ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, September 18, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kotu Ta Bayar Da Belin El-Rufai Kan Tsauraran Sharuɗɗa

by Sulaiman
4 months ago
El-Rufai

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Kotun ta bayar da belin ne kan kuɗi naira miliyan 100 tare da sharadin samun mutum guda da zai tsaya masa.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta gindaya tsauraran sharuɗɗa domin samun belin, inda ta ce dole ne wanda zai tsaya masa ya kasance mazaunin yankin Maitama ko Asokoro a Abuja, sannan ya miƙa asalin takardar mallakar fili ko gida ga kotun.

ADVERTISEMENT

Kotun ta kuma umurci cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance ma’aikacin gwamnatin tarayya mai mataki na 17 ko sama da haka, tare da gabatar da shaidar albashin akalla watanni uku.

Bugu da ƙari, wanda zai tsaya masa zai gabatar da rantsuwar bayyana kadarori, ya sanya hannu kan takardar beli, sannan ya kawo sabon hoton fasfo, wasiƙar tabbatarwa daga ma’aikatarsa da kuma takardar biyan haraji ta watanni shida da suka gabata.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Janye Yajin Aiki A Jami’ar Kaduna

Matatar Dangote Za Ta Ƙara Yawan Ma’aikata Da Samar Da Mai

Kotun ta kuma umurci El-Rufai da ya miƙa duk wasu fasfo na ƙasa da ƙasa masu aiki da yake da su.

Mai shari’a Abdulmalik ta ƙara da umartar sa da riƙa kai rahoto hedikwatar Hukumar DSS a kowace Juma’a ta ƙarshen wata da ƙarfe 10 na safe domin sanya hannu a rajistar halarta har sai an kammala shari’ar.

Kotun ta yi gargaɗin cewa karya wa ko saɓa wa duk wani daga cikin sharuɗɗan zai sa a soke belin kai tsaye.

An gurfanar da tsohon gwamnan ne kan zargin sa ido ko satar bayanan wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.

El-Rufai
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya
  • Sulaiman
    An Gudanar Da Dandalin Tattauna Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Hudu
  • Sulaiman
    Yadda Hadin Gwiwar BRICS Ke Ingiza Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa
  • Sulaiman
    Nazarin CGTN: Baje Koli Na Sin Da ASEAN Ya Nuna Kudurin Sin Na Bunkasa Bude Kofa

MASU ALAKA

ASUU Ta Janye Yajin Aiki A Jami’ar Kaduna
Labarai

ASUU Ta Janye Yajin Aiki A Jami’ar Kaduna

September 18, 2026
Matatar Dangote Za Ta Ƙara Yawan Ma’aikata Da Samar Da Mai
Labarai

Matatar Dangote Za Ta Ƙara Yawan Ma’aikata Da Samar Da Mai

September 18, 2026
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci
Manyan Labarai

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Binciken Mutuwar Masu Haƙar Ma’adinai A Neja

September 18, 2026
Next Post
Yusuf Buhari Ya Halarci Zaɓen Fidda Gwani Na Sanatan Shiyyar Daura

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna

Gwamnatin Neja Ta Sanya Dokar Hana Fita Bayan Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Minna

September 18, 2026
ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi

ICPC Ta Yi Wa Dan Takarar APC A Ekiti Titsiye Kan Zargin Badakalar Kuɗi

September 18, 2026
Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi

Gyaran Kundin Tsarin Mulki: Abubuwa 12 Da Ya Kamata A Sani Kan Abin Da Aka Aika Wa Majalisun Jihohi

September 18, 2026
Saudiyya Ta Yi Biris Da Bukatar Nijeriya Ta Ƙarin Kujerun Hajjin 2027

Saudiyya Ta Yi Biris Da Bukatar Nijeriya Ta Ƙarin Kujerun Hajjin 2027

September 18, 2026
Dalilanmu Na Neman NDLEA Ta Binciki Bello El-Rufai Kan Zargin Amfani Da Hodar Iblis

Dalilanmu Na Neman NDLEA Ta Binciki Bello El-Rufai Kan Zargin Amfani Da Hodar Iblis

September 18, 2026
Shettima Ya Yi Karin Haske Kan Maganar Gwamnonin Arewa 6

Shettima Ya Yi Karin Haske Kan Maganar Gwamnonin Arewa 6

September 18, 2026
Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya

Cinikin Shige Da Fice Mai Dorewa Ba Tare Da Gurbatta Muhalli Ba Na Kasar Sin Yana Sahun Gaba A Duniya

September 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.