• English
  • Business News
Friday, May 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Kun San Filin Kokowar Da Ke Kara Kyautata Zumuncin Sin Da Afirka?

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Kasar Sin
0
Ko Kun San Filin Kokowar Da Ke Kara Kyautata Zumuncin Sin Da Afirka?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A kasar Senegal dake yammacin nahiyar Afirka, wasan kokowa na samun karbuwa sosai, ko manyan jami’an gwamnati, ko kuma fararen hula, kowa da kowa na matukar sha’awar wasan kokowa mai dadadden tarihi a kasar.

Amma a cikin dogon lokaci, al’ummar kasar ba su samu filin kokowar ko daya ba. Lokaci ya zo ranar 22 ga watan Yulin shekara ta 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Senegal, Macky Sall, sun halarci bikin mika babban filin wasan kokowa na Senegal, wanda kamfanin kasar Sin ya taimaka wajen gina shi.

  • Sakon Xi Ya Karfafa Gwiwar Matasan Afrika Wajen Raya Huldar Sin Da Afrika

Irin wannan filin, ba kawai ya taimakawa al’ummar Senegal cimma burinsu na dogon lokaci ba, har ma ya zama abun shaida na dadadden zumunci tsakanin Sin da Afirka, da aikin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin bangarorin biyu.

A yankin karkara na Dakar, fadar mulkin kasar Senegal, akwai wani babban filin wasan motsa jiki dake jawo hankalin jama’a sosai, wanda kamfanin gine-gine na Hunan na kasar Sin wato HCEG ya gina shi cikin shekaru biyu. Filin wasan, mai fadin murabba’in mita dubu 18, zai iya daukar masu kallo kimanin dubu 20, wanda kuma shi ne filin wasan kokowa na zamani na farko a nahiyar Afirka, kana, aiki mafi girma da kasar Sin ta gudanar don tallafawa Senegal.

A ranar 22 ga watan Yulin shekara ta 2018, yayin da yake ziyarar aiki a Senegal, shugaba Xi Jinping ya halarci bikin mika wannan filin wasan kokawa ga Senegal, inda ya yi jawabi cewa, filin wasan kokawar ya shaida zumunci mai zurfi tsakanin al’ummomin Sin da Senegal. Senegal kasa ce mai dimbin al’adu, kuma kasar Sin tana fatan yin kokari tare da Senegal don kara karewa gami da raya al’adun gargajiya, ta yadda za’a fadada hadin-gwiwar kasashen biyu a fannin al’adu.

Labarai Masu Nasaba

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

Sin
•Wani bangare na babban filin wasan kokowa dake Dakar

Ma’aikatan gine-ginen kasashen Sin da Senegal sun fuskanci kalubaloli da dama a yayin da suke gudanar da aikin gina filin mai girma, ciki har da mabambantan al’adu da yare tsakaninsu. Haka kuma, kafin fara aikin, wannan wuri fadama ce, inda aka bukaci a sake gyara shi. Musamman a watan Yuli zuwa Oktoba, wato lokacin damina a Senegal, ruwan sama yana kawo tsaiko ga aikin gine-ginen. Amma ma’aikatan dukkan kasashen biyu ba su yi kasa a gwiwa ba, har sun haye wahalhalu daban-daban, da kulla zumunci mai zurfi tsakaninsu.

Ganin yadda kamfanin kasar Sin ya yi nasarar gina filin mai inganci kuma cikin lokaci, ministan wasannin motsa jiki na kasar Senegal, Matar BA ya yaba da cewa: “Na godewa ma’aikatan gine-gine na kasar Sin saboda jajircewarsu, inda suka yi nasarar kammala aikin tare da mika mana cikin lokaci. A ganina, wannan ya zama tamkar abun koyi ga aikin raya tattalin arzikinmu.”

Sinawa kan ce, da ka baiwa wani kifi, gara ka ba shi fasahar kamun kifin, kuma irin wannan ra’ayi ya riga ya zama babban jigo na gudanar da aikin tallafawa Afirka da hadin-gwiwar Sin da Afirka. A lokacin da kasar Sin ke samar da taimakon gina filin wasan kokawa a Senegal, ma’aikatan gine-gine na Sin sun yi kokarin horas da ma’aikatan wurin. A nasa bangaren, shugaban rukunin kula da fasahohi na aikin gina filin wasan kokawa a Senegal, Wu Guangbin ya bayyana cewa: “Akwai ma’aikatan gine-gine na Senegal da dama da suka koyi fasahohi da dama daga wannan aiki, inda kuma suka kara fahimtar ka’idojin aiki na kasar Sin. Da suka gama aikin, akwai sauran wasu kamfanonin kasar Sin gami da na sauran kasashe da suka samar musu guraben ayyukan yi daban-daban. Ke nan ta hanyar aiki tare da mu, sun kara samun kwarewa a fannin gine-gine.”

Sin
•Yadda ake gudanar da gasar wasan kokowa a wannan babban fili

Malick Diaby, dan Senegal ne da ya halarci aikin ginin babban filin wasan kokawa a Dakar. Ya ce yana matukar alfahari da samun wannan dama, inda ya ce: “Ina farin ciki sosai don samun damar shiga aikin gina wannan filin wasan. Nan gaba, babu shakka zan gayawa ’ya’yana cewa, ni da abokan aiki mun taba shiga cikin wannan gagarumin aiki, tabbas zan gaya wa ’ya’yana.”

A yayin da yake aikin gine-gine a Senegal, kamfanin HCEG daga lardin Hunan na kasar Sin ya yi kokarin sauke nauyin dake wuyansa, don taimakawa rayuwar mazauna wurin, ciki har da samar da agajin kayan masarufi da tallafin kudi ga iyalan da suke fama da talauci, da bada taimakon sake gyara magudanar ruwa a unguwanni daban-daban, da gina filayen wasan kwallon kafa a makarantu da sauransu, al’amarin da ya sa kamfanin kasar Sin wato HCEG ya samu babban yabo da amincewa daga jama’ar Senegal.

Tun daga shekara ta 2018, ya zuwa yanzu, an riga an shirya wasannin kokawa sama da 100 a babban filin wasan kokawa dake birnin Dakar na Senegal, al’amarin da ba cika burin ’yan wasan kasar kawai ya yi ba, har ma yana taimakawa sosai da sosai wajen kara kiyayewa da raya al’adun gargajiyar dake tattare da wasan kokawa a Senegal. Wani dan wasan kokawa a kasar, Galass, ya bayyana cewa: “A baya, mun shirya wasannin kokawa a filin wasan kwallon kafa, amma yanzu muna matukar farin-cikin samun irin wannan babban filin wasan kokawa, wanda shi ne kyauta mai daraja gare mu, musamman matasa ’yan wasan. Kana, ya kara ba mu kuzari da karfafa mana gwiwar ci gaba da gudanar da wasan kokowa.”

Sin
•Babban filin wasan kokowa da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa a Dakar

A farkon watan Nuwambar shekara ta 2021, an yi gasar wasannin kokawa karo na 9 na kasashen ECOWAS a filin wasan kokawa dake birnin Dakar na Senegal, inda wani dan wasan daga kasar Guinea Bissau ya bayyana cewa, filin wasan nan ya burge shi sosai, kuma wannan shi ne karon farko da ya ga irin wannan filin mai girma da zamani haka, ya ce yanzu ya fahimci dalilin da ya sa ’yan wasan kokawan kasar Senegal suka kware a wasan.

Yanzu, babban filin wasan kokawa dake Dakar na Senegal, ya riga ya zama wani shahararren ginin dake alamtar dankon zumunci tsakanin Sin da Senegal, haka kuma akwai sauran wasu ayyukan hadin-gwiwa tsakanin kasashen biyu da suka kara samar da alfanu ga al’ummar Senegal, ciki har da babban dakin wasannin kwaikwayo, da babban dakin adana kayan tarihi, da asibitocin yara da lambunan motsa jiki, da kuma manyan hanyoyin mota na zamani, wadanda suka zama tamkar alamomi ga kokarin gina al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamanin da muke ciki.

Duk da cewa akwai tazara sosai tsakanin kasar Sin da kasar Senegal, amma hadin-gwiwar kasashen biyu ta haifar da alfanu ga al’ummar wurin, inda ake da yakinin ci gaba da fadada hadin-gwiwa tsakaninsu a nan gaba don kara amfanin kowa da kowa.

Sin
•Babban filin wasan kokowa da kasar Sin ta taimaka wajen ginawa a Dakar

Tun da aka shirya babban taro karo na 18 na jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin a shekara ta 2012, ya zuwa yanzu, shugaba Xi Jinping yana matukar maida hankali kan raya huldodin Sin da Afirka, inda ya bayyana wasu muhimman manufofin gwamnatinsa na ingiza dangantakar bangarorin biyu, wadanda suka samu babban yabo daga al’ummomin nahiyar Afirka.

A nasa bangaren, shugaban kasar Senegal, Macky Sall ya bayyana cewa: “Ina girmama shugaba Xi Jinping saboda hangen nesa da ya yi, wanda ke cike da hikima. Irin hangen nesa da yake da shi, ya bayyana ne ta hanyar bullo da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, wadda za ta shafi kowa da kowa a duniya, da hada kan jama’ar kasashe daban-daban, da kawo sauki ga mu’amalarsu, musamman jama’ar Afirka da Sin. Dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, wato FOCAC a takaice, daya ne daga cikin hanyoyin hadin-gwiwa mafi muhimmanci tsakanin kasa da kasa, wanda ke kunshe da kudade masu tarin yawa, don amfanawa al’ummomin kasashe daban-daban. Ina girmama wannan shawara, bari mu hada kanmu don yin kokari kafada da kafada.”

Sin
•Babban filin wasan kokowa a birnin Dakar na kasar Senegal

A watan Nuwambar shekara ta 2021, a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC a birnin Dakar na kasar Senegal, an zartas da “muradun hadin-gwiwar Sin da Afirka zuwa shekara ta 2035”. Bisa la’akari da hakikanin halin da ake ciki, bangarorin biyu sun kara samun fahimtar juna kan manufofinsu na samar da ci gaba, inda a karon farko suka tsara shirin hadin-kai na dogon lokaci. Kuma a sabon mafari, bangrorin Sin da Afirka za su ci gaba da hada kai, don tafiya kafada da kafada. Ko shakka babu, gaba dayan al’ummomin Sin da Afirka sama da biliyan 2.7 za su zama tsintsiya madaurinki daya, don kara samar da ci gaba mai inganci, da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakaninsu. (Murtala Zhang)


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Da Kenya Sun Amince Su Zurfafa Hadin Gwiwarsu

Next Post

Mahaifina Ya Mika Kansa Ga ‘Yan Bindiga Suka Kashe Shi Don Ceton Rayuwarmu – Hajiya Asheku

Related

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya
Daga Kasar Sin

Bude Kasar Sin Na Kyautata Ci Gaban Duniya

2 months ago
Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin
Daga Kasar Sin

Mu Leka Jihar Mongolia Ta Gida Dake Arewacin Kasar Sin

10 months ago
wang lili
Daga Kasar Sin

Yadda Wang Lili Ke Kiyaye Neman Cimma Nasara A Wasan Kwallon Kwando

10 months ago
Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura
Daga Kasar Sin

Kumbon Sin Ya Tashi Daga Bangaren Duniyar Wata Mai Nisa Dauke Samfura

11 months ago
Zambiya
Daga Kasar Sin

’Yar Kasar Zambiya: A Nan Kasar Sin, Ina Jin Tamkar Ina Gida!

1 year ago
Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin
Daga Kasar Sin

Ba Shakka Kamfanonin Ketare Za Su Ci Riba In Suka Zuba Jari Da Aiwatar Da Ayyukansu A Sin

1 year ago
Next Post
Sin

Mahaifina Ya Mika Kansa Ga ‘Yan Bindiga Suka Kashe Shi Don Ceton Rayuwarmu - Hajiya Asheku

LABARAI MASU NASABA

Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

May 9, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

May 9, 2025
AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

May 9, 2025
Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci

Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci

May 9, 2025
Matatar Mai: Har Yanzu ‘Kabal’ A Ɓangaren Mai Na Yaƙar Nasararmu – Dangote

Matatar Mai: Har Yanzu ‘Kabal’ A Ɓangaren Mai Na Yaƙar Nasararmu – Dangote

May 9, 2025
Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

May 9, 2025
Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

May 9, 2025
Xi Da Putin Sun Gana Da Manema Labarai Tare

Xi Da Putin Sun Gana Da Manema Labarai Tare

May 8, 2025
Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

May 8, 2025
Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali

Xi: Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Rasha Na Samar Da Daidaito Ga Duniya Mai Cike Da Tashin Hankali

May 8, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.