ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnati Ta Kashe Naira Tiriliyan 9.39 Wajen Ƙarin Albashi Da Alawus-alawus — Oyedele

by Sadiq
3 weeks ago

Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira tiriliyan 9.39 wajen ƙarin albashi, ƙara mafi ƙarancin albashi da kuma biyan alawus-alawus ɗin ma’aikatan gwamnati tsakanin Yunin 2023 zuwa Disamban 2025.

Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arziƙin ƙasa, Taiwo Oyedele ne, ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja.

Ya ce kuɗaɗen da ake kashewa kan albashi sun ƙaru ne bayan gwamnatin ta ƙara mafi ƙarancin albashin ƙasa daga Naira 30,000 zuwa Naira 70,000 a shekarar 2024.

ADVERTISEMENT

Oyedele ya ce sauye-sauyen da gwamnati ta yi, ciki har da cire tallafin man fetur da sauya tsarin musayar kuɗin waje, sun samar da Naira tiriliyan 15.8 ga tarayya a wannan lokacin.

Daga cikin kuɗin, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira tiriliyan 5.4, yayin da aka raba Naira tiriliyan 10.4 ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Ya ce jimillar ƙarin kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ta samu a wannan lokacin, ciki har da kuɗaɗen sauye-sauye, ƙarin kuɗin shiga da sabbin bashi, sun kai Naira tiriliyan 20.4.

Sai dai ƙarin kuɗin da ta kashe ya kai Naira tiriliyan 30.64.

Baya ga albashi, gwamnati ta kashe Naira tiriliyan 9.37 wajen biyan bashin ƙasashen waje, sannan ta kashe Naira tiriliyan 6.5 kan manyan ayyukan more rayuwa.

Oyedele ya amince cewa sauye-sauyen sun ƙara wa ‘yan Nijeriya matsi, amma ya ce gwamnati ta ɗauki matakai domin rage wa jama’a raɗaɗin matsalar.

Ya ce: “Waɗannan matakai sun zo da tsadar gaske.”

MASU ALAKA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci
Manyan Labarai

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
An Yi Jigilar Ton Biliyan 2.35 Na Kayayyaki Ta Jiragen Kasan Sin A Watanni 7 Na Farkon Bana

An Yi Jigilar Ton Biliyan 2.35 Na Kayayyaki Ta Jiragen Kasan Sin A Watanni 7 Na Farkon Bana

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.