ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Girmama Cikakken ’Yanci Da Yankunan Kasa, Wajibi Ne A Kan Kowacce Kasa Babba, Ko Karama

by CMG Hausa
3 years ago
'yanci

A matsayinta na shugabar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a wannan wata, kasar Sin, bisa jagorancin wakilinta na dindindin, ta kira taro kan samar da tsarin tsaro da ya dace da yanayin da ake ciki da girmama cikakken ’yanci da yankunan dukkan kasashe, domin samun yanayin tsaro mai karko a duniya. 

Hakika kiran wannan taron da Wakilin Sin Zhang Jun ya yi ta zo a daidai lokacin da ya dace, ganin yanayin kalubale da duniya take ciki da kuma yadda ake keta cikakken ’yancin kasashe da takalar fada da kuma ingiza tayar da rikici.

  • Sin Ta Bayyana Kalaman Jakadan Amurka A Sin A Matsayin Shaidar Dake Nuna Tunani Irin Na Danniya

Zamanin mulkin mallaka da danniya ko cinikin bayi ya wuce. Ana cikin wani sabon zamani da ake neman ci gaba ta hanyar girmamawa da moriyar juna.

ADVERTISEMENT

Akwai bukatar kasashen da suke ganin su shafaffu da mai ne, su dai na kokarin dawo da hannun agogo baya, domin duniya ta ci gaba. Girmama cikakken ’yancin kasa ya zama wajibi a kan kowacce kasa babba, ko karama.

Kasashen duniya da al’ummominsu sun bambanta, suka san yanayin da suke ciki da manufofi mafi dacewa da su, kuma su kadai ne za su san yadda ya kamata su shawo kan matsalolin dake addabarsu.

LABARAI MASU NASABA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

Don haka, bai kamata a rika nunawa kasashe fin karfi kan harkokinsu na gida ba, ko kuma a rika nuna musu an fi su sanin abun da ya fi dacewa da su ba.

Kamar yadda Zhang Jun ya bayyana yayin taron, dole ne a samu bambancin ra’ayi daga kasa da kasa kan batutuwan tsaro, amma ya kamata a samu daidaito ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa.

Shirin tsaron duniya da shugaban kasar Sin ya gabatar ga taron BOAO a watan Afrilu, ya gabatar da wata alkibla ta cimma tsaro na bai daya tare da warware matsaloli masu masu ruwa da tsaki.

An riga an san kasar Sin ba mai kaunar rikici ba ce, domin an ji, kuma an ga yadda al’ummominta da suka kunshi kabilu daban daban ke rayuwa cikin jituwa da zaman lafiya, don haka duk wani shiri da za ta gabatar don gane da hakan, a ganina abu ne da ya kamata a karba da hannu bibbiyu, tun da burinta shi ne, gina duniya mai kyakkaywar makoma cike da tsaro da kwanciyar hankali.

Akwai bukatar sauran kasashen duniya su mara mata baya, kuma su ma su yunkura, su hada karfi da karfi wajen ganin an samu ci gaban duniya da kwanciyar hankali, ta hanyar hakuri da girmama juna da tabbatar da adalci. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow
Daga Birnin Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Mutane 6 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Ondo

Mutane 6 Sun Mutu A Hatsarin Mota A Ondo

LABARAI MASU NASABA

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.