ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

by Leadership Hausa
3 months ago
Nijeriya

Shekaru aru-aru, inji Bahaushe, yara a kasar na gudanar da shagulgulan binkin zagayowar ranarsu ta duniya, musamman a cikin walwala da annashawa.

An dai gudanar da bikin zagayowar ranar ce, a duk ranar 27, na kowanne watan Mayu na shekara, tare da fatan samun makomar gobe mai kyau, yaran manyan gobe.

Sai dai, abin takaicin, bisa lamuran da ke bijirowa, a duniya ta yau, za a iya ce, wannan burin na yaran, da kamar wuya.

ADVERTISEMENT

Su ma yara a Nijeriya, ba a bar su a baya, wajen murnar bikin zagoyowar ranar ba, wadda 2026, aka yi mata take da, “ Moma ayau: Janyo Yaran Kasar Nan A Jiki Domin Inganta Makomarsu,”.

Abin bakin cikin a nan shi ne, miliyoyin yara a kasar nan fatan inganta samar masu makomar ta gari, na ci gaba da zama rashin tabbas, musamman duba da yadda suke ci gaba da zama, a cikin tsabagen yunwa, fargaba, cin zarafinsu, nuna masu wariya, zama a cikin duhun jahilci, fusknatar tashin hankula, yin watsi da rayuwarsu.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

A saboda wadannan jerin kalubalen da muka jero, muke ganin, har yanzu, akwai sauran Rina a Kaba, a makomar yara, a Nijeriya.

Kazalika, har yanzu, kasar, ba ta daura damarar samar da kyakywan yanayi, ga makomar yaran kasar, da kuma sauran yaran da ke tafe, a nan gaba ba.

A yayin da jami’an gwamnati ke tunkahon cewa, an samar da shirye-shiryen janyo yaran a jiki, amma a bayan fage, alkaluma na nuna yadda rayuwar yaran, ke ci gaba da fusknatar, dimbin matsaloli.

Bisa yawan yaran da ake da su, a fadin duniya, yara a Nijeriya, su ne, mafi koma baya, da rayuwarsu, ke ci gaba da zamowa, a cikin hatsari.

Karin wata matsalar ita ce, yadda fannin ilimin Bokon kasar, ke ci gaba da tabarbarewa, musamman duba da cewa, an kiyasa, yara miliyan 18.3 ne, suka daina zuwa makaranta, inda wannan adadin, ya rubanya  na fadin duniya.

Hakan na nuna cewa, a duk cikin yara biyar, yaro daya, bai zuwa makaranta.

Daga cikin wannan adadin, kimanin yara, kaso 66 da suka daina zuwa makaranta na a yankunun Arewa Maso Gabas da kuma Arewa Maso Yamma, da kalubalen rashin tsaro, ke ci gaba da ta’azzara,  musamman na ayyukan ‘yan bindiga, ‘yan fashin daji da kuma yadda hare-hare, ya tarwatsu, daga matsugunansu.

Haka zalika, saboda kalubalen rashin tsaro, an rufe makarantu da dama, tare da kai hare-hare, tare da mayar da Azuwa, Fagan fama.

Fannin na ilimin, ya kara tagaiyara, bayan sace dalibai mata, sama da 1,700, ‘yan makarantar Chibok a 2014, inda hakan ya nuna, babbar koma baya, ga ci gaban rayuwar yara.

Misali, a ranar 15 na watan Mayun 2026, wasu ‘yan bindiga, suka kutsa wasu makarantun Firamare da Sakandare da ke a yankin Esiele da Yawota a karamar hukumar Oriire a jihar Oyo, suka sace dalibai da malamai.

Miliyoyin yara a kasar, na fuskantar kalubalen rashin abinci mai gina jiki, inda kuma kimain miliyan 11, ke ci gaba da fuskantar  matsananciyar yunwa, musamman yadda yara kaso 32, ‘yan kasa da shekaru biyar, suma ke ci gaba da fuskantar matsalar.

A gafe daya kuma, ba a tanadi wani kyajyawan tasri, a fannin kiwon lafiya ba, wanda hakan, ke ci gaba da janyo, mutuwar yaran, musamman duba da yadda, a duk haiwa daya, ake samun yara daga 115 zuwa 128 ke rasuwa, kafin cikarsu bikin ranar haihuwarsu.

Yaran na kuma mutuwa saboda cizon Sauro da kwalara da Amai da gudawa, wadanda za a iya magancewa, a cikin gaggawa.

Kimain alumomi sama da miliyan 3.7, ciki har da yara, da mata a daukacin fadin kasar, ke gudun hijira, inda adadin yaran, ya kai kaso 70.

Wannan matsalar ta shafi neman iliminsu da rashin samun kulawar lafiyarsu da kuma rashin samun abinci mai gina jiki.

Kazalika, akwai kuma yaran da ake tilastawa yin ayyukan bauta, duba da alkaluman da Hukumar Kiddidiga ta kasa ta fitar, sun nuna yaran  da ke yin aikin bautar sun  kai kimanin, miliyan  24.67.

Irin wadannan yara, shekarun na faraway ne, daga biyar zuwa 17, inda sama da miliyan 14, ake tilasta su yin aikin bauta, masu hatsari, wanda hakan, ke shafar lafiyarsu da kuma tunaninsu

Matsain tattalin arzki da iyayen irin wadannan yaran ke fama da shi, hakan ya sanya, suna tura ‘ya’yansu, yin tallace-tallace, hakar ma’adanai, ta haramtacciyar hanya.

Ya zama wajibi a kasar, bkin zagowar ranar, ta wuce batun gabatar da kasidu, amma a dauki kwararan matakai, domin intanta rayuwar yaran

Dole ne kuma, matakan gwamnati uku na kasar, su tabbatar da sun wanzar da dokar, bai wa yara ‘yancinsu, da kuma karfafa dokar kare cin zarafinsu da yiwa ‘ya’ya mata auren wure da safarar yara da kuma sanya su, yin aikin bauta.

Bugu da kari, ya zama wajibi, hukumomin tsaro da bangaren Shari’a, su tabbatar da ana hukunta duk wanda aka samu, da cin zarafin yaran.

Haka zalika, ya zama wajbi, gwamnati ta ayyana dokar ta baci, a fannin ilimi, musamman, a yankunan da rashin tsaro, ya daidaita tare da sake gina makarantun da hare-haren ‘yan ta’adda, suka lalata.

Dole ne, kuma a farfado da cibiyoyin kiwon lafiya da ke a karkara tare da mayar da hankali wajen samar da shirye-shiryen samar da abinci mai gina jiki, musamman ga masu juna biyu da kananan yara.

Dole ne, taken taron bikin na bana, ya zama a aikace, wajen samar da tsaro a makarantu da samar da ingantattun kayan duba lafiya da samar da abinci mai gina jiki da samar da ingantacce kuma tsaftattacen ruwa sha da dakile yawan, aukuwar tashe-tashen hankula, a cikin alumomin kasar.

Nijeriya
Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja
  • Leadership Hausa
    Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
  • Leadership Hausa
    Batun Dawo Da Tallafin Mai Da Atiku Ya Yi Na Ci Gaba Da Tayar Da Kura
  • Leadership Hausa
    Batun Guguwar Kakar Yakin Neman Zabukan 2027 A Nijeriya

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Hajji 2026: Mahajjata 1,905 Sun Dawo Nijeriya Daga Saudiyya

Hajji 2026: Mahajjata 1,905 Sun Dawo Nijeriya Daga Saudiyya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.