ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda ‘Yan Spain Suka Mamaye Kyaututtukan Kofin Duniya

by Abba Ibrahim Wada
2 months ago
Spain

Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta karrama wasu gwarazan ‘yanwasa biyar da suka yi fice a gasar Kofin Duniya ta 2026 da aka kammala a ranar Lahadin da ta gabata.

A kowace Gasar Kofin Duniya da FIFA ke shiryawa takan lura da wasu ‘yanwasan da suka fi fice a fannoni daban-daban domin karrama su kan rawan da suka taka a gasar.

Sifaniya ce ta lashe kofin bayan doke Argentina – wadda ta dauka a 2022 – da ci 1-0 a wani wasa da ya dauki hankalin masoya kwallon kafa a fadin duniya. Karo na biyu kenan da Spain ke daukar kofin bayan wanda ta dauka a gasar 2010 da aka gudanar a kasar Afirka ta Kudu.

ADVERTISEMENT

‘Yan wasa biyar da FIFA ta karrama bayan kammala gasar Kofin Duniyar su ne:

RODRI

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Dan wasan tsakiya na Sifaniya ya lashe kyautar Golden Ball, wadda ake bai wa gwarzon dan wasa a gasar baki daya. Kyaftin din tawagar Sifaniyan ya kasance jigon tsakiyar fili, inda ya taimaka wa kasarsa wajen sarrafa wasanni da kuma kaiwa ga lashe kofin duniya ba tare da rashin nasara ba.

Dan wasan tsakiyar na Manchester City ya kware wajen sarrafawa da rarraba kwallo a tsakiyar fili. Rawar da ya taka ta sa aka dauke shi a matsayin mafi tasiri a gasar.

MBAPPE

Kylian Mbappé na Faransa ne ya lashe kyautar danwasan da ya fi zura kwallo a raga, wadda ake kira ‘Golden Boot’ da FIFA ke bayarwa. Dan wasan gaban na Real Madrid ya zura kwallo 10 a gasar, inda ya kare a gaban Messi na Agentina mai takwas. Banda  bajintar zura kwallaye a gasar 2026, Mbappé ya kafa tarihin danwasan da ya fi zura kwallaye a tarihin gasar Kofin Duniya, inda ya ci 22.

Duk da cewa Faransa ba ta kai wasan karshe ba, Mbappé ya nuna bajinta wajen cin kwallaye a kusan kowane mataki na gasar.

UNAI SIMÓN (SIFANIYA)

Unai Simón mai tsaron ragar Sifaniya ne ya lashe kyautar Safar Zinare ta mai tsaron raga mafi kwazo a gasar Kofin Duniya ta 2026. Simón ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Spain, inda ya yi wasanni bakwai ba tare da kwallo ta shiga ragarsa ba.

Kuma a duka tsawon gasar sau daya ne kawai kwallo ta shiga ragarsa.

PAU CUBARSÍ (SIFANIYA)

Pau Cubarsí na Sifaniya ne ya lashe kyautar matashin danwasan mafi kwazo a gasar.

Mai tsaron bayan ya nuna jajircewa wajen tsaron bayan Sifaniya a daukacin gasar, inda ya buga duka wasannin kasar takwas a gasar. Dan wasan mai shekara 19, da ke buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ya haska sosai duk da karancin shekarunsa a gasar.

NETHERLANDS

Kyauta ta karshe ita ce wadda aka bai wa Netherlands a matsayin wadda ta fi nuna kyawawan dabi’u a gasar. FIFA ta ce Netherlands ta nuna kyakkyawar dabi’a da ladabi da mutunta dokokin wasa a tsawon gasar. Bayanai sun ce katin gargadi uku kawai aka bai wa tawagar, yayin da ba ta yi wani laifin da ya cancanci katin kora ba.

Duka katin gargadin uku na Netherlands ta same ne a wasan farko da ta buga da Japan. Bayan haka ba ta kara samun katin gargadi ba a duka sauran wasannin nata, har zuwa lokacin da Moroko ta fitar da ita a matakin ‘yan 32.

Spain
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Yaushe Za A Fara Kofin Zakarun Turai
  • Abba Ibrahim Wada
    Messi Ya Yi Ritaya A Argentina: Da Me Za Mu Iya Tuna Gwarzon Duniyar?
  • Abba Ibrahim Wada
    Su Waye ‘Yan wasan Nijeriya Da Za Su Buga Gasar Firimiyar Ingila Ta Bana?
  • Abba Ibrahim Wada
    Chelsea A Ƙarƙashin Xavi Alonso

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Yadda Kotun Daukaka Kara Ta Kama Hanyar Cin Gashin Kanta

Yadda Kotun Daukaka Kara Ta Kama Hanyar Cin Gashin Kanta

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.