ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, July 20, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kofin Duniya: Sababbin Dokokin Da FIFA Ta Kawo

by Abba Ibrahim Wada
1 month ago
Kofin Duniya

Kamar yadda aka kawo sauyi a gasar cin kofin duniya, daga wannan karon za a hana ƴan wasa a gasar Kofin Duniya ta 2026 zuwa yankin masu horarwa domin tattaunawa da kociyoyi a lokacin da mai tsaron raga ya ji rauni, kamar yadda shugaban alkalan wasa na FIFA, Pierluigi Collina, ya bayyana.

 Hukumar dokokin kwallon kafa ta duniya (IFAB) kuma ta amince da bukatar sauya tsarin BAR, domin ba da damar duba kura-kuran da suka shafi keta. Wannan tsarin da ake kira “goalkeeper tactical timeout” ya zama abin tattaunawa sosai a dan shekarun nan. Ana amfani da shi ne ta hanyar kociyoyi domin ba dan wasa sabbin umarni ko kuma bata lokacin abokan hamayya.

A watan Nuwamba, kocin Leeds United, Daniel Farke, ya zargi mai tsaron ragar Manchester City, Gianluigi Donnarumma, da yin kamar ya ji rauni domin “karkatar da dokoki” da kuma dakatar da wasa na dan lokaci.

ADVERTISEMENT

A irin wannan yanayi, mai tsaron raga kan zauna a kasa ya nuna alamar neman a duba lafiyarsa, sai sauran dan wasa su garzaya wajen koci domin samun wasu umarni. Bayan mai horarwa ya gama magana, mai tsaron raga zai tashi ya ci gaba da wasa kamar babu abin da ya faru.

Hukumar IFAB ta ce ta dade tana nazarin wannan matsala, amma har yanzu ba a amince da sauyin dokar ba. An kuma bukaci gasannin kasashe su gwada wasu hanyoyi daban-daban a lokacin kakar 2026 zuwa 2027 domin gano mafita. Gasar kwallon kafa ta mata ta Amurka (NWSL) ta riga ta fara amfani da wata dokar a matakin wucin gadi a bana.

LABARAI MASU NASABA

Abubuwa Uku Da Ya Kamata Kusani Akan Kofin Duniya

Xavi Ya Ce A Shirye Yake Ya Karɓi Ragamar Horar Da Tawagar Ƙasa

Idan mai tsaron raga ya ji rauni, dole ne ‘yan wasa na kowanne bangare su tsaya a inda suke ko kuma su taru a tsakiyar fili.

FIFA za ta yi amfani da irin wannan tsarin da aka fara gwadawa a gasar mata ta NWSL, inda za a hana ‘yan wasa zuwa gefen fili, domin yin magana da kociyoyi. Sai dai wannan mataki ba zai magance matsalar gaba daya ba, domin har yanzu ana iya amfani da wannan dabara domin dakatar da yanayin wasan ko bata lokacin abokiyar hamayya.

Collina ya ce dukkan kasashe ya kamata su san cewa wannan ba halas ba ne yanzu. Ya ce: sun yi taron horarwa tare da dukkan kociyoyin tawaga 48 da za su buga gasar kofin duniya, kuma sun gaya musu cewa alkalai za su kasance masu tsaurin aiwatar da doka.

Collina ya ci gaba da cewa ba za su bar ‘yan wasa su je wajen benci ba lokacin da mai tsaron raga, yana kwance a kasa ya ji rauni ba. mai tsaron raga yana da ‘yancin ya ji rauni, amma ‘yan wasa ba su da dancin barin fili su yi amfani da wannan damar a matsayin wani irin hutu ko tuntubar kociyoyinsu.

Sai dai ana ganin tasirin wannan doka a gasar Kofin Duniya zai iya kasancewa abin muhawara, domin za a rika yin hutun shan ruwa na mintuna uku a kowane zangon wasan, wanda zai riga ya zama damar tattaunawa ga kociyoyi.

Jami’an wasa ne za su kula da aiwatar da wannan doka, amma Collina ya ce ba za a ba wa dan wasa katin gargadi ko wani hukunci ba idan suka yi kokarin zuwa tattaunawa da koci. Ya kara da cewa: abin mamaki ne cewa a wasu lokuta alkalin wasa da masu duba lafiyar dan wasa da mai tsaron raga kawai suke ragewa a cikin fili, sauran dan wasa duk sun fita. Wannan ba abu ne mai kyau ba.

Collina ya bukaci a sabunta tsarin BAR domin take iya shiga tsakani idan an samu kuskure, kafin a ci gaba da wasan. An riga an samu wasu misalai, kamar kwallon da Ingila ta ci a wasan da suka tashi 1-1 da Uruguay a Wembley a watan Maris.

Cole Palmer ne ya yi bugun kusurwa, amma kafin ya bugo kwallon sai Adam Wharton ya tare mai tsaron raga, Jose Maria Gimenez.

Wannan ya ba da damar kwallon ta kai ga Harbey Barnes, wanda ya buga kwallon a lokacin da Fernando Muslera ke son ya fitar da ita, sai Ben White ya samu ya zura ta a raga.

A baya, tsarin BAR bai ba da damar duba irin wannan laifi da ya faru kafin a yi bugun kusurwa, amma Collina ya nemi IFAB ta amince da wannan canji. Yanzu IFAB ta amince cewa duk wani laifi da ya faru kafin a fara wasa, idan yana da tasiri kai tsaye, za a iya duba shi a BAR.

Wannan zai shafi bugun fenariti ko hukunci da ya taso daga bugun kusurwa.

Za a fara amfani da wannan mataki a gasar Kofin Duniya, sannan a sake duba dokokin bayan gasar.

Wannan yana nufin cewa a kwallon Ingila, BAR za ta iya ba da shawarar a sake bugun tazara, saboda laifin da Wharton ya yi wa Gimenez. Collina ya ce: suna ganin wannan ba adalci ba ne, cewa a ba da kwallo alhali an hana mai tsaro raga damar kare kansa.

Ya ce suna da kwarin gwiwa cewa IFAB za ta ba da karin bayani kafin kofin duniya cewa BAR na iya shiga tsakani a irin wadannan batutuwan. sun yi imanin babu wanda zai ki hakan.

Wannan sabuwar doka za ta shafi laifukan da ‘yan wasa masu neman cin kwallaye ke yi, ba na masu tsaron raga ba kamar rike ko jan riga. Collina kuma ya bayyana sabuwar doka kan ‘yan wasan da ke rufe baki da hannu ko riga yayin tattaunawa da abokin wasa.

Yanzu hakan zai iya kaiwa ga jan kati, kamar yadda wani abin da ya faru tsakanin Gianluca Prestianni na Benfica da Binícius Júnior na Real Madrid a wasan Champions League.

Prestianni ya samu hukuncin dakatarwa daga wasanni shida daga UEFA saboda halin da aka dauka a matsayin na nuna wariya. Collina ya ce: Idan tattaunawa ta kasance ta sada zumunci, babu matsala. Amma idan ta zama ta rikici, rufe baki yana nufin kana boye wani abu mai hatsari, kuma hukuncin zai iya zama jan kati.

Ya kuma ce alkalai za su kasance cikin shiri wajen lura da turereniya a cikin yankin fanareti, tare da samun bayanai kan dabarun da kungiyoyi ko tawagogi ke amfani da su.

Ga Sabbin sauye-sauyen dokoki a gasar kofin duniya

Gasar Kofin Duniya ta wannan bazarar za ta ga yawan sauye-sauyen dokoki, musamman domin rage dabarun bata lokaci idan ana wasa. Collina na fatan wadannan sauye-sauyen za su sa lokacin karin mintuna (stoppage time) ya ragu idan aka kwatanta da gasar 2022. Sai dai an tabbatar da hutun mintuna uku a kowane zangon wasa, domin shan ruwa (hydration breaks).

Sabbin dokoki:

Kirgen seconds na jefa kwallo (5 seconds):

Idan dan wasa ya yi ganganci wajen jinkirta fara wasa, za a iya ba da jefa kwallon ga abokan hamayya. Kirgen seconds na bugun goal-kick (5 seconds):

Haka kuma idan aka yi amfani da wannan domin bata lokaci, za a iya ba da corner ga abokan hamayya.

Lokacin sauya ‘yan wasa (10 seconds):

Dole ne wanda aka canja ya bar fili cikin dakika 10 mafi kusa. Idan ya karya dokar, wanda zai shigo ba zai iya shiga fili ba har sai bayan minti 1, kuma tawagarsa za ta ci gaba da wasa da ‘yan kwallo 10.

Kula da lafiyar dan wasa (minti 1):

Dole ne dan wasan da ake kula da lafiyarsa ya zauna a waje na dakika 60. Sai dai akwai kebantattu, kamar mai tsaron raga, ko rauni mai tsanani, ko idan abokin hamayya ya samu katin gargadi ko aka kore shi.

Rufe baki yayin tattaunawa tsakanin ‘yan kwallo:

Duk dan wasan da ya rufe bakinsa yayin wata hatsaniya ko rashin jituwa da abokin wasa zai iya fuskantar hukuncin jan kati kai tsaye (red card).

Sauye-sauyen BAR:

Ana iya duba bugun kusurwa:

BAR za ta iya tabbatar da ko an ba da bugun kusurwa daidai ko akasin hakan, amma dole ne a yi hakan da sauri kafin a sake fara wasan. Amma ba ya shafi goal-kick wato bugun falan daya da aka ba da kuskure ba.

Za a iya duba katin gargadi na biyu:

Idan dan wasa ya tashi zai fita daga fili, saboda katin gargadi na biyu, za a iya duba na biyu. Amma ba za a yi nazari kan yiwuwar katin na biyu ba kai tsaye.

A cewar tsohon alkalin wasa Collina, wadannan sauye-sauyen duk suna da nufin rage bata lokaci da kuma yin wasa cikin sauri ko a samu cin kwallaye da yin nishadi da tabbatar da yin adalci.

Kofin Duniya
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya
  • Abba Ibrahim Wada
    Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu
  • Abba Ibrahim Wada
    Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Chana Da Indiya Ba Sa Buga Kofin Duniya?
  • Abba Ibrahim Wada
    Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa NSA Kan Shirin Samar Da Dakarun Tsaron Daji

MASU ALAKA

Kofin Duniya
Wasanni

Abubuwa Uku Da Ya Kamata Kusani Akan Kofin Duniya

July 19, 2026
Xavi Ya Ce A Shirye Yake Ya Karɓi Ragamar Horar Da Tawagar Ƙasa
Wasanni

Xavi Ya Ce A Shirye Yake Ya Karɓi Ragamar Horar Da Tawagar Ƙasa

July 18, 2026
Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya
Wasanni

Tasirin Da VAR Ta Yi A Gasar Kofin Duniya

July 18, 2026
Next Post
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai A Yankin Arewa Maso Gabashin Sin Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai A Yankin Arewa Maso Gabashin Sin Ya Zarce 3,000 A Bana

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin ISWAP Na Sace Ɗalibai A Borno, Sun Ceto 46

Sojoji Sun Daƙile Yunƙurin ISWAP Na Sace Ɗalibai A Borno, Sun Ceto 46

July 19, 2026
Ba Mu Sayar Wa Dangote Da Reshen Jami’ar SAZU Na Yuli Ba-Gwamnatin Bauchi

Ba Mu Sayar Wa Dangote Da Reshen Jami’ar SAZU Na Yuli Ba-Gwamnatin Bauchi

July 19, 2026
Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Asibitin Burkina Faso

Tawagar Jami’an Lafiya Ta Sin Ta Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Asibitin Burkina Faso

July 19, 2026
NDLEA Ta Cafke Kwayoyin Tramadol Miliyan 1.63 Da Akai Nufin Shigar Da Su Kano

NDLEA Ta Cafke Kwayoyin Tramadol Miliyan 1.63 Da Akai Nufin Shigar Da Su Kano

July 19, 2026
Ra’ayin Sin Game Da AI Mai Mayar Da Hankali Kan Bukatun Dan Adam Ya Samu Goyon Bayan Kasa Da Kasa

Ra’ayin Sin Game Da AI Mai Mayar Da Hankali Kan Bukatun Dan Adam Ya Samu Goyon Bayan Kasa Da Kasa

July 19, 2026
Kada A Bar Kasashe Masu Tasowa A Baya A Zamanin AI

Kada A Bar Kasashe Masu Tasowa A Baya A Zamanin AI

July 19, 2026
Gwamna Radda Ya Kaddamar da Tattaunawar Kasafin Kuɗin 2027

Gwamna Radda Ya Kaddamar da Tattaunawar Kasafin Kuɗin 2027

July 19, 2026
Shugaba Tinubu Zai Yi Jawabi Ga Shugabannin Duniya A Taron MDD Karo Na 81

Shugaba Tinubu Zai Yi Jawabi Ga Shugabannin Duniya A Taron MDD Karo Na 81

July 19, 2026
majalisar kasa

Damawa Da Mata A Siyasa: Kujerun Majalisun Tarayya Na Iya Ƙaruwa Zuwa 121, da Kuma 397 A 2027

July 19, 2026
Kofin Duniya

Abubuwa Uku Da Ya Kamata Kusani Akan Kofin Duniya

July 19, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.