Wata Kotun Majistare da ke Kano ta bayar da umarnin a tsare wani mutum, Muhammad Najib Rimin Kebe, a gidan gyaran hali bisa zargin satar takalma a wani masallaci da ke cikin harabar Kotunan Norman’s Land a jihar.
’Yansanda sun gurfanar da shi a gaban kotun bisa zargin kutse da kuma satar takalma a masallacin.
Mai shari’a Dayyabu Jamilu Hamza ne, ya jagoranci zaman kotun, inda aka karanta wa wanda ake zargin tuhume-tuhumen da ake masa.
Bayan karanta tuhume-tuhumen, kotun ta bayar da umarnin a tsare shi, sannan ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Agusta, 2026.
Ana zargin mutumin da yawan zuwa masallacin tare da satar takalman masu ibada.
Wasu daga cikin masu sallah a masallacin, ciki har da ma’aikatan kotu, ’yansanda da jami’an gidan gyaran hali, sun ce an daɗe ana satar takalma a masallacin.














