ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƙa’idojin Gudanar Da Biyan Kuɗi Nan Take Domin Kare Kai Daga Zamba

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
3 weeks ago
Noma

Babban Bankin Nijeriya (CBN) na ƙara ƙaimi wajen yaƙi da damfarar intanet ta hanyar fitar da sabbin ƙa’idoji kan tsarin biyan kuɗi nan take (Instant Payment – IP). Sabbin ƙa’idojin sun tanadi matakai masu yawa domin ƙara tsaron hada-hadar kuɗi, kare kwastomomi da kuma daidaita tsarin da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.

Ana sa ran waɗannan sabbin dokoki za su taimaka wajen rage damfarar Intanet tare da bai wa kwastomomi ƙarin iko kan yadda ake gudanar da hada-hadarsu.

Daga cikin sabbin matakan akwai bai wa kwastomomi damar dakatar da amfani da tsarin biyan kuɗi nan take a asusunsu na wani lokaci idan sun ga dama, duk da cewa za su iya ci gaba da canja wurin kuɗi ta hanyar ziyartar reshen banki.

ADVERTISEMENT

A wata sanarwa da CBN ya fitar, ya ce tsarin shiga da fita daga wannan aiki (opt-in da opt-out) dole ne ya kasance ƙarƙashin tsarin tabbatar da sahihanci mai amfani ta hanyoyi da dama. Haka kuma, duk sabbin asusun banki za a sanya su cikin tsarin biyan kuɗi nan take kai tsaye, sai dai kwastoma na da damar sauya wannan zaɓin daga baya.

A ɓangaren bankuna kuwa, an umurce su da su bi wannan umarni ba tare da gazawa ba, tare da bai wa kwastomomi damar sanya iyakar adadin kuɗin da suke son canjawa a kowace mu’amala, bayan an yi tantancewa da nazarin haɗari. Sai dai iyakar adadin da dokoki suka tanada a yanzu ba za ta canza ba.

LABARAI MASU NASABA

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

Bugu da ƙari, an umurci cibiyoyin kuɗi da su samar da tsarin sa ido kan damfara a ainihin lokacin da ake gudanar da mu’amala, tare da ƙara tsaurara matakan tantance bayanan masu buɗe ko sake buɗe asusun banki ta Intanet.

CBN ya kuma ba da umarnin cewa manhajar banki ta wayar hannu za ta kasance a haɗe da na’ura guda ɗaya kacal a lokaci guda. Idan aka kunna ta a sabuwar na’ura, za a sanya iyakar canja kuɗi ta Naira 20,000 ne kawai a cikin sa’o’i 24 na farko.

A ƙarƙashin tsohon tsarin, ba a tilasta wa cibiyoyin kuɗi samar da damar da kwastomomi za su iya shiga ko fita daga sabis na biyan kuɗi nan take a cikin manhajojin banki ba. Amma sabbin ƙa’idojin sun wajabta wa cibiyoyin kuɗi su bai wa kwastomomi damar ficewa daga wannan sabis a kowane lokaci, muddin sun cika sharuɗan tabbatar da sahihancinsu ta MFA.

Sabbin ƙa’idojin sun yin tanadin cewa duk sabbin kwastomomi za a saka su cikin tsarin opt-in kai tsaye. Idan kwastoma ya fita daga tsarin (opt-out), ba zai iya yin canjin wurin kuɗi ta Intanet nan take ba, sai dai ya je reshen banki domin gudanar da irin wannan mu’amala.

Kafin fitar da waɗannan ƙa’idoji, iyakar adadin kuɗin da mutum zai iya canjawa ta kasance Naira miliyan 25 ga mutum ɗaya, yayin da ta kamfanoni ta kasance Naira miliyan 250, ba tare da damar kwastoma ya rage wannan adadi yadda yake so ba.

Sai dai sabbin ƙa’idojin sun ba da damar mutane da kamfanoni su daidaita iyakar kuɗin da suke son canjawa gwargwadon buƙatarsu, bayan cibiyar kuɗi ta gudanar da cikakken bincike da matakan kula da haɗari.

Domin tabbatar da tsaro, sabuwar iyakar adadin kuɗin da kwastoma ya zaɓa zai fara aiki ne kawai bayan ya kammala tsarin tabbatar da sahihancinsa ta hanyoyi da dama).

Masana harkokin kuɗi sun bayyana cewa sabbin ƙa’idojin sun kuma tanadi matakan tsaro na musamman ga mutanen da ke son buɗe sabon asusu ta Intanet ko kuma sake dawo da tsohon asusun da aka dakatar.

Waɗannan matakan sun haɗa da: Yin gwajin tabbatar da cewa mai amfani na ainihi; Tabbatar da ingancin bayanan BƁN ko NIN kai tsaye yayin buɗewa ko sake dawo da asusun ta Intanet;

Amfani da ingantattun hanyoyin tantancewa mai amfani kamar tantance fuska ko yatsa, soft token da hard token yayin sake dawo da asusu.

Masanan sun bayyana cewa Liɓeliness Check wata hanya ce ta tsaro da ke amfani da fasahar tantance halittu domin tabbatar da cewa wanda ke gudanar da mu’amala mutum ne na gaske da ke wurin, ba hoto, bidiyo ko kuma hoton bogi da aka ƙirƙira ta fasahar deepfake ba. Wannan na aiki ne ta hanyar nazarin siffofin fuska kamar yanayin fata, motsin ido da zurfin fuska, domin hana masu damfara amfani da hotunan bogi.

Sabbin ƙa’idojin sun kuma wajabta wa cibiyoyin kuɗi su kafa tsarin sa ido kan damfara a dukkan fannoni na mu’amalar kuɗi, wato kuɗin da ke shiga da kuma waɗanda ke fita daga asusu. Wannan tsarin zai iya gano mu’amaloli masu kama da damfara nan take, ya dakatar da su, tare da bai wa bankuna damar ɗaukar matakin gaggawa.

A tsohon tsarin, kwastomomi na iya amfani da manhajar bankinsu a na’urori da dama a lokaci guda. Amma a ƙarƙashin sabbin ƙa’idojin, za a iyakance amfani da manhajar banki zuwa na’ura guda ɗaya kacal a lokaci guda. Idan aka kunna manhajar a wata sabuwar na’ura, tsohuwar za ta daina aiki kai tsaye, sannan za a sake kunna sabuwar ne bayan an kammala tantance sahihancin mai amfani.

CBN ya kuma tanadi waɗannan matakai ga masu amfani da manhajar banki da kuma bankin intanet:

Sabbin masu asusu: Bayan kunna manhajar banki, duk kuɗin da ke shiga da waɗanda ke fita daga asusun za su kasance iyakar Naira 20,000 kacal a cikin sa’o’i 24 na farko.

Masu tsofaffin asusu: Idan suka kunna manhajar banki a sabuwar na’ura, kuɗin da za su iya fitarwa daga asusun a cikin sa’o’i 24 na farko ba zai wuce Naira 20,000 ba.

An tsara waɗannan sabbin matakai ne domin ƙara kare kwastomomi daga damfarar intanet da kuma inganta tsaron mu’amalar kuɗi a Nijeriya.

Abin lura shi ne cewa, duk wanda zai shiga bankin intanet a karon farko ta sabuwar na’ura, dole ne ya bi ingantaccen tsarin tabbatar da sahihancinsa ta tsarin (Multi-Factor Authentication – MFA).

Yana da muhimmanci a jaddada irin rawar da waɗannan sabbin ƙa’idoji za su taka wajen yaƙi da damfarar intanet da sauran matsalolin da ke rage amincewar kwastomomi da tsarin hada-hadar kuɗi.

Haka kuma, ya dace a yaba wa Babban Bankin Nijeriya (CBN) saboda hangen nesa da ya nuna wajen fitar da Sabbin Ƙa’idojin Gudanar da Tsarin Biyan Kuɗi Nan Take ga cibiyoyin kuɗi. Waɗannan ka’idoji na nuna wani gagarumin ci gaba wajen kare mu’amalolin kuɗi na zamani a faɗin Nijeriya.

Daga 1 ga Yulin 2026, duk cibiyoyin kuɗi za su fara aiwatar da waɗannan sabbin matakai. Daga cikin abubuwan da aka tanada akwai wajabcin gudanar da cikakken bincike kan tsaro da kuma Binciken Tasirin Kare Bayanai (Data Protection Impact Assessment – DPIA) domin tabbatar da bin tanade-tanaden Dokar Kare Bayanai ta Nijeriya ta 2023.

Zamba
Rabi'u Ali Indabawa
+ posts Bio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna
Zamba
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA
  • Sulaiman
    Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti
  • Sulaiman
    Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026
  • Sulaiman
    Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

MASU ALAKA

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu
Rahotonni

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

July 17, 2026
Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau
Rahotonni

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

July 17, 2026
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara
Rahotonni

Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

July 17, 2026
Next Post
Husaini Isa Ya Gargaɗi Ƴan Takarar NDC A Kano Kan Buƙatar Kiyaye Ƙa’dojin Jam’iyya

Husaini Isa Ya Gargaɗi Ƴan Takarar NDC A Kano Kan Buƙatar Kiyaye Ƙa’dojin Jam’iyya

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

Xi Ya Gana Da Babban Sakataren MDD Da Firaministocin Thailand Da CambodiaA

July 17, 2026
Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

Zaben Fidda Gwani Da Ake Takaddama:APC Ta Dauki Matakan Kauce Wa Shari’o’in Kotu

July 17, 2026
Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

Sin Ta Mika Sabuwar Manhajar Gargadin Gaggawa Ta MAZU Ga Djibouti

July 17, 2026
Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima

Sake Daukar Shettima Da Tinubu Ya Yi Zai Kara Karfafa APC A Zaben 2027 –Farfesa Yerima

July 17, 2026
Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026

Kwamitin Ba Da Shawara Kan Hadin Gwiwar Kasa Da Kasa Na Dandalin BRI Ya Yi Taronsa Na 2026

July 17, 2026
Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

Wang Huning Ya Ziyarci Koriya Ta Arewa

July 17, 2026
Yawan Mu’amalar Kudi Tsakanin Mazauna Sin Da ’Yan Kasashen Waje Ya Hau Wani Sabon Matsayi A Tarihi

Yawan Mu’amalar Kudi Tsakanin Mazauna Sin Da ’Yan Kasashen Waje Ya Hau Wani Sabon Matsayi A Tarihi

July 17, 2026
Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

Gasar Kofin Duniya: Da Ƙarfinmu Muka Kawo Matakin Da Muke Yanzu – Messi

July 17, 2026
Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala

Matatar Man Dangote Ta Dawo Sayar Da Fetur A Dala

July 17, 2026
Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Bude Babban Taron AI Na Duniya Na 2026 Tare Da Gabatar Da Jawabi

July 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.