Jakadan kasar Sin a Nijeriya, Yu Dunhai, ya gana da ministan kula da makamashi na kasar kuma darakta janar mai kula da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da ke tsakanin Sin da Nijeriya.
Jakada Yu ya ce a matsayinsa na bangare mai matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasa da rayuwar jama’a, bangaren makamashi wani muhimmin ginshiki ne na tattalin arzikin kasa kuma wanda ake ba fifiko a hadin gwiwar Sin da Nijeriya.
Ya kara da cewa, a shirye Sin take ta karfafa daidaita tsare-tsarenta da Nijeriya da zurfafa hadin gwiwa a bangaren kayayyakin samar da makamashi da makamashi mai tsafta da sauran bangarori, da cin gajiyar manufar soke haraji yadda ya kamata da kuma ci gaba da daukaka dangantakar Sin da Nijeriya zuwa sabon matsayi.
Joseph Tegbe ya ce Nijeriya na daukar batun raya dangantakar abota tsakaninta da Sin da muhimmanci. Ya kuma yaba wa taimakon da Sin ta dade tana ba Nijeriya a kokarinta na zamanatar da kanta da bunkasa masana’antu a bangarorin da suka hada da na lantarki. Ya kara da cewa, a shirye Nijeriya take ta zurfafa hadin gwiwa na zahiri da Sin a dukkan bangarori da bunkasa abotarsu da samar da moriya ga kasashen biyu da al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha)














