ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nasarawa Na Sa Ran Samun Dala Miliyan 10 Daga Lithium Kafin Karshen Shekara – Gwamna Sule

by Zubairu M Lawal
2 months ago

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce gwamnatin jihar na sa ran samun aƙalla Dalar Amurka miliyan 10 daga harkar haƙowa da sarrafa ma’adinin lithium kafin ƙarshen wannan shekara.

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ƙaddamar da titin Agwada zuwa Udege mai tsawon kilomita 12.4 da ke Ƙaramar Hukumar Kokona, bayan dawowarsa daga wata tafiya zuwa Amurka domin nemo masu zuba jari.

Gwamna Sule ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen wajen gudanar da ayyukan ci gaba a jihar, musamman a yankin Endo da ke Kokona, inda aka gina ɗaya daga cikin manyan masana’antun sarrafa lithium a Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Ya ce gwamnatin jihar ta cimma yarjejeniya da kamfanin Ganfeng Mining Company Limited, wanda jihar za ta karbi Dalar Amurka miliyan 15 cikin shekaru 10.

Haka kuma, al’ummar Endo za su samu Dalar Amurka 500,000 domin ayyukan ci gaban yankinsu.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Gwamnan ya ƙara da cewa kuɗaɗen shiga daga ma’adinai a jihar sun zarce Naira biliyan ɗaya a kowane wata, sakamakon zuba jarin da ya kai Dalar Amurka miliyan 850 a masana’antar sarrafa lithium.

A cewarsa, ƙarin masu zuba jari na nuna amincewa da damar da jihar ke da ita a ɓangaren ma’adinai, lamarin da ya sa Nasarawa ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin haƙar da sarrafa lithium a Nijeriya.

Sule ya kuma bayyana cewa ziyararsa zuwa Amurka ta jawo hankalin masu zuba jari da jami’an gwamnatin ƙasar, waɗanda suka nuna sha’awar saka hannun jari a lithium da sauran ma’adinan da ke jihar.

Ya ce Ministan Ma’adinai, Dokta Dele Alake, zai ci gaba da tattaunawa da masu zuba jari a Amurka, yayin da shi kuma zai kai ziyara ƙasar China domin neman ƙarin masu zuba jari zuwa jihar.

Gwamnan ya ce ƙarin kuɗaɗen shiga daga ma’adinai da kuma ƙarin rabon kuɗaɗen gwamnatin tarayya sun taimaka wajen yin ayyukan raya ƙasa a jihar.

Ya bayyana cewa ana ci gaba da gina hanyoyi da dama, ciki har da titunan Nasarawa Eggon–Mada Station da Nasarawa–Ara, domin inganta sufuri da tallafa wa noma, haƙar ma’adinai da kasuwanci.

A yayin taron, Gwamna Sule ya ƙaddamar da titin Agwada zuwa Udege mai tsawon kilomita 12.4 da aka gina kan kuɗivNaira biliyan 4.401.

Titin ya haɗa Ƙaramar Hukumar Kokona da Ƙaramar Hukumar Nasarawa, kuma ana sa ran zai rage lokacin tafiya tare da sauƙaƙa jigilar amfanin gona da ma’adinai.

A ƙarshe, gwamnan ya yaba wa kamfanin da ya gina titin saboda kammala aikin ba tare da neman ƙarin kuɗin kwangila ba, yana mai cewa gwamnatinsa ba ta amincewa da ƙarin kudin kwangila bayan an ƙulla yarjejeniya.

Zubairu M Lawal
+ postsBio
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    2027: Miyetti Allah Ta Yi Barazanar Ƙauracewa APC Kan Ci Gaba da Tsare Boɗejo
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Tsaftar Muhalli: Gwamnatin Nasarawa Ta Rufe Kasuwar Tumatir A Lafia
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Samar Da Abinci Mai Gina Jiki: Gwamna Sule Ya Duba Gonakin Shinkafa A Jangwa
  • Zubairu M Lawal
    https://hausa.leadership.ng/author/zubairu-m-lawal/
    Tsohon Sufeto Janar Na ‘Yansanda Ya Tallafawa Manoma Da Kayan Aikin Gona Na Miliyoyin Naira A Nasarawa

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Kasar Sin Ta Gabatar Da Matakan Bunkasa Bangaren Bayar Da Hidimomi A Cikin Gida

Kasar Sin Ta Gabatar Da Matakan Bunkasa Bangaren Bayar Da Hidimomi A Cikin Gida

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.