ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, September 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Watsi Da Kiran Obi Na Buƙatar Tinubu Ya Yi Murabus

by Sadiq
3 months ago

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da kiran da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi na neman Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, fadar shugaban ƙasa ta ce kalaman Obi ba su fayyace gaskiyar halin da Nijeriya ke ciki ba.

Sanarwar ta bayyana cewa Nijeriya na amfani da tsarin shugabanci na shugaban ƙasa ne, ba irin na majalisar dokoki kamar na Birtaniya ba, don haka shugaban ƙasa yana da wa’adin shekaru huɗu da doka ta tanada, kuma ba a sauke shi da kiran jama’a ko rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta ba.

ADVERTISEMENT

Ta kuma ce sakamakon zaɓe na baya-bayan nan ya nuna cewa Tinubu na da goyon bayan jama’a, inda ta ce ya kamata Obi ya jira lokacin zaɓen 2027 maimakon yin kiranye-kiranye a shafin X.

A ɓangaren tsaro, fadar shugaban ƙasa ta ce gwamnati ta samu nasarori wajen ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, da kakkaɓe ‘yan ta’adda, da kuma ƙarfafa aikin sojoji a faɗin ƙasar.

LABARAI MASU NASABA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

Ta kuma ce an kawar da ‘yan ta’adda sama da 15,000 a dazuka, sannan an inganta kayan aiki da horar da jami’an tsaro a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

A ɓangaren tattalin arziƙi, sanarwar ta ce Nijeriya na samun ci gaba ta hanyar haƙar mai, ƙarin kuɗaɗen shiga, da zuba jari daga ƙasashen waje.

Ta ƙara da cewa matsin tattalin arziƙi da hauhawar farashi matsala ce ta duniya baki ɗaya, ba ta Nijeriya kaɗai ba, tana danganta hakan da rikice-rikicen duniya.

A ƙarshe, fadar shugaban ƙasa ta bayyana kiran Obi a matsayin siyasa, tana mai cewa Shugaba Tinubu yana mayar da hankali kan gyare-gyare, tsaro, da bunkasa tattalin arziƙi.

MASU ALAKA

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro
Manyan Labarai

Sakkwato: Al’ummar Tambuwal Sun Yi Zanga-Zanga Kan Taɓarɓarewar Tsaro

September 12, 2026
Manyan Labarai

Idan Atiku Ya Janye, Za Mu Kula Da Shi Bayan Mun Yi Nasara – Kwankwaso

September 11, 2026
Manyan Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki Na Ƙasa Gaba Ɗaya

September 11, 2026
Next Post
Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya

Yara 14 Sun Rasu Sakamakon Gobara A Kudancin Indiya

LABARAI MASU NASABA

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

Zan Dawo Da Tallafin Mai Ne Don Rage Farashin Fetur Da Na Sufuri – Atiku

September 12, 2026
An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

An Gargaɗi Mazauna Kusa Da Kogin Kaduna Kan Sako Ruwa Daga Shiroro

September 12, 2026
Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

Shekaru 22 Bayan Rushewar Nigeria Airways, Gwamnati Ta Biya Ma’aikata 2,700 Biliyan 18

September 12, 2026
Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

Kalaman Christopher Musa Game Da El-Rufa’i Na Ci Gaba Da Tayar Da Ƙura

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Zamfara

September 12, 2026
Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

Gwamna Dauda Lawal Ya Raba Motocin Aiki Ga Manyan Makarantu A Zamfara

September 12, 2026
Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

Dangote Ya Ƙara Farashin Fetur, Kwana 2 Kafin Shiga Kasuwar Hannun jari

September 12, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Jam’iyyar APC Ce Za Ta Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Gwamnoni A Nijeriya -Dikko Raɗɗa

September 12, 2026
NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur Zuwa ₦860 Kan Kowacce Lita – IPMAN

Mene Ne Ra’ayinku Kan Dawo Da Tallafin Man Fetur Ko Barin Sa?

September 12, 2026
Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

Sin Ta Nuna Rashin Jin Dadinta Ga Italiya Da Tarayyar Turai Kan Ziyarar Jami’ar DPP

September 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.