ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Kallo Ya Koma Kan Yadda APC, ADC Da PDP Ke Neman Abokan Takarar Mataimakin Shugaban Kasa

by Yusuf Shuaibu
3 months ago
APC

Bayan kammala zaben fid da gwani don tantance ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2027, jam’iyyun siyasa sun mayar da hankali kan zabar abokan takarar shugaban kasa.

Rahotanni sun nuna cewa wasu jam’iyyun suna fuskantar kalubale wajen yanke hukunci. Duk da cewa suna da lokaci har zuwa ranar 27 ga Yuni don saka cikakkun bayanan ‘yan takarar shugaban kasa da abokan takararsu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), masu ruwa da tsaki suna jin matsin lamba don kammala zabukansu.

An ruwaito cewa jam’iyyar masu mulki ta APC, na kan gaba wajen fuskantar wadannan matsaloli. Majiyoyi sun nuna cewa batutuwan da ba a warware ba da suka shafi zaben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima har yanzu ana tattaunawa a kansu. Duk da cewa cikakken bayani game da wadannan batutuwan yana ga Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ba a kai ga kai karshensu ba, inda sunaye daban-daban ke bayyana a matsayin masu yiwuwar maye gurbinsa. Wani muhimmin bangare na tsarin zaben shi ne, bukatar daidaito na addini. Wannan ya kawo sunaye irin su tsohon shugaban majalisar wakilai, Hon. Yakubu Dogara, da ministan tsaro, Janar Christopher Musa. Duk da haka, masu goyon bayan ci gaba da tikitin Musulmi-Musulmi suna ikirarin cewa tasirin cire Shettima za a iya rage shi ta hanyar zabar wani kamar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa, Malam Nuhu Ribadu, wanda ya fito daga Adamawa a arewa maso gabas, yanki daya da Shettima.

ADVERTISEMENT

A halin yanzu, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, shi ma yana fama da matsalar zaben mataimakin takara. Sunayen da ake duba sun hada da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai, Hon. Emeka Ihedioha.

Sai dai kuma majiyoyi na nuna cewa tattaunawa har yanzu na ci gaba, kuma an yi hasashen cewa Amaechi na iya kin karbar damar zama mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar a zaben 2027. Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan Jihar Ribas na jiran tayin a hukumance daga jam’iyyar.

LABARAI MASU NASABA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

Wata majiya me tushe da ke kusa da ADC ta ce jam’iyyar na kokarin zaben mataimaki dan takarar shugaban ne a hankali kuma tana da niyyar kammala tattaunawa kafin wa’adin INEC. “Ana ci gaba da aiwatar da tsarin jam’iyyar. Muna kokarin yin hakan cikin hikima,” in ji majiyar.

Wata majiya da ta musanta zargin cewa Amaechi zai iya kin karbar tayin, ta bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Ribas na jiran a gabatar da tayin hukumance ne. Majiyar ta kara bayyana cewa tattaunawa na ci gaba a matakin jam’iyya da na ‘yan takara. Suna gudanar da tattaunawa, kuma da zarar sun cimma matsaya, za a sanar.

Haka kuma, wata majiya ta nuna cewa Atiku a baya ya yi la’akari da zabar abokin takara daga yankin kudu maso yamma na kasar nan.  Majiyar ta ce tattaunawar ta ci gaba, inda ake tsammanin cewa Atiku zai zabi abokin takararsa daga kudu maso yamma.

Daga cikin manyan jam’iyyun siyasa guda uku a fafatawar zaben shugaban kasa na 2027, APC da ADC da NDC, jam’iyyar NDC ne kadai ta warware batun abokin takarar shugaban kasa. Dan takararta, Mista Peter Obi, ya sanar cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai kasance abokin takararsa. Sauran jam’iyyun, ciki har da APC mai mulki da ADC mai hamayya, har yanzu suna cikin tattaunawa mai zurfi don tantance wadanda za su iya kasancewa mafi inganci a matsayin abokan takararsu.

Bangarori biyu na jam’iyyar PDP, wadanda suka zabi tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da Sanata Sandy Onor, a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimaki na ci gaba da kasancewa cikin rashin tabas. Haka kuma, dan takarar jam’iyyar AP, Gbenga Olawepo-Hashim, bai sanar da mataimakinsa ba. Ita ma jam’iyyar SDP na fuskantar irin wannan lamari, wadda a halin yanzu ke da ‘yan takarar shugaban kasa na bangarori.

APC
Yusuf Shuaibu
+ postsBio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa

MASU ALAKA

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
Tambarin Dimokuradiyya

2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe

September 5, 2026
Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
Tambarin Dimokuradiyya

Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta

September 4, 2026
Ko INEC Na Da Hannu A Rikice-rikicen Jam’iyyun Siyasa A Nijeriya?
Tambarin Dimokuradiyya

INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027

August 28, 2026
Next Post
Manufar Soke Haraji Ga Kasashen Afirka Ta Sin Ta Samar Da Sabbin Damammaki Ga Nahiyar

Manufar Soke Haraji Ga Kasashen Afirka Ta Sin Ta Samar Da Sabbin Damammaki Ga Nahiyar

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.