ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 25, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?

by Yusuf Shuaibu
1 month ago
INEC

A lokacin da zaben fitar da gwani na jam’iyyun siyasa da ya kare a ranar 30 ga Mayu, jam’iyyun adawa hudu da suka hada da ADC da PDP da LP da kuma SDP sun mika sunaye fiye da daya na dan takarar shugaban kasa ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC).

A yayin da ADC ta mika sunayen ‘yan takarar uku ga hukumar zabe, PDP, LP da SDP sun mika biyu kowannasu bisa ga samun rabuwar kai na jam’iyyun. Ko da yake INEC ba ta shaida wasu zaben fid da gwanin ba, mafi yawancin bangarorin na jam’iyyun adawa sun sanar da niyyarsu na shirya zaben ga INEC.

Ko da yake hukumar zabe tana da lokaci har zuwa 29 ga Agusta, 2026, don wallafa sunayen karshe na ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun siyasa bisa ga ka’idojinta, mutane da yawa sun yi ikirarin cewa bai kamata hukumar zabe ta bar bangarorin jam’iyyu su gudanar da zabukan fitar da gwani ba, hukumar zabe tana da hannu wajen kawo rashin daidaito a jam’iyyun.

ADVERTISEMENT

Sun yi ikirarin cewa duk da cewa jam’iyyun siyasa suna da hannu a cikin lamarin wajen shin bin ka’idoji da bin tsarinsu na cikin gida don warware rikice-rikicensu, rashin kulawar INEC ko rashin shiga tsakani cikin hukunci a matsayin mai tsara harkokin jam’iyyun siyasa ya sanya ta samu laifi wajen nuna son kai.

Bisa ka’ida, an sanya tsarin zabe a karkashin kulawa ta musamman, yayin da jam’iyyun adawa ke tambayar gaskiyar lamarin, wadanda ke ganin cewa ci gaba da rikice-rikicen shari’a, yanke hukuncin gudanarwa, da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyya ana amfani da su ne don kara raunana ‘yan takara.

LABARAI MASU NASABA

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

A baya an zargi hukumar zabe da taka rawa a cikin rigingimun cikin gida na jam’iyyu, musamman a cikin jam’iyyar LP. Ana ganin cewa matsayin siyasa na tsohon gwamnan Jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa na LP a 2023, Mista Peter Obi, wanda masu sharhi da dama ke ganin babban kalubale ne ga APC mai mulki, yana ci gaba da kasancewa a tsakiyar wannan rikici.

Jiga-jigan ‘yan adawa suna zargin cewa hukumomin gwamnati, ciki har da INEC da wasu bangarorin shari’a, ana amfani da su ne don raunana jam’iyyun adawa, musamman kin amincewar da INEC ta yi na kwamitin rikon kwarya na LP karkashin jagorancin Nenadi Usman ya zama babbar matsala a rikicin jam’iyyar.

Masu suka sun lura cewa hukumar zabe ta ki yin biyayya ga hukuncin kotun koli na wasu watanni bayan zartar da hukunci, jinkirin da ya kara haifar da zarge-zargen kin bin hukuncin.

Rigimar ta kara tsananta bayan Obi ya yi murabus daga jam’iyyar LP a ranar 31 ga Disamba, 2025. Cikin mako guda bayan ficewarsa, INEC ta sanar da bin hukuncin watan Afrilu don kare matsayinta, wanda hakan ya sa ‘yan adawa suka yi jayayya cewa rikicin bai ta’allaka ne kawai ga bin ka’idoji ba har ma ya shafi muhimmancin siyasa na Obi.

Don haka, a koda yaushe rikicin jam’iyyun siyasa yana haifar da shakku game da ‘yancin ‘yan adawa, musamman a yanzu da ake fuskantar zaben 2027.

Masu nazari da dama sun ci gaba da jaddada rashin daidaito da ake ganin yana cikin INEC, ciki har da shirinta na yin aiki kan hukuncin babbar kotun tarayya a wasu lokuta yayin da take dagewa kan hukuncin kotun koli. Sun ce irin wadannan matakan suna karfafa rudani na cewa yanke hukuncin hukumar yana da tasiri ne ta hanyar matsin lamba na siyasa da ake samu a lokuta da dama.

Irin wannan zargi ya bi fassarar hukumar da wani yanayi ba, wanda suka dogara da shi don janyewa shugabancin ADC karkashin jagorancin Sanata Dabid Mark. Wannan hukunci ya haifar da gibin shugabanci kuma ya bayyana son zuciyar hukumar ga jam’iyyun adawa.

Haka kuma, duk da hukuncin kotun koli da ya yi watsi da daukaka kara na PDP karkashin jagorancin Nyesom Wike, hukumar ta yi shiru yayin da rikici ke ci gaba da raba jam’iyyar.

Duk da haka, INEC ta rika musanta zarge-zargen nuna son kai, tana jaddada cewa ayyukanta suna bin doka da kuma hukuncin kotu ne akwai.

A watan Maris da ya gabata, Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa rikice-rikicen shugabanci a cikin jam’iyyun suna tasiri kan tsare-tsaren zaben 2027.

Duk da musantawa, wanda ya lashe zaben fid da gwani na shugaban kasa na jam’iyyar ADC, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a jawabinsa nasamun nasara, ya dora laifin rikicin shugabanci a cikin jam’iyyun adawa kan jam’iyyar APC da INEC da wasu abubuwa a cikin bangaren shari’a.

Tsohon mamba na majalisar wakilai kuma jigo a jam’iyyar PRP, Usman Bugaje ya bayyana cewa gwamnati tana aiki tare da INEC don lalata jam’iyyun adawa.

Haka zalika, masanin shari’a kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Dakta Sam Amadi, ya ce tsarin zabe da cibiyoyin shari’a sun zama manyan abubuwan da ke haifar da karuwar rashin kwanciyar hankali a cikin jam’iyyun siyasa, yana mai jayayya cewa hukunce-hukuncen da ba su dace ba, da kuma yanke hukunci masu rikitarwa suna ta’azzara rikice-rikicen cikin gida da raunana hadin kan jam’iyya a fadin nan.

Tsohon shugaban hadakar cibiyar jam’iyyun siyasa (IPAC), Cif Peter Ameh, ya yi kira ga INEC da ta magance abin da ya bayyana a matsayin matsalar rashin gaskiya. Ya kara da cewa rashin amincewa da ya samo asali daga yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa na 2023 bai samu gyara ba.

Ita ma gidauniyar kare hakkin muhalli da ci gabansa (FENRAD) ta yi gargadin cewa wannan lamari na iya raunana dimokuradiyyar Nijeriya gabanin zaben 2027.

Haka kuma, gamayyar kungiyoyin fararen hula karkashin cibiyar ‘Network of Cibil Society Groups’ sun bukaci INEC ta daina yarda ana amfani da ita a matsayin makamin siyasa a yayin da rikicin shugabanci ke ci gaba da gudana a jam’iyyar ADC. Shugaban kungiyar, Kwamared Yaya Ademola, ya zargi cewa ana amfani da INEC domin cire sahihin shugabancin ADC bisa dalilin hukuncin kotu.

Kungiyar ta yi gargadin cewa idan rikicin ya ci gaba, zai iya raunana jam’iyyun adawa, ta yadda zai bude hanya ga Shugaba kasa, Bola Tinubu don samun zangon mulki na biyu a zaben 2027.

Bisa yadda ake samun karuwar damuwa game da shigar INEC cikin rikice-rikicen jam’iyyun siyasa, hukumar na bukatar tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa zaben 2027 zai kasance cikin adalci.

INEC
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027

MASU ALAKA

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa
Tambarin Dimokuradiyya

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

July 24, 2026
Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya
Tambarin Dimokuradiyya

Tinubu Da Atiku Da Obi Na Ci Gaba Da Zafafa Neman Kuri’un Arewacin Nijeriya

July 17, 2026
Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura
Tambarin Dimokuradiyya

Zaben 2027:Tikitin Muslim-muslim Na Jam’iyyar APC Ya Sake Tayar Da Kura

July 17, 2026
Next Post
2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

LABARAI MASU NASABA

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

An Karrama Masana Ilimin Lissafi Na Kasar Sin Da Lambobin Yabo Na Fields Medal

July 24, 2026
Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

Ta Da Zaune Tsaye Da Philippines Ta Yi A Teku Ba Zai Lalata Dangantakar Hadin Gwiwar Sin Da ASEAN Ba

July 24, 2026
Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

Jadawalin INEC:Kotun Daukaka Kara Ta Kassara Fatan Jam’iyyu Da ‘Yan Siyasa

July 24, 2026
An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

An Zartas Da Sanarwar Chengdu A Taron Ministocin Kungiyar APEC Kan Harkar Raya Fasahohin Dijital Da AI

July 24, 2026
NNPP Za Ta Kwace Mulki A Jihar Imo – Kwankwaso

Jam’iyyar NDC Ta Shirya Tsaf Domin Kafa Gwamnati A 2027 —Kwankwaso

July 24, 2026
Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

Sin Ta Kara Kamfanoni 14 Na Tarayyar Turai Cikin Jerin Wadanda Aka Hana Fitar Masu Da Kaya

July 24, 2026
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Kyamar Baki: Shettima Ya Ja Kunnen Gwamnatin Afirka Ta Kudu

July 24, 2026
Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

Yadda Kasar Sin Ta Samar Da Ci Gaba Na Bai Daya

July 24, 2026
Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

Hatsin Da Kasar Sin Ta Girbe Da Lokacin Zafin Bana Ya Zarce Tan Miliyan 150

July 24, 2026
Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

Wani Dalilin Da Ya Sa Al’Ummar Afirka Ke Kaunar Kasar Sin Shi Ne Yadda Take Kokarin Zuba Musu Jari

July 24, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.