Babbar Kotun Tarayya ta ba Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) wa’adin sa’o’i 48 kacal domin ta amshi gami da ɗora sunan ɗan takarar da Jam’iyyar APC ta miƙa mata na mazaɓar Owo/Ose bayan an gudanar da canjin ɗan takara bisa ƙa’ida.
Hukuncin ya fito ne sakamakon ƙarar da aka shigar gabanta da ke ƙalubalantar jinkirin da hukumar zaɓen ta yi wajen amincewa da sauye-sauyen da jam’iyyar mai mulki ta gudanar bayan kammala zaɓen fitar da gwani na cikin gida.
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa, Alƙalin da ya yanke hukuncin ya jaddada cewa hukumar zaɓe ba ta da ikon ƙana amfani da sunan sabon ɗan takarar da jam’iyyar ta gabatar mata, muddin an bi dukkan hanyoyin da Dokar Zaɓe ta ƙasa ta shinfida wajen sauya ɗan takara.
A lokacin da yake yanke shari’ar, Alƙalin ya bayyana cewa gazawar INEC wajen sabunta jerin sunayen ƴan takarar a kan tsarin intanet ɗin ta ya saɓa wa haƙƙin jam’iyyar da kuma na shi kansa ɗan takarar Barrister Ghani Arobo da aka miƙa sunansa.
Kotun ta gargaɗi hukumar da cewa dole ne ta cika wannan umarni cikin wa’adin da aka gindaya mata ba tare da wani jinkiri ba, domin tabbatar da an yi adalci tare da kauce wa matsaloli a tsarin gudanar da zaɓen.














