ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyi 5 Da Za Ki Magance Zubewar Gashin Kai

by Bilkisu Tijjani and Sulaiman
7 months ago
Gashi

Sau da dama mata kan samu kansu cikin shiga ukun zubewar gashi, wanda yawancin hakan na faruwa ne a garin neman a gyara gashin kai, sai kuma a Bata, karshe gashin kai ya zube. Don haka ne na taho miki da hanyoyi biyar da idan kin bi kowacce daga ciki za ta magance miki zubewar gashin kanki, ta kuma kara wa gashin kanki tsawo da kyau da kuma sheki.

1. Amfani da mayukan gashin kai: Ki samu daya daga cikin man gashin kai kamar su, Man Olibe oil da man Kwakwa da Canola oil da sauransu. Daga nan sai ki zuba daya daga cikin man da na lissafa a sama a cikin tukunya, sannan ki dora a kan wuta. Ki bar shi ya yi zafi, amma ba wai sosai ko ya tafasa ba.

Bayan nan sai ki sauke daga kan wuta, sannan ki shafa a gashin kanki. Yana da kyau ki shafa a kofofin gashin kanki, hakan zai taimaka wajen sanya gashin kanki ya yi tsawo da kuma sheki. Idan kin shafa sai ki rika amfani da hannuwanki wajen goggogawa da dan karfi-karfi. Bayan nan sai ki sanya hular ‘shower cap’ har zuwa awa daya. Daga nan sai ki shafa man shampoo ki wanke kan.

ADVERTISEMENT

2. Amfanin da Jus din Citta ko Tafarnuwa ko Albasa: Ki samu albasa ko citta ko tafarnuwa, sannan ki markada daya daga cikinsu har ta zama kamar Jus. Daga nan sai ki shafa a gashin kanki. Yana da kyau idan kika shafa ki kwana da shi. Da safe sai ki wanke sosai. Yin hakan zai magance miki zubewar gashin kai.

3.Tausa a kai da kuma gashin kai: Idan kina tausar gashin kanki lokaci zuwa lokaci ya kan samar da gudanar jini cikin sauki a kofofin gashin kanki. Masana kiwon lafiya sun ce idan har jini na gudana yadda ya kamata a kofofin gashin kai, to hakan zai sanya gashin kai ya kara tsawo. Shafa man essential oil kamar su Labender da bay essential oil da almond da kuma sesame a lokacin da za a yi tausar kai ko gashin kai yana sanya gashin kai ya kara tsawo da kyau da kuma sheki.

LABARAI MASU NASABA

Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi

Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

4. Amfani da abin da yake kashe kwayoyin cuta: Idan kina shafa abin da yake kashe kwayoyin cuta a gashin kanki zai hana shi zubewa. Misali ki samu kwalin ko ledar ganyen shayin ‘Green tea’ biyu, sai ki jika su a cikin kofi daya da ruwan zafi. Bayan ya huce, sai ki shafa a gashin kanki. Idan kin yi hakan za ki bar shi har zuwa awa daya, daga nan sai ki wanke. Ganyen shayin green tea yana dauke da sinadaran da ke hana zubewar gashi, a lokaci guda yana kara yawan gashin kai.

5. Ki rika samun hutu: Masana kiwon lafiya sun tabbatar da aikin wahala, rashin kwanciyar hankali hade da gajiya na haifar da zubewar gashi. Don haka idan ba kya so gashin kanki ya zube sai ki rika hutawa, a lokaci guda ki guje wa aikin wahala.

Gashi
Bilkisu Tijjani
+ posts Bio
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Tuwon Alkama Da Miyar Taushe
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Chicken Teriyaki Rice
  • Bilkisu Tijjani
    https://hausa.leadership.ng/author/bilkisu-tijjani/
    Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa
Gashi
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi
Ado Da Kwalliya

Yadda Ake Kula Da Labba Domin Su Kasance Masu Laushi

September 5, 2026
Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa
Ado Da Kwalliya

Yadda Ake Kare Hannu Daga Bushewa

August 29, 2026
Gashi
Ado Da Kwalliya

Yadda Ake Kula Da Farce

August 23, 2026
Next Post
Illar Kari (Fibroid) Da Kuma Maganinsa

Ko Kin San... Dalilan Kamuwa Da Karin Mahaifa (Fibroid) (1)

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.