa da kididdigar kofuna da kwallaye kawai ake bi wajen tantance wanda ya fi gawurta da yanzu wannan muhawara ta kare. Messi ya tara kyautuka da abubuwan tarihi a matsayinsa da kuma matakin kungiyoyi ta yadda ba wanda ya kama kafarsa a wannan fannin.

Amma wadannan lambobi kadai ba za su iya tantance danwasan da ya zama gagarabadau ba a kwallo. Don haka ake ci gaba da wannan muhawara. Wani abu da ya sanya wannan muhawara ta kara zama mai wahala shi ne: Pelé da Maradona da kuma Messi sun yi tashe ne a zamani daban-daban.

Lokacin da Pelé ya lashe kofin duniya a karon farko a 1958, babu fasahar zamani ta yada wasanni kwallo cikin sauki. Ya zuwa zamanin Maradona a shekarar 1980, wasan ya gawurta har ya zamo wata ma’aikata da ake juya biliyoyin Dala. Messi kuwa ya zo a lokacin da akwai kayan aikin zamani na tantance duk wani salo da ya yi a fili, da tsarin kiwon lafiya mai inganci kuma ga fasahar zamani da ke taimakawa wajen yanke hukunci kan duk abin da ya faru a filin wasa.

Saboda haka kwatanta wadannan ‘yanwasa abu ne mai wahalar gaske. Domin haka da wuya a iya kawo karshen wannan muhawara ta gano danwasan da ya zarce kowa zakakuranci a tarihi.

Messi
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Messi

Amurka Ta Kakaba Harajin Kaso 12.5% A Kan kayayyakin Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.