ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, October 23, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gidauniya Ta Maka TikTok A Kotu Kan Toshe Masu Amfani Da Manhajar A Wasu Jihohin Arewa

by Sulaiman
2 weeks ago
TikTok

Gidauniyar ‘Foundation for Digital Justice and Sustainable Development’ ta shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin cewa kamfanin TikTok ya daƙile wa wasu masu amfani da manhajar damar shiga shafinsa a wasu jihohin Arewacin Nijeriya.

A cikin karar da jaridar Daily Trust ta gani, kungiyar ta zargi TikTok da toshe masu amfani da manhajar a jihohin Kaduna, Kebbi, Kano da Sakkwato.

Kungiyar, ta hannun lauyanta Festus Ogun, ta bukaci kotun ta tantance ko matakin da ake zargin TikTok ya dauka ya saba wa ‘yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa ‘yan kasa, tare da tantance ko hakan ya zama nuna wariya ga masu amfani da manhajar a jihohin da abin ya shafa.

ADVERTISEMENT

An shigar da karar mai kwanan wata 5 ga Oktoba, 2026, bisa tanade-tanaden Sashe na 39, 42, 45 da 46 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, da kuma Fundamental Rights Enforcement Procedure Rules 2009, tare da wasu tanade-tanaden Yarjejeniyar Afirka kan ’Yancin Dan’Adam.

Mai shigar da karar ya ce TikTok ba shi da hurumin doka na takaita masu amfani da manhajar a jihohin Arewa da abin ya shafa, yayin da yake barin masu amfani da manhajar a sauran sassan kasar su ci gaba da amfani da ita ba tare da takura ba.

LABARAI MASU NASABA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

Gidauniyar ta bukaci kotun ta ayyana matakin da ake zargin TikTok ya dauka a matsayin “ba daidai ba, wanda ya saba wa kundin tsarin mulki kuma ba shi da ingantaccen dalili”, tana mai cewa hakan ya keta hakkokin ’yan kasa na fadin albarkacin baki da kuma samun kariya daga wariya.

Har ila yau, Gidauniyar na neman kotun ta bayar da umarnin cewa TikTok ya gaggauta cire takunkumin da ake zargin ya sanya, tare da hana kamfanin sake takaita masu amfani da manhajar a Arewacin Nijeriya ko wani ɓangare na kasar ba tare da ingantaccen dalili na doka ba.

TikTok
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Ya Rantsar Da Manyan Sakatarori Biyar
  • Sulaiman
    Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwaransa Na Djibouti
  • Sulaiman
    Ta Yaya Ake Ci Gaba Da Fitar Da Sabbin Kayayyaki A Yayin Baje Koli Na Canton Fair
  • Sulaiman
    Darasi Daga Zuhudun Manzon Allah (SAW)

MASU ALAKA

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara
Manyan Labarai

Jama’ar Gari Sun Kashe ’Yan Bindiga Sama Da 30 A Wani Gumurzu A Zamfara

October 23, 2026
Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu
Manyan Labarai

Yaƙin Neman Zaɓe: ’Yansanda Sun Hana Manyan Motoci Shiga Kaduna Gabanin Ziyarar Tinubu

October 23, 2026
Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau
Manyan Labarai

Sanata Abdul’aziz Yari Ya Ziyarci Sarkin Zazzau

October 23, 2026
Next Post
Bauchi Ta Ƙaddamar Na’urorin Kula Da Mata Masu Juna Biyu Na N625m

Bauchi Ta Ƙaddamar Na'urorin Kula Da Mata Masu Juna Biyu Na N625m

LABARAI MASU NASABA

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

Mutane 7 Sun Rasu, 11 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Gombe

October 23, 2026
Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

Xi Jinping Ya Umarci Yin Bakin Kokari Wajen Ceto Mutanen Da Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.0 Ta Rutsa Da Su A Xizang

October 23, 2026
Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

Binciken CGTN: Daga Samar Da Tsare-tsare Zuwa Aiwatarwa Tsarin Jagorancin Duniya Na Bukatar Karin Dabaru Na Hakika

October 23, 2026
NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

NUJ Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yaɗa Rahotannin Da Ba Su Da Inganci Kan Cire Limami Kan Tallata Tinubu A Bauchi

October 23, 2026
Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

Ma’aikatan Lafiya Sun Fara Shirin Tsunduma Yajin Aiki Kan Bashin Alawus Na Wata 19

October 23, 2026
Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

Cikakke Kuma Tsattsauran Jagoranci A Kanta Dabarar JKS Ce Ta Gina Kanta

October 23, 2026
Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

Shugaba Xi Ya Aike Da Sako Ga Dandalin Xiongan Na 2026

October 23, 2026
Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

Real Madrid Na Tattaunawa Da Bellingham Don Tsawaita Kwantiraginsa

October 23, 2026
MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

MOC: Manufofin Bunkasa Amfani Da Kayayyaki Sun Fadada Kasuwar Cinikayyar Kayayyaki A Kai A Kai A Farkon Watanni 9 Na Bana

October 23, 2026
NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

NLC Ta Gabatar Da Buƙatu 6 Tare Da Barazanar Yajin Aiki A Nijeriya Baki Ɗaya

October 23, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.